Haramtacciyar Ƙungiyar Jama’ar Asalin Biyafra, wato Indigenous People of Biafra (IPOB) ta mayar da martani kan kalaman da ɗan Majalisar Wakilan Amurka Riley Moore ya yi game da Nijeriya, tsanantawar addini, da kuma fafutukar neman cin gashin kan yankin kudu-maso-gabashin Nijeriya da sunan Biafra.
A cikin sanarwar da kakakin ƙungiyar, Kwamared Emma Powerful, ya fitar a yau Lahadi, ƙungiyar ta soki ra’ayin Mista Moore cewa kare cikakken yankin Nijeriya tamkar kare Kiristoci ne.
A jiya Asabar ne Moore ya yi gargaɗi kan raba Nijeriya gida-gida, yana mai cewa ƙarfafa ƙungiyoyin masu neman ɓallewa daga Nijeriya yana iya barazana kai-tsaye ga tsaron Kiristoci, musamman a yankunan Arewa da Tsakiyar ƙasa masu fama da rikice-rikice.
Ɗan majalisar na Amurka, wanda kwanan nan ya kammala wata ziyarar bincike mai zurfi a faɗin ƙasar, ya bayyana abin da ya lura da shi ɗin ne ta shafin sa na X.
Ya ce ziyarar tasa ta haɗa da ganawa da manyan jami’an gwamnati, shugabannin coci, ƙungiyoyin agaji, da kuma ’yan gudun hijira na cikin gida (IDPs), domin binciken abin da ya kira “tsanantawar Kiristoci da ta yi ƙamari” a Nijeriya.
Ya kuma ƙara da cewa, saɓanin matsayar ƙungiyoyin masu fafutukar ɓallewa, rushewar ƙasar ba shi ne abin da ya fi muhimmanci ga waɗanda ya gana da su ba.
Sai dai IPOB ta bayyana matsayar Moore ɗin a kan batun a matsayin mai cike da kuskure.
Ta ce: “Da cikakkiyar girmamawa, matsayin da aka danganta wa Rep. Riley Moore yana nuna wata fahimta da aka saba da ita amma mai zurfin kuskure: cewa kiyaye cikakken yankin Nijeriya daidai yake da kare Kiristoci. Tarihi ya tabbatar da akasin haka.”
A sanarwar ta IPOB, Powerful ya bayyana cewa a cikin shekaru sittin da suka gabata, an ci gaba da kiyaye cikakken yankin Nijeriya a ƙarƙashin “tsarin mulki mai takura da Turawan Birtaniya suka ƙirƙira,” inda Kiristoci, musamman a Arewacin Nijeriya, Tsakiyar ƙasa, da wasu sassan ƙasar Yarabawa, suka fuskanci “kisan gilla na lokaci-lokaci, tarwatsa jama’a, ƙona coci-coci, da al’adar rashin hukunta masu laifi da gwamnati ke ba da dama.”
A cewar IPOB, waɗannan rikice-rikicen ba wai “rashin haɗin gwiwar tsaro ba ne; illa ce ta tsarin haɗa ƙasa da aka tilasta tsakanin al’ummomi masu bambancin addini da wayewar kai da ba su da jituwa.”
Ƙungiyar ta kuma yi tsokaci kan maganar Moore cewa neman cin gashin kai “yana ƙarfafa ’yan ta’adda,” inda ta bayyana hakan a matsayin “ra’ayi da ya samo asali daga harkar kuɗin kamun ƙafa dala miliyan tara a Washington, ba daga hujja ba.”
Kwamared Powerful ya ce, “Ƙungiyoyin ta’addanci ba sa tasowa ne saboda al’ummomin da ake zalunta suna neman tsaro; suna bunƙasa ne a inda ƙasashe masu tsarin mulkin tarayya suke danne asali, hana cin gashin kai, tare da saka wa tashin hankali da sassauci.”
Ya kawo ƙasar Afghanistan a matsayin misali na baya-bayan nan, yana mai cewa “shekaru na haɗin gwiwar soja, tallafi, da gina cibiyoyi sun rushe cikin dare guda, yayin da tsattsauran ra’ayi ya sake ƙarfi fiye da da.”
