• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Mahanga

Bayan wuya, sauƙi ya fara bayyana a Nijeriya – Tinubu

CIKAKKEN JAWABIN MAI GIRMA BOLA AHMED TINUBU, GCFR, SHUGABAN TARAYYAR NIJERIYA KAN CIKAR ƘASAR SHEKARU 65 DA SAMUN `YANCIN-KAI, A RANAR 1 GA OKTOBA, 2025.

SHUGABA BOLA AHMED TINUBU by SHUGABA BOLA AHMED TINUBU
October 1, 2025
in Mahanga
A A
0
Bayan wuya, sauƙi ya fara bayyana a Nijeriya – Tinubu
Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Ya ‘yan’uwa na ‘yan Nijeriya.

Yau ce ranar da wannan ƙasa tamu mai girma ke cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai. A yayin da muke bitar muhimmancin wannan rana da tuna yadda ƙasar mu ta faro tun daga rana irin ta yau, wato 1 ga Oktoba, 1960, ranar da gwarazan iyayen mu suka karɓi shaidar samun mulkin cin gashin kai daga Turawan mulkin mallaka, dole ne mu tuna da sadaukarwar su, da ƙwazon su, da ma babban burin su na samun tsayayyiya, wadatacciya kuma dunƙullalliyar Nijeriya, wadda za ta jagoranci Afrika, kana ta zama yar manuniya ga sauran ƙasashen duniya.

2. Gwarazan gwagwarmayar kafa ƙasar mu maza da mata—irin su Herbert Macaulay, Dakta Nnamdi Azikiwe, Sa Abubakar Tafawa Ɓalewa, Cif Obafemi Awolowo, Sa Ahmadu Bello, Margaret Ekpo, Anthony Enahoro, Ladoke Akintola, Michael Okpara, Aminu Kano, Funmilayo Ransome-Kuti, da sauran ‘yan ƙasa — sun yi imani da cewa a matsayin Nijeriya na ƙasar baƙar fata mafi girma a duniya, Allah ya ƙaddara mata jagorancin dukkan baƙar fata a duniya.

3. Tabbas, tsawon shekaru da dama, ‘yancin kan mu ya fuskanci ƙalubale mai tsanani a fannin zamantakewa, tattalin arziki, da siyasa, sai dai duk da haka mun yi nasara. Ta yiwu ba mu cika wa magabatan mu dukkan manyan burikan su ba, amma ba mu juya wa muradun su baya ba, domin a cikin shekaru 65 da samun ‘yancin kan mu, mun samu cigaba mai tarin yawa a fannonin da suka haɗa da tattalin arziki da haɗin kan ‘yan ƙasa. Ko shakka babu, daga shekarar 1960 zuwa yanzu, tattalin arzikin mu ya samu cigaba sosai.

4. Koda yake abu ne me sauƙi ga idanun masu kallon abu ta ɓangare ɗaya su kasa hango irin cigaban da aka samu, sai dai ya zama dole mu fahimci irin abubuwan cigaba masu muhimmanci da ƙasar mu ta rabauta da su, har ma mu yi murna. ‘Yan Nijeriya a yau suna da damar samun ingantaccen ilimi da kiwon lafiya fiye da na 1960. A lokacin samun ‘yancin kai, Nijeriya tana da makarantun sakandare 120 tare da yawan ɗalibai kusan 130,000. Amma bayanai sun nuna cewa a ƙarshen 2024 akwai makarantun sakandare sama da 23,000 a ƙasar mu. A lokacin ‘yancin kai, muna da Jami’ar Ibadan da Kwalejin Fasaha ta Yaba ne kawai a matsayin cibiyoyin manyan makarantun Nijeriya. A ƙarshen shekarar da ta gabata akwai jami’o’i 274, kwalejojin kimiyya da fasaha 183, da Kwalejin Ilimi 236 a Nijeriya, waɗanda suka haɗa da cibiyoyin Gwamnatin Tarayya, na jihohi, da na masu zaman kan su. Tabbas, mun samu gagarumin cigaba a kowane fanni na rayuwar mu daga samun ‘yancin kai zuwa yanzu – a fannin kiwon lafiya, samar da ababen more rayuwa, hadahadar kuɗi, masana’antu, sadarwa, fasahar zamani, jiragen sama, tsaro, da sauran su.

