• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
November 2, 2025
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Gwamnan CBN ya gargaɗi masu wulaƙanta takardar Naira
Mista Olayemi Cardoso, Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN)

Mista Olayemi Cardoso, Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN)

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Mista Olayemi Cardoso, ya yi magana dangane da ƙoƙarin da bankuna ke yi domin ganin sun cika sharuɗɗan adadin ƙarfin jari da CBN ya gindaya masu.

Ya ce da yin hakan zai sa a guje wa sake maimata kurakuran da aka taɓa yi can a baya.

“Mun bai wa bankunan kasuwanci isasshen lokaci da kuma zaɓi domin ganin sun cika sharuɗɗan da aka gindaya masu. Saboda haka ba wani abin tayar da hankali ko razana a nan,” inji Cardoso.

Da yake magana kan batun tsare-tsaren inganta tattalin arziki, kuɗaɗen ruwa da kuma taƙaita karɓar lamuni daga masu kasuwanci, gwamnan ya ce tilas batun bunƙasa tattalin arziki mai ɗorewa shi ne farkon abin dubawa, kafin a yi maganar batun rance mai karsashi.

“Domin idan tattalin arziki bai samu nagartaccen tushe ko tubali na, to samun ci gaba ba zai yiwu ba. Maganar cewa kuɗin ruwa ya yi tsada kuma haka ɗin ne, amma tunda tattalin arziki ya hau kan miƙaƙƙar hanya, za a sassauta kuɗin ruwan.”

Ya yi wannan jawabi wurin taron da London Business School tare da haɗin gwiwar JP Morgan da Goldman Sachs suka shirya.

A wani labarin kuma, Ministan Harkokin Kuɗaɗe, Wale Edun, ya jinjina wa Gwamnan CBN, Cardoso, dangane da nasarorin da yake samu wajen aiwatar da tsare-tsaren tattalin arzikin ƙasa masu tasirin daƙile tsadar rayuwa da kuma taka wa hauhawar farashin kayayyaki burki.

Edun ya yi bayanin a wurin taron da Cibiyar Chartered Institute of Bankers of Nigeria (CIBN) ta shirya, a Legas.

Ya ce CBN na ƙoƙari matuƙa wajen dawo wa tattalin arzikin Nijeriya da tsarin hada-hadar kuɗaɗe darajar su a idon masu zuba jari.

Tags: CBNOlayemi Cardoso
Previous Post

CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

Next Post

Chana ta gargaɗi Amurka da ta daina tsoma baki a ƙasashen waje kan zargin tauye ‘yancin addini

Related Posts

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya ƙara ba da fifikon sa-ido wajen daƙile hadahadar kuɗaɗen ɗaukar nauyin ta’addanci

September 9, 2026
Next Post
Chana ta gargaɗi Amurka da ta daina tsoma baki a ƙasashen waje kan zargin tauye ‘yancin addini

Chana ta gargaɗi Amurka da ta daina tsoma baki a ƙasashen waje kan zargin tauye ‘yancin addini

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!