Gwamnatin ƙasar Chana ta bayyana cikakken goyon bayan ta ga Nijeriya a daidai lokacin da ake samun zazzafar muhawara kan sukar da Amurka ta yi kan yadda gwamnatin Nijeriya ke tafiyar da batutuwan addini a cikin ƙasar nan.
Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Waje ta China, Madam Mao Ning, ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da aka wallafa a shafin ma’aikatar a yau Talata, inda ta ce ƙasar ta tana adawa da duk wani ƙoƙarin tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kowace ƙasa, musamman da sunan kare ‘yancin addini ko ɗan’adam.
Ta ce: “A matsayin ta na abokiyar hulɗa ta dabarun cigaba da Nijeriya, Chana na cikakken goyon bayan gwamnatin Nijeriya wajen jagorantar al’ummar ta bisa tsarin da ya dace da halin da ƙasar take ciki.
“Muna adawa da duk wata ƙasa da ke tsoma baki cikin harkokin wasu ƙasashe da sunan addini ko kare ‘yancin ɗan’adam. Muna kuma adawa da barazanar sanya takunkumi ko amfani da ƙarfi don tilasta wa wata ƙasa bin wata hanya.”
Wannan matsayi na Chana yana zuwa ne bayan Shugaba Donald Trump ya bayyana Nijeriya a matsayin “ƙasa mai matsala ta musamman” saboda, a cewar sa, ana zaluntar mabiya addinin Kirista a ƙasar.
Trump ya yi barazanar cewa Amurka na iya dakatar da duk wani taimako ga Nijeriya, ko ma ta ɗauki matakin soja idan gwamnatin Nijeriya “ta ci gaba da bari ana kashe Kiristoci.”
Masana harkokin diflomasiyya sun bayyana cewa kalaman Trump na iya dagula dangantaka tsakanin Amurka da Nijeriya, musamman ganin yadda Chana ke ƙara ƙarfafa hulɗar tattalin arziki da diflomasiyya da Nijeriya a ƙarƙashin tsarin BRICS.
Chana ta kasance ɗaya daga cikin manyan abokan hulɗar tattalin arziki na Nijeriya, tana zuba jari a fannoni da dama kamar makamashi, gine-gine da fasahar zamani, tare da nuna goyon bayan siyasa da diflomasiyya ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.