5. A cikin shekaru 65, ƙasar mu ta ɗanɗana zaƙi da ɗacin kasancewar ta ƙasa, kamar yadda yake iya faruwa ga kowace ƙasa da jama’ar ta. Mun ɗanɗana yaƙin basasa, mun ɗanɗana mulkin soja, kana mun rayu a cikin manyan matsalolin siyasa. Sai dai babu ɗaya daga cikin waɗannan ƙalubale da jarumtakar mu da juriyar mu ba su ga bayan su ba. Ko da yake wasu lokuta masu adawa da cigaban mu da al’adun mu kan yi wa tsarin mu da danƙon zumuncin mu zagon ƙasa, hakan ba zai hana mu ci gaba da ƙoƙarin samar da dausayin da kowane dan Nijeriya zai rayu cikin walwala, hadafi da cikar burin sa ba.

6. ‘Yan’uwa na ‘yan ƙasa nagari, karo na uku kenan da na samu damar yi maku jawabi a ranar cika shekaru da samin ‘yancin kan mu tun bayan da na zama Shugaban ku a ranar 29 ga Mayu, 2023. A cikin watanni 28 da suka gabata na gwamnati na, na yi koyi da jajircewar iyayen ƙasar mu, da sauran shugabannin da suka gabace ni wajen yin tsayin daka a kan aikin gina ƙasa da bai kammala ba.

7. Da muka hau mulki, gwamnatin mu ta gaji tsarin tattalin arziki da ke gab da rushewa wanda ya samo asali daga shekaru da dama na karkatar da manufofin kasafin kuɗi da rashin daidaito, wanda ya yi lahani na gaske ga cigaban mu. A matsayin sabuwar gwamnati, muna da zaɓi mai sauƙi: ko dai mu ci gaba da gudanar da al’amurra kamar yadda aka saba muna kallo ƙasar mu na cigaban mai haƙar rijiya, ko kuma mu shiga aikin gyara tuƙuru cikin kau da kai da juriya. Gaskiya mun zaɓi hanyar gyara. Mun zaɓi jin daɗin gobe da jibi a kan na yau kawai. Mun ɗauki matsaya mai wahala, amma ƙasa da shekara uku ta fara samar da ɗa mai ido.

8. Duk don mu ɗora ƙasar mu kan doron manufa muka kawo ƙarshen tallafin man fetur da ke cike da cin hanci da rashawa, haka ma a fannin hadahadar kuɗaɗen ƙasashen waje mun toshe kafar da ke taƙaita walwalar tattalin arzikin ga amfanin ‘yan tsiraru, su hana talakawa komai daga dukiyar ƙasar mu. Gwamnatin mu ta sake mayar da tattalin arzikin zuwa hanyar da za ta wadaci kowa da kowa, ta hanyar karkatar da kudi don samar da ilimi, kiwon lafiya, tsaron kasa, noma, da muhimman ababen more rayuwa da habaka tattalin arziki, kamar samar da manyan hanyoyi, wutar lantarki, da samar da jarin yau da kullum. Waɗannan tsare-tsare su ne za su inganta rayuwar ‘yan Nijeriya gaba ɗaya. A sakamakon dabarun da muka ɗauka na daƙile manyan matsaloli, a yanzu daga Gwamnatin Tarayya zuwa gwamnatin iihohi, kai har da Ƙananan Hukumomi, babu wanda bai sami isassun kula da jama’ar sa a kowane mataki ba.

9. Ya ku ‘yan’uwa ‘yan Nijeriya, ba mu da sauran lokaci. Dole ne mu tashi tsaye mu gina hanyoyin da ƙasar mu ke bukata, mu gyara waɗanda suka lalace, kana mu gina makarantun da ‘ya’yan mu za su je da kuma asibitocin da za su kula da jama’ar mu. Dole ne mu yi shiri don zuri’ar da za ta zo bayan mu. Ta dalilin kasa zuba dukiyar kasar mu a inda ya dace tun shekaru aru-aru, mun wayi gari ba mu da wadatacciyar wutar lantarki da za ta kunna masana’antun mu da gidajen mu a yau, ba mu da wadatar da za mu gyara hanyoyin mu da suka lalace, ko kuma gina tashoshin jiragen ruwa, ko na kasa, kai har da filayen jiragen sama da za su iya jera kafaɗa da mafi kyau a duniya. Gwamnatin mu ba ta ga ta zama ba, ta duƙufa gyara abubuwa.

