• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Ilimi

Gwamnatin Tarayya ta buɗe rajistar neman guraben karatu a ƙasar waje na PTDF

Wakilin Mu by Wakilin Mu
January 20, 2026
in Ilimi
A A
0
Gwamnatin Tarayya ta buɗe rajistar neman guraben karatu a ƙasar waje na PTDF
Tambarin ba da guraben karatu na PTDF

Tambarin ba da guraben karatu na PTDF

Gwamnatin Tarayya ta bayyana buɗe fara rajistar neman guraben karatu a ƙasar waje na shekarar 2026 ƙarƙashin Hukumar Haɓaka Fasahar Man Fetur (Petroleum Technology Development Fund, PTDF) domin bai wa ɗaliban Nijeriya damar karatun digiri na biyu (MSc) da digiri na uku (PhD) a Birtaniya, Jamus, Faransa da Malaysia.

Sanarwar ta fito ne ta shafin X na Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Sadarwa ta Zamani, Dada Olusegun, a jiya Litinin.

Sanarwar ta ce an fara karɓar rajistar masu neman guraben karatun PTDF na ƙasashen waje na 2026.

A cewar bayanin da PTDF ta wallafa a shafin ta na intanet, shiri ne na masu neman MSc da PhD a fannoni da suka shafi harkar mai da iskar gas, inda tsarin zai ɗauki nauyin kuɗin karatu, tikitin jirgi na zuwa da dawowa, masauki, alawus na rayuwa, inshorar lafiya, da kuɗin bincike (bench fees).

PTDF ta bayyana cewa shirin zai bai wa waɗanda suka samu guraben horo da kayan bincike na zamani a matakin duniya, tare da ƙarfafa ƙwarewar ’yan Nijeriya a fannin mai da iskar gas.

Ga masu neman PhD a Birtaniya, an tanadi tsarin split-site, inda za a gudanar da bincike tsakanin College of Petroleum and Energy Studies, Kaduna (CPESK) da wasu jami’o’in haɗin gwiwa a Birtaniya, ciki har da Robert Gordon University, University of Strathclyde, da University of Portsmouth.

Hukumar ta jaddada cewa gurabe ne da ake tsananin gasa, inda za a tantance masu nema bisa ƙwarewar ilimi, shirin bincike, kasancewa cikin ƙungiyoyin ƙwararru, da kuma dacewar karatun da harkar mai da iskar gas.

Sharuɗɗan MSc sun haɗa da samun aƙalla Second Class Lower (2.2) ko 2.1 a digiri na farko, kammala NYSC, iya amfani da kwamfuta, da samun Credit a sakamakon O’Level biyar, ciki har da Turanci da Lissafi.

Masu neman PhD kuma dole su gabatar da shirin bincike na shafuka biyar wanda zai fayyace manufofi, dabarun aiwatarwa, da hanyoyin tattara bayanai.

PTDF ta ƙara da cewa za a tantance NIN na duk masu nema kafin cike fom, tare da gargaɗin cewa maimaita rajista ko gabatar da takardu na bogi zai haifar da cire mutum kai-tsaye.

An shawarci masu sha’awa su nemi guraben ta yanar gizo a scholarship.ptdf.gov.ng bisa tsare-tsaren da aka amince da su a jami’o’in abokan hulɗar PTDF.

Za a rufe rajistar a ranar 27 ga Fabrairu, 2026.

Tags: gurabekaratuPTDFscholarships
Previous Post

Abdul’aziz ya wakilci Shugaban Ƙasa a wajen ta’aziyyar mata da ‘ya’yan ta shida da aka kashe a Kano

Next Post

Gwamnatin Tarayya ta buƙaci haɗin kai domin ƙarfafa martabar Nijeriya a idon duniya

Related Posts

Hukumar NSUBEB ta kammala gyaran wasu makarantu a Neja
Ilimi

Hukumar NSUBEB ta kammala gyaran wasu makarantu a Neja

August 29, 2026
Ilimi

Niger-SUBEB ta tabbatar da ƙarin girma ga malaman da suka cancanta

August 22, 2026
Zuba jarin Gwamnatin Tarayya a manyan makarantu zai bunƙasa tattalin arzikin Arewa ta Tsakiya – Idris
Ilimi

Zuba jarin Gwamnatin Tarayya a manyan makarantu zai bunƙasa tattalin arzikin Arewa ta Tsakiya – Idris

August 20, 2026
Gwamnan Neja ya ba jami’ar AKUM motocin aiki
Ilimi

Gwamnan Neja ya ba jami’ar AKUM motocin aiki

August 4, 2026
Ɗan Goodluck Jonathan, Ariwera, ya yi bikin kammala karatun jami’a a Birtaniya
Ilimi

Ɗan Goodluck Jonathan, Ariwera, ya yi bikin kammala karatun jami’a a Birtaniya

July 16, 2026
Gwamnatin Tarayya da ASUU sun ƙulla yarjejeniya ta farko a tarihi domin kawo ƙarshen yawan yajin aiki a jami’o’i
Ilimi

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin ƙara kuɗin rajistar jarabawar WAEC da NECO

July 14, 2026
Next Post
Gwamnatin Tarayya ta buƙaci haɗin kai domin ƙarfafa martabar Nijeriya a idon duniya

Gwamnatin Tarayya ta buƙaci haɗin kai domin ƙarfafa martabar Nijeriya a idon duniya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!