• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Kiwon Lafiya

Rigakafi: Tinubu ya kafa kwamitin gaggawa kan Ebola, ya amince da kashe naira biliyan 10 don shirin ba da kariya

Wakilin Mu by Wakilin Mu
June 9, 2026
in Kiwon Lafiya
A A
0
Rigakafi: Tinubu ya kafa kwamitin gaggawa kan Ebola, ya amince da kashe naira biliyan 10 don shirin ba da kariya
Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa Kwamitin Musamman na Fadar Shugaban Ƙasa kan Shirin Kariya daga Cutar Ebola da Sauran Barazanar Lafiyar Jama’a, tare da bayar da umurnin sakin naira biliyan 10 domin shirye-shiryen gaggawa.

A cewar sanarwar da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar yau Talata, kuɗaɗen za su taimaka wajen ƙarfafa shirye-shiryen Hukumar Yaƙi da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Ƙasa (NCDC) da kuma ayyukan da suka shafi tunkarar duk wata barazanar gaggawa ga lafiyar al’umma.

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, shi ne zai jagoranci sabon kwamitin, wanda zai haɗa da wakilai daga ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnati daban-daban, da kuma wakilan jihohi.

Matakin ya biyo bayan sake ɓullar cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokiraɗiyyar Kongo (DRC) da kuma Uganda.

Shugaba Tinubu ya amince da kafa kwamitin ne bayan wani taron masu ruwa da tsaki da shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa ya jagoranta domin nazarin irin shirin da Nijeriya ta yi da kuma dabarun da za su hana cutar shiga ƙasar nan.

Daga cikin mahalarta taron akwai wakilai daga Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Ƙasa (FAAN), Hukumar Shige da Fice (NIS), Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama (NCAA), da gwamnatin Jihar Legas.

Shugaban Ƙasar ya kuma umurci dukkan jihohin da ke da filayen jiragen sama na ƙasa da ƙasa da kuma manyan hanyoyin shiga ƙasar nan daga ƙasashen waje da su gabatar da tsare-tsaren su, buƙatun kuɗi da irin tallafin da suke buƙata domin aiwatar da matakan kariya cikin haɗin gwiwa.

A cikin matakan da aka bayyana za a ɗauka akwai ƙara tsaurara binciken fasinjoji a dukkan filayen jiragen sama na ƙasa da ƙasa, ciki har da duba zafin jiki da tsara yadda jama’a ke shiga da fita.

Haka kuma za a ƙarfafa sa ido kan fasinjojin da ke shigowa ta wasu hanyoyin jiragen sama da gwamnati ta ayyana a matsayin masu haɗari, ciki har da Air Uganda, RwandAir, Air Tanzania, Air Angola, Kenya Airways da Ethiopian Airlines.

Gwamnatin ta ce za a gaggauta bude cibiyoyin killace marasa lafiya da wuraren tura waɗanda ake zargin sun kamu da cutar a filayen jiragen saman Legas da Abuja, kafin daga baya a faɗaɗa tsarin zuwa sauran filayen jiragen saman ƙasar.

Sauran matakan sun haɗa da wajabta cike bayanan lafiyar matafiya ta hanyar tsarin QR Code kafin su iso ƙasar idan sun fito ko suka bi ta ƙasashen da aka ayyana masu haɗari, da kuma tsaftace ɗakunan tashi da saukar jirage, wuraren kaya da sauran sassan filayen jiragen sama.

Shugaba Tinubu ya kuma umurci kwamitin da ya tattauna da hukumomin tsaro, diflomasiyya da sufurin jiragen sama kan yiwuwar ɗaukar ƙarin matakan da suka shafi zirga-zirgar jirage daga ƙasashen da cutar ta bulla ko waɗanda aka sanya cikin jerin masu haɗari.

Bugu da ƙari, kwamitin zai duba yiwuwar ware wasu filayen jiragen sama ko tashoshi na musamman domin karɓar jiragen da ake ganin suna da haɗari, tare da nazarin sauya lokutan saukar wasu jirage domin rage haɗuwar fasinjojin da ake sa ran za su buƙaci ƙarin bincike da sauran matafiya.

Tags: EbolaKongokwamitirigakafiShugaba Bola Ahmed Tinubu
Previous Post

Ranar Dimokiraɗiyya ta 2026: Tinubu yana gina ƙwaƙƙwarar Nijeriya, ta kowa da kowa – Minista

Next Post

Asusun IMF ya jinjina wa manufofin kuɗi na CBN, ya yaba da shirin ƙarfafa jarin bankuna

Related Posts

Ranar Zuciya ta Duniya: Idris ya yi kira da a ƙara kaimi wajen yaƙi da cututtukan zuciya
Kiwon Lafiya

Ranar Zuciya ta Duniya: Idris ya yi kira da a ƙara kaimi wajen yaƙi da cututtukan zuciya

September 30, 2026
Gwamna Bago ya ƙaddamar da kayan aikin asibiti na Naira miliyan 100 domin inganta harkar lafiya a Neja
Kiwon Lafiya

Gwamna Bago ya ƙaddamar da kayan aikin asibiti na Naira miliyan 100 domin inganta harkar lafiya a Neja

August 19, 2026
Gwamnatin Tarayya ta ce babu tabbacin ɓullar cutar Ebola a Nijeriya, jama’a su kwantar da hankalin su
Kiwon Lafiya

Gwamnatin Tarayya ta ce babu tabbacin ɓullar cutar Ebola a Nijeriya, jama’a su kwantar da hankalin su

July 9, 2026
Tinubu ya naɗa Fatima Zuntu shugabar hukumar NBMA
Kiwon Lafiya

Tinubu ya naɗa Fatima Zuntu shugabar hukumar NBMA

April 20, 2026
Likitoci za su fara yajin aiki na gama-gari daga Talata
Kiwon Lafiya

Likitoci za su fara yajin aiki na gama-gari daga Talata

April 5, 2026
Uwargidan Shugaban Ƙasa ta ƙaddamar da Asusun Ciyarwar Abinci na Ƙasa, ta ba da gudunmawar naira miliyan 500
Kiwon Lafiya

Uwargidan Shugaban Ƙasa ta ƙaddamar da Asusun Ciyarwar Abinci na Ƙasa, ta ba da gudunmawar naira miliyan 500

April 3, 2026
Next Post
Asusun IMF ya jinjina wa manufofin kuɗi na CBN, ya yaba da shirin ƙarfafa jarin bankuna

Asusun IMF ya jinjina wa manufofin kuɗi na CBN, ya yaba da shirin ƙarfafa jarin bankuna

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!