10. Ina farin cikin sanar da ku cewa a ƙarshe mun shawo kan manyan matsalolin mu. Mafiya munin sun wuce, ina faɗa ina ƙara faɗi, kowane tsanani na tare da sauƙi. Na yaba wa juriyar da kuka nuna. Ina tabbatar maku da cewa haɗin kan da kuka ba ni ya samar min da ƙwarin gwiwar da ba zan gushe ba ina aiki tuƙuru, har sai na kai ƙasar mu tudun mun-tsira.

11. A ƙarƙashin jagorancin mu, tattalin arzikin mu yana farfaɗowa cikin hanzari, kuma sauye-sauyen da muka faro shekaru biyu da suka gabata suna bada sakamako mai ma`ana. Alƙaluman kuɗin shiga na zango na biyu na shekarar 2025 ya nuna ƙaruwa da kashi 4.23 cikin ɗari—wanda shi ne cigaba mafi sauri a Nijeriya a cikin shekaru huɗu — har ma ya zarce kashi 3.4 da Asusun Bada Lamuni na Duniya (IMF) ya yi hasashen za a samu. Hauhawar farashin kayayyaki ya ragu zuwa kashi 20.12% a watan Agusta 2025, abin da bai taɓa faruwa ba a cikin shekaru 3 da suka gabata. Gwamnati na aiki tuƙuru don haɓaka noman ababen masarufi na yau da kullum don tabbatar da samar da abinci da zai rage farashin abinci.

12. A cikin shekaru biyu da suka gabata na gwamnatin mu, mun cimma muhimman nasarori 12 na tattalin arziki sakamakon aiwatar da ingantattun manufofinmu na kasafin kudi da na kudi: ga su kamar haka:

• Mun sami karin kudaden shiga da ga albarkatun da ba na man fetur ba, inda muka cimma burinmu na 2025 kafin watan Agusta ta hanyar samin fiye da Naira Tiriliyan 20, wannan wani abin ya shiga tarihi ne. A watan Satumba 2025 kadai, mun tara Naira Tiriliyan 3.65, wanda ya ninka adadin da aka tara a watan Mayu 2023 da kashi 411%.

• . Mun farfado da darajar Kasafin Kudi: sabon tsarin biyan bashin da muke bi idan aka kwatanta da kudaden shiga ya ragu sosai daga kashi 97% zuwa kasa da kashi 50%. Mun biya “Ways and Means” da ke barazana ga kwanciyar hankalin tattalin arzikinmu har ma da haifar da hauhawar farashi. Bayan cire tallafin man fetur mai cike da cin hanci da rashawa, mun karkata Triliyoyin Naira zuwa ga ainahin hannayen jarin tattalin arziki da zai inganta rayuwar yan kasa marasa galihu.

• Mun dada garajar Asusun Ajiyar Kasa fiye da yadda yake a shekaru uku da suka gabata. A yanzu asusun ajiyar mu na waje ya karu zuwa Dala Biliyan $42.03 a wannan watan Satumba—wanda shine mafi girma tun 2019.

• Harajinmu na kudaden shiga ya tashi daga kaso 10 zuwa kashi 13.5, kuma ana sa ran darajar za ta karu idan sabuwar dokar haraji ta fara aiki a watan Janairun badu. Sai dai a sani! Dokar haraji ba ta nufin kara wa masu biyan haraji nauyi, sai ma ragin harajin da ake Shirin yi wa masu karamin karfi, manufar dokar ita ce tattaro kudaden harajin tun daga tushe don gina Nijeriyar da muke mafarki.

