• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Thursday, May 14, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Gwamnati za ta hukunta wanda ya karɓi kuɗi don sanya mitar lantarki

Wakilin Mu by Wakilin Mu
January 23, 2026
in Labarai
A A
0
Gwamnati za ta hukunta wanda ya karɓi kuɗi don sanya mitar lantarki
Ministan Wutar Lantarki, Mista Adebayo Adelabu

Ministan Wutar Lantarki, Mista Adebayo Adelabu

Gwamnatin Tarayya ta haramta wa kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos) da masu sanya mita karɓar kowanne irin kuɗi daga jama’a kafin ko bayan girke mitar wuta, tare da yin gargaɗin cewa duk jami’i ko mai girke mita da aka kama yana karɓar kuɗi zai fuskanci hukunci.

Ministan Wutar Lantarki, Mista Adebayo Adelabu, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da yake duba sababbin mitocin wuta na zamani (smart meters) da aka shigo da su ƙasar nan a tashar APM Terminals da ke Apapa, Legas.

Ya ce an sayo mitocin ne ƙarƙashin shirin Bankin Duniya na Distribution Sector Recovery Programme (DISREP), kuma wajibi ne a sanya su ga masu amfani da wuta kyauta.

Ministan ya jaddada cewa duk wani yunƙuri na neman kuɗi daga masu amfani da wuta laifi ne.

“Ko jami’an DisCos ko masu sanya mita ba su da ikon karɓar ko sisi guda daga jama’a. Sanya mitocin kyauta ne gaba ɗaya,” inji shi.

Adelabu ya bayyana farin cikin sa kan shigowar karin mitoci 500,000, inda ya ce gwamnati na shirin shigo da mitoci kimanin miliyan 3.4 a karo na biyu da za a yi.

Ya ce a kashin farko na mitoci miliyan 1.43, an riga an karɓi kusan miliyan ɗaya, kuma sama da mitoci 150,000 an riga an sanya su a gidaje a faɗin ƙasar nan.

Ya ƙara da cewa mitocin za a raba su ga dukkan masu amfani da wuta ba tare da la’akari da band ɗin su ba, da nufin rage gibin mitoci, inganta adalci da gaskiya wajen lissafin kuɗin wuta, da kuma ƙara yawan kuɗaɗen shiga a ɓangaren wutar lantarki.

Ministan ya kuma bayyana cewa gwamnati za ta sa ido sosai kan aikin sanya mitocin, tare da buɗe ofishin karɓar ƙorafe-ƙorafe domin jama’a su rika kai rahoton duk wani jami’i ko mai sanya mita da ya nemi kuɗi ba bisa ƙa’ida ba.

Ya ce Hukumar Kula da Wutar Lantarki (NERC) da hukumomin jihohi za su taka rawa wajen sa ido da ɗaukar mataki.

A cewar sa, idan aka kammala wannan shiri, cikin ‘yan shekarun nan kowane gida, kasuwa da ma’aikata za su kasance da mita, lamarin da zai kawo sauyi mai ma’ana a ɓangaren wutar lantarki a Nijeriya.

Tags: AdebayoAdelabuDISCOsmitawutarlantarki
Previous Post

Tinubu ya ba da umurnin a fara aikin haƙo man fetur a Ogun

Next Post

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano

Related Posts

EFCC ta kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Nijeriya, Mustapha Abdullahi, kan zargin zambar naira biliyan 500
Labarai

EFCC ta kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Nijeriya, Mustapha Abdullahi, kan zargin zambar naira biliyan 500

May 13, 2026
Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista
Tsaro

Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista

May 13, 2026
Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75
Labarai

Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75

May 13, 2026
Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu
Ilimi

Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu

May 11, 2026
An kama Bello Boɗejo, shugaban Fulani Kuma ɗan takarar kujerar Sanata na APC a Taraba
Siyasa

An miƙa ɗan takarar Sanata kuma shugaban Fulani, Bello Boɗejo ga EFCC

May 10, 2026
Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka
Tsaro

Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka

May 9, 2026
Next Post
Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano

Abin da ya sa na fice daga NNPP - Gwamnan Kano

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!