• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Monday, September 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Mahanga

Muhimman Shawarwarin Tsaro Ga Magidanta Da Iyalai

Abdullahi Bakoji Adamu by Abdullahi Bakoji Adamu
January 20, 2026
in Mahanga, Tsaro
A A
0
Muhimman Shawarwarin Tsaro Ga Magidanta Da Iyalai
Wani layi a Kano (tsohon hoto daga: Luc Gnago/Reuters)

Wani layi a Kano (tsohon hoto daga: Luc Gnago/Reuters)

A matsayin ka na magidanci, ka sani cewa tsaron iyalin ka amana ce a wuyan ka, kuma ba a bar ta a kan addu’a kaɗai ba, sai an haɗa addu’a and ilmi and taka-tsantsan da tsari.

1. Kulle Gida da Kula da Kofa

Ka sabar wa iyalin ka rufe gida ko da yaushe, musamman:

  • Bayan sallar Asuba
  • Da rana
  • Da dare

Kada a buɗe ƙofa sai an tabbatar:

  • Waye ne?
  • Daga ina ya fito?
  • Me ya kawo?

Kada a taɓa buɗe ƙofa kai-tsaye, ko da:

  • Ya ce ɗan NEPA ne. Ya ce mai ruwa ne
  • Ya ce mai allurar Polio ne ko wani abu daban.

Sai an tabbatar da sahihancin sa ta waya ko maƙota.

2. Tsarin Fita daga Gida (Movement Protocol)

Idan zakl ka fita:

  • Ka sanar da iyalin ka inda zaka je
  • Lokacin da kake tsammanin dawowa

Idan za ka aiko wani mutum, ka faɗa musu sunan sa da dalilin zuwan sa.

Idan ba ka aiko kowa ba, ka gaya musu kar su karɓi kowa a madadin ka.

3. Tsarin Sadarwa (Communication Security)

Ka lazimci kiran iyalin ka a kai a kai

Kada ka taɓa barin wayar iyalin ka babu kati, ko da ₦100 ne

Ka tanadi waya ta musamman a gida don gaggawa (emergency phone)

Idan iyalin ka ko maƙota suka kira ka:

  • Kada uzuri ya hana ka ɗaga wa
  • Ko kana taro, ka fita ka ɗaga
  • Idan ba ka samu ba, ka kira su nan take

4. Lambobin Gaggawa (Emergency Contacts)

Ka tabbatar iyalin ka suna da lambobin:

  • Maƙwabta nagari (maza da mata)
  • ‘Yan banga / vigilante na unguwa
  • Mai’unguwa
  • Jami’an ‘yan sanda mafi kusa

Ka rubuta lambobin:

  • A waya
  • A takarda a manne a bango
  • A haddace su

5. Tsaron Cikin gida (Internal Security)

Kada iyali su yawaita faɗar sirrin gida

ada a gaya wa mutane:

  • Lokacin da maigida baya nan
  • Ko cewa suna su kaɗai a gida

Ka hana yara:

  • Yawaita buɗe ƙofa
  • Yarda da baƙi

6. Haske a Muhalli

Ka tabbatar da:

  • Fitilu a waje da cikin gida idan da hali.
  • Gyara katanga da ƙofa

Kada a bar:

  • Duhu duhu da za a iya ɓuya
  • Ɓarayi suna tsoron haske.

7. Alamomin Haɗari (Threat Indicators)

Ka horar da iyalin ka su kula da:

  • Mutanen da ke zagayawa ba tare da dalili ba
  • Motoci da suke tsayawa suna kallo
  • Masu tambayar bayanai da yawa

Idan an lura: a kira kai ko jami’an tsaro nan take

8. Haɗa Kai da Maƙwabta (Community Security)

  • Ka gina kyakkyawar alaƙa da maƙwabta
  • Ku kafa tsaron unguwa
  • Ku raba jadawalin sa ido
  • Ku riƙa sanar da juna duk wani abu da ake zargi

Unguwa mai haɗin kai tana da wahalar kai hari.

9. Kada a Dogara da Addu’a Kaɗai

Haƙiƙa: “Addu’a makami ce, amma ilmi garkuwa ne.”

  • Ka yi addu’a
  • Ka dage da addu’a
  • Ka ƙarfafa imanin ka

Amma ka sani: Annabi (SAW) ya ce ɗaure raƙumin ka sannan ka yi tawakkali.

10. Darasi daga Abin da Ya Faru A Kano

Abin da ya faru na kisan mutane 7 kwanan nan a Kano da na baya duk da suka faru:

  • Darasi ne mai zafi
  • Gargaɗi ne ga kowa
  • Nuna cewa haɗari ba ya ba da sanarwa
  • Mu sani rigakafi ya fi magani

Ƙarshen Saƙo

  • Tsaro ba aikin gwamnati kaɗai ba ne.
  • Tsaro alhakin kowa ne, musamman magidanci.

Allah ya jiƙan su, Allah ya kare mu da iyalan mu, amin.

* Abdullahi Bakoji Adamu mai sharhi ne kan harkokin tsaro

Tags: shawarwaritsaro
Previous Post

Zargin damfarar dala miliyan 13: Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan buƙatar EFCC na ƙwace kuɗi gaba ɗaya

Next Post

Duk za a fice daga ADC idan Atiku ya zama ɗan takarar jam’iyyar, inji Hakeem Baba-Ahmed

Related Posts

Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Ministan Yaɗa Labarai ya taya Kiristoci murnar bikin Ista
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta jajanta wa al’ummar Neja kan rasuwar mutane a Wushishi, ta bayar da umarnin bincike

September 18, 2026
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja

September 18, 2026
Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa
Tsaro

Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa

September 9, 2026
Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam

September 1, 2026
Next Post
Duk za a fice daga ADC idan Atiku ya zama ɗan takarar jam’iyyar, inji Hakeem Baba-Ahmed

Duk za a fice daga ADC idan Atiku ya zama ɗan takarar jam’iyyar, inji Hakeem Baba-Ahmed

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!