• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Siyasa

Haɗakar ‘yan adawa ba za ta yi tasiri ba domin cike take da ‘yan siyasar da ba sa kishin al’umma, inji Abdulaziz Abdulaziz

Wakilin Mu by Wakilin Mu
September 30, 2025
in Siyasa
A A
0
Haɗakar ‘yan adawa ba za ta yi tasiri ba domin cike take da ‘yan siyasar da ba sa kishin al’umma, inji Abdulaziz Abdulaziz
Malam Abdulaziz Abdulaziz

Malam Abdulaziz Abdulaziz

Babban mai taimaka wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan harkokin jaridu, Malam Abdulaziz Abdulaziz, ya bayyana yunƙurin kafa jam’iyyar haɗakar adawa da wasu ’yan siyasa ke jagoranta a matsayin yunƙuri mara tasiri, yana mai cewa shugabannin haɗakar mutane ne da tasirin siyasar su ya jima da ƙarewa kuma ba su da ƙimar siyasa a idon jama’a.

Abdulaziz ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ’yan jarida a cibiyar Ƙungiyar ’Yan Jaridu ta Ƙasa (NUJ) reshen Kano a ranar Talata, inda ya bayyana waɗanda ke jagorantar ƙungiyoyin a matsayin “’yan siyasa da ba sa kishin al’umma, waɗanda ke motsi kawai don huce haushin rashin samun.”

Ya ce: “Ina tabbatar maku da cewa Shugaban Ƙasa bai da wani ɗar. Ba ya cikin damuwa game da kowace irin jam’iyya ko haɗaka domin jagororin haɗakar sun daɗe da rasa tasiri a siyasa. Sun sha tsayawa takara suna faɗuwa. A yanzu ma tauraruwar su na ƙarasa dusashewa.”

Ya ƙara da cewa: “Waɗannan mutane ba damuwar talakawa ce a gaban su ba. Damuwar su ita ce rashin samun kujerar mulki. Kuma ’yan Nijeriya sun riga sun fahimci hakan, shi ya sa wannan haɗaka ba ta yi tasiri kamar yadda suka zata ba.”

Abdulaziz ya bayyana cewa shugabancin Tinubu ya fi karkata kan ɗaukar matakan gyara masu wahala amma masu amfani, ba wai bin tsarin neman farin jini ba tare da samar da mafita ba.

“Akwai bambanci tsakanin shugabanci da siyasa. Siyasa fagen neman farin jini ne, shugabanci kuwa aikin gina ƙasa ne. Kuma wannan shi ne abin da Shugaba Tinubu ke yi. Yana ɗaukar matakai masu tsauri, ko da zai shafi kan sa, muddin ya ga cewa zai amfani ƙasar,” inji shi,

Dangane da koke-koken da ake yi na cewa gwamnatin ta fi mayar da hankali kan ayyuka a Kudu, Abdulaziz ya ce maganganu ne kawai na siyasa, yana mai jaddada cewa Shugaban Ƙasa na ci gaba da manyan ayyuka a Arewa da ya gada, ciki har da aikin bututun gas na Ajaokuta–Kaduna–Kano, babban titin Abuja–Kaduna–Kano da kuma layin dogo na Kano–Katsina–Maraɗi.

Ya ce: “Ina so ku sani, idan da wannan mutum (Shugaba Tinubu) zai nuna wariya ko ƙyama ga Arewa, da ya bar waɗannan ayyuka su mutu. Amma ya ci gaba da bada kuɗi don a aiwatar da su, kuma ana ci gaba da aiwatar da su.”

Ya ƙara da cewa gwamnatin Tinubu ta kuma fara sababbin ayyuka kamar titin Sokoto–Badagry wanda yake daga manyan ayyukan da gwamnatin Shugaba Tinubu ta ke yi don bunƙasa tattalin arzikin ƙasa baki ɗaya.

Tags: Abdulaziz AbdulazizShugaba Bola Ahmed TinubuZaɓen2027
Previous Post

An halaka ‘yar jaridar gidan talbijin na Arise, Somtochukwu Maduagwu ta gidan talbijin na Arise a wani harin fashi da makami

Next Post

Bayan wuya, sauƙi ya fara bayyana a Nijeriya – Tinubu

Related Posts

Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista
Siyasa

Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista

May 5, 2026
Kwankwaso da Obi sun koma NDC
Siyasa

Kwankwaso da Obi sun koma NDC

May 3, 2026
Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi
Siyasa

Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi

May 3, 2026
Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC
Siyasa

Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC

May 1, 2026
Rikicin shugabanci a ADC: Ɓangaren David Mark ya rubuta wa CJN takarda, ya roƙi a gaggauta yanke hukunci
Siyasa

Rikicin shugabanci a ADC: Ɓangaren David Mark ya rubuta wa CJN takarda, ya roƙi a gaggauta yanke hukunci

April 28, 2026
A taron Ibadan, ‘yan adawa sun haɗa kai, sun amince da tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya a zaɓen 2027
Siyasa

A taron Ibadan, ‘yan adawa sun haɗa kai, sun amince da tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya a zaɓen 2027

April 25, 2026
Next Post
Bayan wuya, sauƙi ya fara bayyana a Nijeriya – Tinubu

Bayan wuya, sauƙi ya fara bayyana a Nijeriya - Tinubu

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!