• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Gwamnatin Tarayya ta buƙaci haɗin kai domin ƙarfafa martabar Nijeriya a idon duniya

Wakilin Mu by Wakilin Mu
January 20, 2026
in Labarai
A A
0
Gwamnatin Tarayya ta buƙaci haɗin kai domin ƙarfafa martabar Nijeriya a idon duniya
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, yana jawabi a wurin taron bitar martabar Nijeriya na shekarar 2026 da aka gudanar a Cibiyar Shehu Musa Yar'Adua yau a Abuja

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, yana jawabi a wurin taron bitar martabar Nijeriya na shekarar 2026 da aka gudanar a Cibiyar Shehu Musa Yar'Adua yau a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga ɗaukacin ‘yan Nijeriya, ƙwararru, cibiyoyi, da kamfanoni masu zaman kan su da su ɗauki nauyin ginawa tare da kare martabar ƙasar nan a idon duniya, ta hanyar sadarwa ta gaskiya da kuma nuna cigaban da ake samu.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya yi wannan kiran a ranar Talata a wurin taron bitar martabar Nijeriya na shekarar 2026 da aka gudanar a Abuja.

Yayin da yake jawabi a taron, Ministan ya bayyana ƙaddamar da ma’aunin fahimtar martabar Nijeriya na farko da Cibiyar Hulɗa da Jama’a ta Nijeriya (NIPR) ta yi, a matsayin wani babban mataki na fahimtar yadda ake kallon ƙasar nan a gida da waje.

Ya ce: “Wannan rahoto ba hukunci ba ne kan Nijeriya; madubi ne. Kuma a matsayin mu na ƙasa da suka san haƙƙin da ya rataya a wuyan su, dole ne mu kasance masu ƙarfin halin kallon wannan madubin sannan mu ɗauki mataki.”

Idris da Fashola

Idris ya yaba wa NIPR da Rukunin Masu Gudanar da Martaba Nijeriya da shugabancin su bisa samar da wannan rahoto bayan shekaru da dama na bincike, yana mai jaddada cewa gina martabar ƙasa aiki ne na dogon lokaci da ke buƙatar ladabi da ɗorewa.

Yayin da ya amince cewa rahoton ya sanya Nijeriya cikin rukunin ƙasashen da ba a cika amincewa da su ba, Ministan ya ce an samu gagarumin cigaba a cikin shekaru biyu da suka gabata a ƙarƙashin gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Ya ce: “Ba ma inda muke a baya. Ko da yake fahimta takan yi jinkiri kafin ta riski gaskiyar abin da ake ciki, ana samun cigaba na gaske, kuma dole ne a riƙa bayyana hakan a sarari, a kai a kai, kuma cikin gaskiya,” inji shi.

Ya bayyana ɗorewar dimokiraɗiyyar Nijeriya, inda ya bayyana cewa ƙasar nan ta shafe shekaru 27 tana cin moriyar dimokiraɗiyya ba tare da tangarɗa ba, tare da buɗaɗɗiyar damar shiga harkokin siyasa da kuma ɗaya daga cikin mafi ’yancin yaɗa labarai a duniya.

Ministan tare da jami’an NIPR

Ya ce: “Waɗannan ba ƙananan nasarori ba ne. Suna nuna ingancin jagoranci, sahihanci, da amana, waɗanda su ne jigon martabar ƙasa.”

Game da harkokin mulki da gyaran tattalin arziƙi, Idris ya kawo misali da gyare-gyaren da ake yi domin ƙarfafa ’yancin kan Ƙananan Hukumomi, inganta tsaro ta hanyoyin da suka shafi al’umma, da maido da daidaiton kuɗi ta hanyar cire tallafin man fetur da daidaita farashin canjin kuɗaɗen ƙasashen waje.

Ya ce: “An ɗauki tsauraran matakai, amma matakai ne masu muhimmanci. A yau, hauhawar farashin kaya na raguwa, tattalin arziki yana daidaita, sannan asusun ajiyar mu na ƙasar waje yana ƙaruwa.”

Haka kuma, Ministan ya jaddada zuba jari da ake ci gaba da yi a fannonin samar da ababen more rayuwa, kiwon lafiya, ilimi, da noma, da kuma shirye-shiryen ƙirƙira da suka shafi matasa, ciki har da tsarin ba da rance ga ɗalibai da tallafin jari ga matasa ’yan kasuwa.

Da yake magana kan rahotannin ƙarya da ake yaɗawa game da Nijeriya, musamman iƙirarin rashin jituwa ta addini, Ministan ya ce irin waɗannan bayanai ba sa nuna ainihin yadda ƙasar take.

Ya ce: “Nijeriya ba ƙasa ba ce ta rashin jituwa. Muna aiki tuƙuru wajen gyara bayanan ƙarya ta hanyar diflomasiyya, ƙarfafa tsaro, da kuma ci gaba da hulɗa da abokan hulɗar mu.”

Ya jaddada cewa ba gwamnati kaɗai ba ce take da alhakin gina martabar Nijeriya.

“Ana samun martaba ne ta hanyar ayyuka, ba kawai taken baka ba. Ana gina ta ne idan manufofin gwamnati suka haɗu da kyakkyawar niyya, kuma idan sadarwa ta nuna gaskiya,” inji Ministan.

“Wannan aiki ne na ƙasa baki ɗaya, kuma kowane ɗan Nijeriya yana da rawar da zai taka.”

Ministan ya yi kira ga ƙwararrun masu sadarwa da kuma ’yan ƙasa da su ƙarfafa haɗin kai, su yi watsi da labaran ƙarya, sannan su nuna martabar Nijeriya cikin ƙwarin gwiwa.

Ya gode wa mahalarta taron bisa jajircewar su ga cigaban ƙasa.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, yana jawabi a wurin taron bitar martabar Nijeriya na shekarar 2026 da aka gudanar a Cibiyar Shehu Musa Yar’Adua yau a Abuja

Manyan baƙi da suka halarci taron sun haɗa da tsohon Ministan Ayyuka da Gidaje kuma tsohon Gwamnan Jihar Legas sau biyu, Cif Babatunde Raji Fashola, wanda ya gabatar da babban jawabi; tsohuwar Ministar Harkokin Mata, Misis Pauline Tallen; Darakta-Janar na Hukumar Kula da Tallace-Tallace ta Nijeriya (ARCON), Dakta Olalekan Fadolapo;

Darakta-Janar na hukumar gidan Muryar Nijeriya (VON), Malam Jibrin Baba-Ndace; da kuma Shugaban Cibiyar Hulɗa da Jama’a ta Nijeriya (NIPR), Dakta Ike Neliaku, da sauran manyan baƙi.

Tags: MohammedIdrisNIPR
Previous Post

Gwamnatin Tarayya ta buɗe rajistar neman guraben karatu a ƙasar waje na PTDF

Next Post

Zargin damfarar dala miliyan 13: Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan buƙatar EFCC na ƙwace kuɗi gaba ɗaya

Related Posts

Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya
Labarai

Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya

September 29, 2026
Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
Next Post
Zargin damfarar dala miliyan 13: Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan buƙatar EFCC na ƙwace kuɗi gaba ɗaya

Zargin damfarar dala miliyan 13: Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan buƙatar EFCC na ƙwace kuɗi gaba ɗaya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!