Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi murabus daga jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), tare da wani guntun manyan jami’an gwamnati a faɗin jihar.
An ba da sanarwar murabus din gwamnan ne ta hanyar wata wasiƙa da aka aike wa Shugaban NNPP na Mazaɓar Ɗiso-Chiranchi da ke Ƙaramar Hukumar Gwale, inda aka bayyana cewa murabus ɗin zai fara aiki ne daga ranar 25 ga Janairu, 2026.
An tabbatar da wannan lamari a yau cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, inda ya ce matakin ya biyo bayan dogon rikicin cikin gida da ke addabar jam’iyyar.
A cewar sanarwar, Gwamna Yusuf ya rubuta wa jam’iyyar takarda inda ya bayyana godiya matuƙa ga NNPP bisa ba shi damar siyasa da kuma goyon bayan da ya samu daga shugabanni da ‘ya’yan jam’iyyar a lokacin da yake cikin ta.
A cikin wasiƙar, ya ce: “Ina rubuto wannan wasiƙa ne cike da godiya domin sanar da shugabancin jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) a hukumance game da shawarar da na yanke na yin murabus daga jam’iyyar.”
Abba ya ce har yanzu yana godiya ga damar da jam’iyyar ta ba shi tun daga shekarar 2022 ya kasance cikin tafiyar siyasar ta, da kuma kyakkyawar mu’amala da haɗin kai da aka nuna masa a lokacin mulkin sa.
Sai dai ya danganta murabus ɗin nasa da rikice-rikicen shugabanci da kuma dogayen shari’o’i da suka daɗe suna girgiza tsarin jam’iyyar a matakin jiha da na ƙasa.
Ya ce: “A ‘yan kwanakin nan, jam’iyyar ta fuskanci ƙalubale na cikin gida masu ci gaba da faruwa sakamakon saɓanin shugabanci da shari’o’in da ke gudana, da dama daga cikin su a gaban kotuna domin yanke hukunci.”
Ya ƙara da cewa rikice-rikicen, waɗanda ba a warware su ba, sun haifar da toshe haƙƙin membobi da dama, suna ƙara rarrabuwar kai da raunana dunƙulewar jam’iyyar.
“Yawaitar toshe haƙƙin ‘ya’yan jam’iyya ya haifar da babbar rarrabuwar kai a cikin tsarin jam’iyyar, wanda ya haifar da ɓaraka da ke ƙara zama mai wahalar gyarawa, tare da haifar da rashin tabbas a matakin jiha da na ƙasa.”
Gwamnan ya ce ya yanke shawarar ne bayan dogon nazari, yana mai cewa ya yi hakan ne bisa abin da ya ga ya fi dacewa da al’ummar Jihar Kano, yana jaddada cewa matakin an ɗauke shi ne cikin kyakkyawar niyya ba tare da wata muguwar manufa ba.
Ya ƙara da cewa: “Bayan yin tunani mai zurfi, kuma ba tare da raina ikon jam’iyyar na warware matsalolin ta na cikin gida ba, na yanke shawarar cewa murabus ɗina shi ne mafi alheri ga al’ummar Jihar Kano.”
Abba Yusuf ya sake jaddada ƙudirin sa na wanzar da zaman lafiya, haɗin kai da cigaban Jihar Kano, yana mai tabbatar wa da al’umma cewa gudanar da mulki zai ci gaba da kasancewa babban abin da ya sa a gaba.
Wani abin lura mai muhimmanci, gwamnan bai fice daga jam’iyyar shi kaɗai ba, sai da ya tafi tare da na ‘yan Majalisar Dokokin Jihar Kano mutum 21, da ‘yan Majalisar Wakilai takwas, da kuma shugabannin ƙananan hukumomi 44 a faɗin jihar—abin da ke wakiltar ɗaya daga cikin mafi girman ficewar jama’a daga jam’iyya a tarihin siyasar Kano.
Sakataren NNPP na Mazaɓar Ɗiso-Chiranchi, Hon. Kabiru Zubairu, wanda ya tabbatar da karɓar wasiƙar murabus ɗin gwamnan, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da nuna alhini kan ficewar Yusuf.
“Ina goyon bayan Mai Girma kan rikicin da ya daɗe yana addabar jam’iyyar mu. Duk da cewa muna ƙoƙarin mu wajen shawo kan sa, ba mu da wani zaɓi face amincewa da murabus ɗin ɗaya daga cikin gwamnonin NNPP da suka fi yin aiki,” inji Zubairu.
Ya yaba wa Gwamna Yusuf kan manyan nasarorin da ya ce ya samu a ɓangarorin raya ababen more rayuwa, sabunta birane, lafiya, ilimi da ƙarfafa tattalin arziki, yana mai cewa jam’iyyar za ta ji matuƙar tasirin ficewar sa.







