• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Gwamnatin Tarayya ta tura ƙarin jami’an tsaro don kawar da ta’addanci — Ministan Yaɗa Labarai

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
November 19, 2025
in Labarai
A A
0
Gwamnatin Tarayya ta tura ƙarin jami’an tsaro don kawar da ta’addanci — Ministan Yaɗa Labarai
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, yana jawabi a taron manema labarai a yau a Abuja

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, yana jawabi a taron manema labarai a yau a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta jaddada ƙudirin ta na kare rayuka da dukiyar dukkan ‘yan Nijeriya sakamakon hare-haren da aka kai a baya-bayan nan a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Da yake jawabi a wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Laraba, a Radio House, Abuja, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya isar da saƙon ta’aziyyar Shugaban Ƙasa ga iyalai da al’ummomin da suka fuskanci ayyukan ta’addanci na baya-bayan nan.

Idris ya ce: “Ku sani cewa Shugaban Ƙasa Tinubu ya tura sojoji su kawar da ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga, da sauran miyagu a duk inda suke a Nijeriya. Haka kuma, an bada umurni ga jami’an tsaron mu da su gaggauta ceto ‘yan matan makarantar Kebbi da aka sace tare da haɗa su da iyalan su.”

Ministan ya bayyana kashe wani babban Janar na soja, da sace ɗalibai a Jihar Kebbi, da kuma harin da aka kai kan wani coci a Jihar Kwara a matsayin “abin tunatarwa mai raɗaɗi game da barazanar da ƙasar nan ke fuskanta,” yana mai cewa irin waɗannan ayyukan suna ƙara ƙarfafa aniyar Gwamnatin Tarayya ta kawo ƙarshen ta’addanci.

Ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya ɗage tafiye-tafiyen sa na ƙasashen waje, ciki har da taron G20 a Afrika ta Kudu, don maida hankali kan tsaron cikin gida, tare da cewa Shugaban Ƙasar ya umurci sojoji da ‘yan sanda da su tura ƙarin jami’ai zuwa Eruku da kuma dukkanin Ƙaramar Hukumar Ekiti ta Jihar Kwara, don tabbatar da tsaro da kuma bada amsa cikin gaggawa.

Bugu da ƙari, Idris ya bayyana cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, a halin yanzu yana Birnin Kebbi bisa umarnin Shugaban Ƙasa, inda yake tattaunawa da Gwamnan Jihar Kebbi, da manyan jami’an tsaro, da sarakunan gargajiya, da kuma iyalai na ‘yan matan makarantar da aka sace.

“Shugaba Tinubu ya kuma umurci dukkan hukumomin tsaro da su bi diddigi, su kawar, tare da lalata cibiyoyin ‘yan ta’adda da na miyagu a duk faɗin ƙasar nan,” inji Idris, kuma ya tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa ceto ‘yan matan makarantar Kebbi da aka sace abu ne mai matuƙar muhimmanci.

Da yake jawabi kan yunƙurin da ake yi na siffanta lamarin tsaro a matsayin lamarin addini, Ministan ya ce Gwamnatin Tarayya “ba ta amince da kowace irin fassara ta addini ba” dangane da matsalolin tsaro na ƙasar nan.

Ya jaddada cewa barazanar tsaro ta Nijeriya daga ta’addanci zuwa ‘yan bindiga ta shafi ‘yan ƙasa daga dukkan addinai da asali.

Ya ce: “A wannan lokaci mai muhimmanci, haɗin kan ƙasa shi ne mafi girman abin da muke da shi. Dole ne mu ƙi yaɗuwar labaran ƙarya da rarrabuwa. Maƙiyan mu ‘yan ta’adda ne kuma miyagu da ke neman hargitsa ƙasar mu.”

Ministan ya sake nanata matsayin Nijeriya a matsayin ƙasa mai addinai daban-daban inda ‘yancin yin addini yake da kariya ta tsarin mulki.

Ya yi kira ga ‘yan ƙasa da su haɗa kai da kuma goyon bayan ƙoƙarin jami’an tsaro da ke aiki tuƙuru don tabbatar da tsaron ƙasar, yana mai cewa gwamnati tana da yaƙinin cewa ayyukan tsaro da ake gudanarwa za su kai ga gaggauta ceto ‘yan matan makarantar da aka sace da kuma dawo da zaman lafiya a cikin al’ummomin da abin ya shafa.

Tags: Mohammed Idristsaro
Previous Post

Sunayen ‘yan makarantar sakandaren mata 25 da aka sace a Kebbi

Next Post

Kotu ta kama Nnamdi Kanu da laifin ta’addanci bayan ya ƙi kare kan sa

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Kotu ta kama Nnamdi Kanu da laifin ta’addanci bayan ya ƙi kare kan sa

Kotu ta kama Nnamdi Kanu da laifin ta'addanci bayan ya ƙi kare kan sa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!