Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya dawo Nijeriya bayan kammala babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 da aka gudanar a birnin New York tare da wasu muhimman tattaunawa a ƙasar Jamus.
A yayin zaman mako guda na hulɗar ƙasashen duniya, Shettima ya gabatar da jawabin ƙasa na Shugaba Bola Ahmed Tinubu inda ya yi kira ga cikakkun sauye-sauye a Majalisar Ɗinkin Duniya.
Haka kuma, ya jagoranci kare ikon Afrika kan albarkatun ma’adananta da aka ƙiyasta darajar su a dala biliyan 700 tare da ƙarfafa hulɗa ta dabarun cigaba da Birtaniya da Gidauniyar Gates, da sauran manyan masu ruwa da tsaki a duniya.
Daga bisani, Shettima ya gana da shugaban Majalisar Ɗinkin Duniya, António Guterres, wanda ya yaba da yunƙurin Najeriya na neman kujerar dindindin a kwamitin tsaro na majalisar.

A wani zama ta daban kuma, Shettima ya gabatar da damar zuba jari a fannin sauyin makamashin Najeriya da darajar sa ta kai dala biliyan 200 ga manyan masu zuba jari na duniya.
Mataimakin Shugaban Ƙasar ya kuma tabbatar wa da al’ummar Nijeriya mazauna ƙasashen waje cewa gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da gana da su a harkokin gudanarwar ta kafin ya wuce Jamus don kammala wasu muhimman hulɗoɗi.