• Yanzu mu ne kan gaba a masu fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje (Net Exporter): Nijeriya ta rubanya karin cinikayya (trade surplus) har sau biyar a jere. Yanzu muna sayar da abubuwa da yawa ga duniya fiye da yadda muke saya, wani canji mai mahimmanci wanda ke karfafa kudinmu da samar da ayyukan yi a gida. Karin cinikayyar Nijeriya ya karu da kashi 44.3% a Q2 2025 zuwa ₦7.46 Tiriliyan ($4.74 Biliyan), wanda shine mafi girma a cikin kusan shekaru uku. Kayan da aka kera a Nijeriya kuma aka fitar sun karu da kashi 173%. Kayayyakin da ba danyen mai ba, sune kashi 48 a bangaren cinikayyar fitar da kayanmu, idan aka kwatanta da fitar da mai, wanda ya kai kashi 52%. Wannan yana nuna cewa mun fara raba tattalin arzikinmu da tushen kudin waje da ake samowa daga danyen mai da iskar gas.

• Samar da danyen mai ya karu daga ganga kasa da milyan daya a watan Mayun 2023 zuwa ganga miliyan 1.68 a rana. Wannan karin ya samu ne sakamakon ingantaccen tsaro, da sabbin hannayen jari, da kula da hakkokin masu ruwa da tsaki a yankin Neja Delta. Bugu da kari, kasar ta samu gagarumin ci gaba ta hanyar tace man fetur (PMS) a cikin gida a karon farko cikin shekaru arba’in. Haka kuma ta kafa kanta a matsayin jagorar fitar da man jirgin sama a nahiyar Afirka.

• Naira ta farfado daga rikta-riktar da ta sami kanta a tsakanin shekarar 2023 da ta 2024. Gibin da ke tsakanin farashin gwamnati da na kasuwar bayan fage ya ragu ainun, biyo bayan gyare-gyaren FX da sabbin kudaden shiga da ke rufa mata baya. Kazamar ribar da ake ci a hada-hadar Naira a baya yanzu ta zama tarihi. Kazalika farashin Nairar mu ya dena dogara da farashin danyen mai.

• A karkashin shirye-shiryen zuba jari na zamantakewa don tallafa wa iyalai masu rangwamen gata a Nijeriya, an raba Naira Biliyan 330 ga iyalai miliyan takwas, akasarinsu sun karbi ko dai kashi daya ko biyu na kashi uku na Naira 25,000 kowanne.

• An farfado da hakar ma`adinin kwal sosai daga raguwar da yayi na kashi 22% a Q1 a baya zuwa karuwar kashi 57.5% a Q2, inda ya zama kan gaba cikin jerin ma`aninan Najeriya masu saurin murmurewa. Hakan na nufin sashin hakar ma’adanai ya sami gurbin zama mai muhimmanci a cikin tattalin arzikin kasarmu, ma`adinan da ke karkashin kasarmu sun zama kashin bayan samar da kayayyaki masu daraja.

• Gwamnati na ci gaba da aikin fadada kayayyakin more rayuwa a bangaren sufuri a duk fadin kasar, wanda suka hada da samar da jiragen kasa, manyan hanyoyi, filayen saukar jiragen sama, da tashoshin jiragen ruwa. Sufurin jirgin kasa da na ruwa, duk sun karu da fiye da 40% da 27%, bi da bi. Aikin layin dogo na Kano-Kastina-Maradi Standard Gauge mai tsawon kilomita 284 da layin dogo na Kaduna-Kano suna gab da kammalawa. Haka ma aikin titin Lagos-Calabar Coastal Highway da Sokoto-Badagry Highway duk sun yi nisa. Majalisar Zartaswa ta Tarayya kwanan nan ta amince da Dala Biliyan $3 don kammala Aikin Jirgin Kasa a gabashin kasar nan.

• Duniya ta fara farga da kokarinmu. Hukumomin sa ido kan tattalin arziki da bayar da lamuni na kasa da kasa sun fara sauya Kallon da da suke wa Nijeriya a baya, yanzu suna gamsuwa da ingantattun matakanmu na tattalin arziki. Kasuwancinmu na hannun jari yana samun ci gaba da ba a taba gani ba, inda ya tashi daga ma’aunin index na 55,000 a watan Mayu 2003 zuwa 142,000 a ranar 26 ga Satumba, 2025.

• A taron kwamitin manufofin kudi (MPC) na baya-bayan nan, Babban Bankin ya rage kudin ruwa a karon farko a cikin shekaru biyar, yana nuna amincewa da kwanciyar hankali na tattalin arzikin kasarmu.