Yayin da yake danganta batun da tarihin baya, mai magana da yawun IPOB ɗin ya ce rabuwa sau da yawa ta zama kariya ga ƙananan al’ummomin addini da ake tsananta wa.
Ya ce: “’Yan Huguenot da ake tsananta wa ba su tsira a Faransa ta Katolika ba ne saboda Faransa ta zama mai haƙuri. Sun tsira ne saboda akwai Ingila mai zaman kan ta ta Furotestan — mafaka mai cikakken iko da ƙarfin siyasa, soja, da ƙudirin kare su. In da ba tare da Ingilar Furotestan ba, to da ba a samu mafaka ga Furotestocin Turai da ke gudun hallaka ba.”
Powerful ya kwatanta fafutukar Biyafra ta yanzu da wannan, yana mai cewa yunƙurin da Mazi Nnamdi Kanu ke jagoranta “ba kira ne zuwa tashin hankali ba, kuma ba wani shiri ba ne na tayar da rikici a Yammacin Afrika kamar yadda masu kamun ƙafar Birtaniya/Nijeriya a Turai da Amurka ke so a yarda ba. Buƙata ce ta ƙuri’ar raba gardama ta dimokiraɗiyya, wadda ita ce hanya mafi zaman lafiya ta warware rikici da dokokin ƙasa da ƙasa suka amince da ita.”
Ya ƙara da cewa Biyafra da aka maido “za ta zama ginshiƙin wayewa mai aminci — ƙasa inda Kiristoci da mabiya sauran addinai daga ko’ina cikin Nijeriya za su rayu ba tare da tsoro ba, kuma daga nan ne Kiristocin da ake tsananta wa a wasu wurare za su sami mafaka da kariya.”
Sanarwar ta kuma yi iƙirarin cewa fitowar IPOB ta haifar da tasiri a ɓangaren tsaro, tana cewa, “Tun bayan fitowar IPOB, kisan gilla da aka saba yi wa ‘yan ƙabilar Igbo a Arewacin Nijeriya ya tsaya cak. Wannan ba kuskure ba ne. Nuna ƙarfin kai na gama-gari ya samar da tsoratarwa inda sassauci na shekaru ya gaza.”
Duk da amincewa da muhimmancin haɗin gwiwar tsaro, IPOB ta ce hakan na magance alamomi ne kawai ba tushen matsalar ba.
“Haɗin gwiwar tsaro tsakanin Amurka da Nijeriya na iya sarrafa alamomi, amma bai taɓa warkar da cutar ba. Maimaita dabarar da ta gaza tsawon ƙarni — tare da watsi da neman cin gashin kai a matsayin haɗari — ba hikima ba ce; mantuwa ce da tarihi,” inji sanarwar.
Powerful ya jaddada cewa goyon bayan neman cin gashin kai ba ya nufin adawa da zaman lafiya ko haɗin gwiwa wajen yaƙi da tsattsauran ra’ayi.
“Babu mai gaskiyar neman zaman lafiya da zai ƙi haɗin gwiwa wajen yaƙi da tsattsauran ra’ayi. Amma ƙin amincewa da hanyoyin doka na fita cikin zaman lafiya, tare da nacewa kan ɗorewar ƙasa da ta nuna gazawa, yana tabbatar da ci gaba da tsanantawa maimakon kawo ƙarshen ta,” inji sanarwar.
Kakakin ƙungiyar ya ce Biyafra mai cin gashin kan ta za ta ƙarfafa zaman lafiyar yankin maimakon barazana gare shi.
“Biyafra mai zaman kan ta, kamar Ingila ta Furotestan mai cin gashin kan ta ko ƙasar Isra’ila, ba za ta zama barazana ga zaman lafiyar yankin ba. Za ta samar da shi — ta hanyar bai wa al’ummomin da ake tsananta wa abin da ba su taɓa samu a cikin Nijeriya ba: wato mafaka mai cikakken iko.”
“Gaskiyar damuwa ga Kiristoci — da kuma duk ’yan Nijeriya — ta fara ne da gaskiyar tunani: haɗin kai na tilas ya gaza. Tsaro, mutunci, da zaman lafiya sun kasance sakamakon mulkin kai, ba musun sa ba,” inji Powerful.







