Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Alhaji Mohammed Idris, ya buƙaci a ƙara ƙaimi wajen daƙile cututtukan zuciya da jijiyoyin jini, da gano su da wuri, tare da faɗaɗa damar samun magani.
Idris ya yi wannan kira ne ranar Talata a Abuja, a cikin saƙon da Darakta-Janar na Hukumar Rediyon Tarayya ta Nijeriya (FRCN), Dakta Mohammed Bulama, ya isar a madadin sa yayin bikin Ranar Zuciya ta Duniya ta 2026, wanda gidauniyar “Heart Recovery Foundation” (HRF) ta shirya.
Ministan ya jaddada muhimmancin samar da sahihan bayanan kiwon lafiya ga jama’a domin taimaka musu fahimtar cututtukan zuciya da jijiyoyin jini, gane alamomin haɗari da kuma neman kulawar likita da wuri.
Ya ce: “Jama’ar ƙasa suna buƙatar sahihan bayanai, masu sauƙin samu da fahimta, game da rayuwa mai inganci, alamomin haɗari, abubuwan da ke jawo cututtuka da kuma lokacin da ya kamata a nemi kulawar likita.”
Idris ya bayyana matakan da gwamnati take ɗauka wajen ƙarfafa harkar kiwon lafiya, ciki har da farfaɗo da Cibiyoyin Kiwon Lafiya na Matakin Farko da faɗaɗa cibiyoyin kiwon lafiya na musamman. Sai dai ya jaddada cewa gwamnati ba za ta iya magance matsalar ita kaɗai ba.
“Amma a lokaci guda, gwamnati ba za ta iya yin hakan ita kaɗai ba,” inji shi, yana kira da a ci gaba da haɗin gwiwa tsakanin gwamnati, ƙwararrun ma’aikatan lafiya, ƙungiyoyin farar hula, abokan hulɗar cigaba da kafafen yaɗa labarai.
Shugaban Kwamitin Amintattu na HRF, Dakta Suleiman Haruna, ya ce ayyukan gidauniyar sun wuce ba da magani kawai, domin tana taimaka wa iyalan da cututtukan zuciya suka shafa wajen farfaɗo da rayuwar su.
“Ba maganin zuciya kawai muke yi ba. Muna farfaɗo da iyalai, muna farfaɗo da sana’o’i, sannan muna farfaɗo da rayuwar yara,” inji shi.
Wanda ya kafa gidauniyar, Gilbert Kiaka, ya ce irin ƙwarewar da ya samu sakamakon fama da cutar zuciya ce ta zaburar da shi wajen bayar da gudunmawa a wannan fanni.
Ya jaddada buƙatar tabbatar da cewa talauci bai hana yara samun maganin da suke buƙata ba.
“Bai kamata talauci ya zama abin da zai ƙayyade ko yaro zai rayu ko ya mutu sakamakon cutar zuciya da za a iya magancewa ba,” inji shi.
A cikin jawabin babban baƙo, Shugaban Ƙungiyar Likitocin Zuciya da Ƙirji ta Nijeriya, Farfesa Umar Abubakar, ya yi kira da a ƙarfafa tsarin da ke haɗa gano cuta da samun magani.
“Gano cuta kaɗai bai isa ba; dole ne a samar da damar samun magani,” inji shi, yana buƙatar samar da ingantaccen tsarin tallafin kuɗi, ƙarfafa ƙwarewar cikin gida da kuma ƙara haɗin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki.
An gudanar da taron ne ƙarƙashin taken “Yi Amfani da Zuciya Wajen Aiki”, inda ya samu halartar ƙwararrun ma’aikatan lafiya, masu fama da cututtukan zuciya da waɗanda suka warke, abokan hulɗar cigaba, jami’an diflomasiyya, ma’aikatan kafafen yaɗa labarai da sauran masu ruwa da tsaki.
An gabatar da lambobin yabo na musamman kan hidimar jinƙai ga mutane da ƙungiyoyin da aka yaba da gudunmawar su ga ayyukan jinƙai da wayar da kan jama’a kan lafiyar zuciya.