TSARO

13. Muna aiki tukuru don inganta tsaron kasa, don tabbatar da cewa tattalin arzikinmu ya samu ingantaccen ci gaba. Dakarun sojojinmu da sauran hukumomin tsaro suna aiki ba dare ba rana, suna sadaukar rayuwarsu don kiyaye rayukanmu da dukiyoyin mu. Kuma suna cin nasara a yakin da muke yi da ta’addanci, fashi, da ma sauran manyan laifuka. Muna ganin nasarorin su a cikin jinin su da gumin su don kawar da Ta’addancin Boko Haram a Arewa maso Gabas, ta’addancin IPOB/ESN a Kudu maso Gabas da fashi da garkuwa da mutane. Dole ne mu ci gaba da yaba musu da jinjinawa jaruntakarsu a matsayinmu na al’ummar da ke yaba kyauta da tukuici. Zaman lafiya ya dawo ga daruruwan al’ummominmu da aka ‘yanta a Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas, kuma dubban mutanenmu sun dawo gida lafiya.

MATASA

14. Ga Sakona zuwa ga matasanmu. Ku ne kan gaba kuma kune mafi girman baiwar da Allaha yayi wa wannan kasa mai albarka. Dole ne ku ci gaba da yin manyan mafarkai, ku gina manyan tunani, ku kirkiri sabbin abubuwa, ku ci nasara a fannoni daban-daban na kimiyya, fasaha, wasanni, da kuma bangaren kere-kere. Gwamnatinmu, zata ci gaba da zuba kudaden da za su kera muku fikafikai don ku tashi sama a ku yi gudun wuce-sa`a. Mun kirkiri NELFUND don tallafa wa dalibai da lamuni don karatunsu. Kusan dalibai 510,000 a cikin jihohi 36 da FCT sun amfana da wannan shiri, wanda ake gudanarwa a manyan makarantu 228. Ya zuwa ranar 10 ga Satumba, jimlar lamunin da aka raba ya kai Naira Biliyan 99.5, yayin da kudin kula da walwalar rayuwa ya kai Naira Biliyan 44.7.

15. Credicorp, wani Shirin garabasa ne daga gwamnatinmu, ya bai wa ‘yan Nijeriya kimanin 153,000 lamuni mai rahusa har na Naira Biliyan 30 don siyan motoci, makamashin hasken rana, kayan kyale-kyalen gida, na’urorin dijital, da sauran su.

16. YouthCred, din nan da na yi alkawarin bayarwa a watan Yuni da ta gabata, shi ma yanzu ya tabbata, inda dubban ‘yan NYSC a yanzu suke cin moriyar bashi na Consumer Credit don sake daidaita komadarsu bayan kammala hidimar kasa.

17. A karkashin Ajandar Sabunta Fata Nagari (Renewed Hope Agenda), mun yi alkawarin gina Nijeriya inda kowane matashi, ko daga wane bangare ya fito, yana da damar samin ingantacciyar rayuwa—saboda haka shirin Zuba Jari a Kasuwancin Dijital da Kere-kere na (iDICE). Wanda bankin Masana’antu (Bank of Industry) ke jagorantar tare da hadin gwiwar Bankin Raya Afirka (African Development Bank), da Hukumar Raya Faransa (French Development Agency), da Bankin Musulunci (Islamic Development Bank). Wannan shiri yana gab da fara aiwatarwa. A cikin shekaru biyu da suka gabata, mun yi aiki tare da abokan huldanmu don kaddamar da shirin, wanda zai tallafa wa matasanmu da suka fara aiki da masu mafarkin farawa, duk a fannin fasaha da kirkire-kirkire.

SAƘON KYAUTATA FATA

18. Ya ku ‘Yan Nijeriya ‘Yan Uwana! Ko yaushe ina nanata cewa bana musa cewa, sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatina sun zo da radadi, amma na wucin gadi ne. Mummunan tasirin hauhawar farashi da karuwar kudin akan ababen yau da kullun sun kasance babban abin damuwa ga gwamnatinmu. Sai dai, zabin da zai kai kasarmu ga fadawa cikin rikicin tattalin arziki ko dauwamammiyar fatara ba zabi ne me kyau ba. Ci gaban tattalin arzikinmu ya tabbatar da cewa sadaukarwarmu ba ta tafi a banza ba. Da ni da ku, muke kafa sabon harsashi da aka zubawa kankare, ba na tubalin toka ba.

