• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Kiwon Lafiya

Gwamnatin Tarayya ta ce babu tabbacin ɓullar cutar Ebola a Nijeriya, jama’a su kwantar da hankalin su

Fati Abdul by Fati Abdul
July 9, 2026
in Kiwon Lafiya
A A
0
Gwamnatin Tarayya ta ce babu tabbacin ɓullar cutar Ebola a Nijeriya, jama’a su kwantar da hankalin su
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na Ƙasa, Mohammed Idris

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na Ƙasa, Mohammed Idris

ABUJA – Gwamnatin Tarayya ta tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa babu wani tabbataccen rahoton ɓullar cutar Ebola a ƙasar nan, tare da kira ga jama’a da su kwantar da hankalin su, amma su ci gaba da kasancewa cikin shiri da taka-tsantsan.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, shi ne ya bayar da wannan tabbaci a yau Alhamis a Abuja yayin taron farko na Kwamitin Sadarwa na Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Shirye-shiryen Tunkarar Cutar Ebola da Barazanar Sabbin Cututtukan Lafiyar Jama’a.

Idris ya ce duk da cewa babu tabbacin ɓullar cutar Ebola a Nijeriya, sababbin abubuwan da suka faru a wasu ƙasashen Afrika sun nuna muhimmancin ƙara shirye-shiryen kariya.

Ya ce: “Ina so in tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa a halin yanzu babu wani tabbataccen rahoton ɓullar cutar Ebola a Nijeriya. Sai dai kuma, abubuwan da ke faruwa a wasu sassan Afrika suna tunatar da mu cewa cututtuka masu yaɗuwa ba su da iyaka.”

Ministan ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa kafa wannan Kwamitin Shugaban Ƙasa, yana mai bayyana matakin a matsayin wani tsari na hangen nesa da nufin kare lafiyar al’ummar Nijeriya ta hanyar ingantaccen shiri, haɗin gwiwa da kuma ɗaukar matakan gaggawa a kan lokaci.

Ya jaddada cewa ingantacciyar sadarwa za ta kasance ginshiƙi wajen tunkarar duk wata barazanar lafiyar jama’a, yana mai cewa isar da sahihan bayanai cikin gaggawa da suka dogara da hujjojin kimiyya na iya ceton rayuka, yayin da yaɗa ƙarya da ji-ta- ji-ta ke iya raunana amincewar jama’a tare da kawo cikas ga matakan da ake ɗauka.

Idris ya tuna da yadda Nijeriya ta samu nasarar daƙile ɓarkewar Ebola a shekarar 2014, inda ya danganta wannan nasara da kyakkyawan jagoranci, haɗin gwiwar hukumomi, ingantaccen sa ido kan cututtuka da kuma ci gaba da wayar da kan jama’a.

A cewar sa, Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA) ta riga ta fara yaƙin wayar da kan jama’a a faɗin ƙasar ta hanyar amfani da saƙonnin lafiya da aka amince da su, waɗanda aka tsara tare da haɗin gwiwar Cibiyar Kula da Cututtuka da Rigakafi ta Nijeriya (NCDC).

Ya sake jaddada cewa saƙon gwamnati a bayyane yake: babu tabbataccen ɓullar cutar Ebola a Nijeriya, babu dalilin fargaba, kuma hukumomin da abin ya shafa suna cikin cikakken shiri tare da sanya ido sosai.

Ministan ya kuma buƙaci ‘yan Nijeriya da su ci gaba da kiyaye tsafta, su gaggauta sanar da hukumomin lafiya idan sun ga alamun da ake zargin na cutar, sannan su dogara ne kawai da sahihan bayanai daga hukumomin gwamnati.

Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai Karamin Ministan Harkokin Waje kuma Mataimakin Shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa, Ambasada Sola Enikanolaiye; Ministan Sufurin Jiragen Sama da Bunƙasa Harkokin Sararin Samaniya, wanda Mataimakinsa na Musamman kan Sadarwar Zamani, Saka Olugbenga, ya wakilta; Darakta Janar na Cibiyar Kula da Cututtuka da Rigakafi ta Nijeriya (NCDC), wanda Dakta Tochi Okwor ya wakilta; Darakta Janar na Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA), Mallam Lanre Issa-Onilu; Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ), Kwamared Alhassan Yahya; Shugaban Cibiyar Hulɗa da Jama’a ta Nijeriya (NIPR), Dakta Ike Neliaku; da Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Editocin Nijeriya (Arewa), Hamza Idris, tare da sauran masu ruwa da tsaki.

Tags: cutaEbolafaɗakarwakwamitiMohammed Idris
Previous Post

Aikin sake gina titin Abuja–Kaduna ya kai kashi 85% na kammaluwa – Gwamnati

Next Post

Kasuwar Hannun Jari ta Nijeriya ta kasance cikin mafi bunƙasa a duniya – Masana

Related Posts

Ranar Zuciya ta Duniya: Idris ya yi kira da a ƙara kaimi wajen yaƙi da cututtukan zuciya
Kiwon Lafiya

Ranar Zuciya ta Duniya: Idris ya yi kira da a ƙara kaimi wajen yaƙi da cututtukan zuciya

September 30, 2026
Gwamna Bago ya ƙaddamar da kayan aikin asibiti na Naira miliyan 100 domin inganta harkar lafiya a Neja
Kiwon Lafiya

Gwamna Bago ya ƙaddamar da kayan aikin asibiti na Naira miliyan 100 domin inganta harkar lafiya a Neja

August 19, 2026
Rigakafi: Tinubu ya kafa kwamitin gaggawa kan Ebola, ya amince da kashe naira biliyan 10 don shirin ba da kariya
Kiwon Lafiya

Rigakafi: Tinubu ya kafa kwamitin gaggawa kan Ebola, ya amince da kashe naira biliyan 10 don shirin ba da kariya

June 9, 2026
Tinubu ya naɗa Fatima Zuntu shugabar hukumar NBMA
Kiwon Lafiya

Tinubu ya naɗa Fatima Zuntu shugabar hukumar NBMA

April 20, 2026
Likitoci za su fara yajin aiki na gama-gari daga Talata
Kiwon Lafiya

Likitoci za su fara yajin aiki na gama-gari daga Talata

April 5, 2026
Uwargidan Shugaban Ƙasa ta ƙaddamar da Asusun Ciyarwar Abinci na Ƙasa, ta ba da gudunmawar naira miliyan 500
Kiwon Lafiya

Uwargidan Shugaban Ƙasa ta ƙaddamar da Asusun Ciyarwar Abinci na Ƙasa, ta ba da gudunmawar naira miliyan 500

April 3, 2026
Next Post
Kasuwar Hannun Jari ta Nijeriya ta kasance cikin mafi bunƙasa a duniya – Masana

Kasuwar Hannun Jari ta Nijeriya ta kasance cikin mafi bunƙasa a duniya - Masana

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!