Ƙungiyar Ƙwararrun Likitoci ta Nijeriya (NARD) ta ayyana fara cikakken yajin aiki na ƙasa baki ɗaya wanda ba shi da wa’adi, daga ƙarfe 12 na daren ranar Talata, 7 ga Afrilu, 2026, sakamakon matakin da Gwamnatin Tarayya ta ɗauka na dakatar da aiwatar da Teburin Alawus na Ƙwararru (PAT).
NARD ta bayyana matakin da gwamnatin ta ɗauka na cire PAT a matsayin abin takaici kuma wanda ba za su amince da shi ba.
Ƙungiyar ta ce membobin ta sun yanke shawarar shiga cikakken yajin aiki bayan tattaunawa mai zurfi, ta ƙara da cewa za su dakatar da yajin aikin ne kawai idan an biya buƙatun su.
Daga cikin buƙatun nasu, NARD ta buƙaci a gaggauta janye matakin dakatar da aiwatar da PAT daga Afrilu 2026.
Ƙungiyar ta kuma buƙaci a biya bashin ƙarin girma da kuma sauran bashin albashi da ake bin likitoci a cibiyoyin da abin ya shafa a faɗin ƙasar nan.
Haka kuma ta buƙaci a gaggauta kammala tsarin biyan kuɗin Asusun Horar da Likitocin Residency na shekarar 2026 (MRTF).
NARD ta kuma buƙaci a gaggauta aiwatar da biyan bashin watanni 19 na alawus na ƙwararru da ke ƙarƙashin PAT.
An cimma wannan matsaya ne a yayin wani taron gaggawa na majalisar zartarwa ta ƙasa (NEC) ta ƙungiyar wanda aka gudanar ta yanar gizo a ranar 4 ga Afrilu, 2026, kamar yadda Babban Sakataren ƙungiyar, Dakta Shu’aibu Ibrahim, ya bayyana a cikin wata sanarwa yau Asabar.
Majalisar ta buƙaci membobin ta a faɗin ƙasar nan da su kasance masu haɗin kai tare da ci gaba da jajircewa a kan yajin aikin har sai an biya buƙatun su.
Ta ce: “Shugabancin NARD na kira ga membobin ta da su haɗa kai a wannan gwagwarmaya da ake yi da wannan rashin adalci, tare da ƙudirin kai ta zuwa ƙarshe mai ma’ana.”