19. Na lashi takobin ganin ma’aunin nasarar mu bai takaita ga alkaluman kididdigar tattalin arziki dake rubuce a zallar takarda ba, wannan karon sai mun gani a kasa, sai mun shaida shi a kwanon cin mu, sai mun gan shi a ingancin ilimin da ‘ya’yanmu ke samu, sai mun shaida shi a wutar lantarkin gidajenmu, da tsaro rayuwakan al’ummominmu.

Bari in tabbatar muku da damarar da gwamnatinmu ta sha, na tabbatar da cewa albarkatun da muka ajiye da kuma kwanciyar hankali da muka gina an karkatar da su zuwa wadansu muhimman fannoni da suka shafe ku suka shafe mu. A yau, Gwamnonin jihohi da masu ikon cin gashin kai na kananan hukumomi suna iya haifar da karin ci gaba tun daga tushe.

20. Saboda haka, a sakon cika Shekaru 65 na ‘Yancin kanmu, sakona shine Fata Nagari da aiki tukuru. Gwamnatin tarayya za ta ci gaba da yin nata kokarin don gyara matsalolin tattalin arzikinmu. Sauran aikinmu kuma shine ambulo fasahar samar da kayayyaki, kirkire-kirkire, da kasuwanci, kamar yadda Ma’aikatar Cikin Gida ta yi da fasfunan tafiye-tafiye, ta hanyar saurin aiki da su. A wannan bangaren, ina kira ga kananan hukumomi da na jihohi da su yi aiki tare da mu don gina kasa. Mu mayar da Najeriya kasar masu samar da kayayyaki, ba wai masu saye kawai ba. Mu noma gonakinmu kuma mu gina masana’antu don sarrafa amfanin gonakinmu. Mu yi amfani da kayayyakin da aka kera a Nijeriya. Nijeriya ce farko. Mu biya harajinmu.

21. A karshe, ina kira da mu dage kafar wando mu kama aiki, mu sake yarda da kasarmu, da karfin da take da shi da bai san iyaka ba.

22. Da Ikon Allah Maɗaukakin Sarki nake iya tabbatar muku cewa lokacin bayyanar sabuwar Nijeriya, mai wadata, mai dogaro da kanta ya zo.

23. Ina taya mu murna da Cika Shekaru na 65 na ‘Yancin Kai, Allah Ya albarkaci Jamhuriyar Tarayyar Nijeriya.

Amin.

Tags: jawabiNijeriyashekaru 65Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Previous Post

Haɗakar ‘yan adawa ba za ta yi tasiri ba domin cike take da ‘yan siyasar da ba sa kishin al’umma, inji Abdulaziz Abdulaziz

Next Post

Shettima ya dawo gida bayan taron Majalisar Ɗinkin Duniya

Related Posts

Hausa Zalla Ko Zallar Jahilci?
Mahanga

Hausa Zalla Ko Zallar Jahilci?

March 29, 2026
Mahanga

Yadda Aka Raba Musulmi Da Ƙur’ani

February 22, 2026
Taƙaddamar Imam Ghazali Da Ibn Rushud A Kan Ruhi (Rai)
Mahanga

Taƙaddamar Imam Ghazali Da Ibn Rushud A Kan Ruhi (Rai)

February 18, 2026
Musulunci Da Masu Yi Masa Zagon Ƙasa A Nijeriya
Mahanga

Musulunci Da Masu Yi Masa Zagon Ƙasa A Nijeriya

February 15, 2026
Sarkin Adabi: Mafi Girman Sarautar Fasaha
Mahanga

Sarkin Adabi: Mafi Girman Sarautar Fasaha

February 13, 2026
Muhimman Shawarwarin Tsaro Ga Magidanta Da Iyalai
Mahanga

Muhimman Shawarwarin Tsaro Ga Magidanta Da Iyalai

January 20, 2026
Next Post
Shettima ya dawo gida bayan taron Majalisar Ɗinkin Duniya

Shettima ya dawo gida bayan taron Majalisar Ɗinkin Duniya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!