• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Mahanga

Sarkin Adabi: Mafi Girman Sarautar Fasaha

KABIRU YUSUF FAGGE by KABIRU YUSUF FAGGE
February 13, 2026
in Mahanga, Nishaɗi Da Al'adu
A A
0
Sarkin Adabi: Mafi Girman Sarautar Fasaha
Daga hagu: Alhaji (Dr) Aminu Ladan Abubakar (Ala), Sarkin Adabin Harshen Hausa da Alhaji Dauda Adamu Kahutu (Rarara), Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa

Daga hagu: Alhaji (Dr) Aminu Ladan Abubakar (Ala), Sarkin Adabin Harshen Hausa da Alhaji Dauda Adamu Kahutu (Rarara), Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa

A kwanakin baya Mai Martaba Sarkin Daura ya yi wasu naɗe-naɗe na sarautu da dama, ciki har da waɗanda suka shafi fasaha, inda ya naɗa Alhaji Dauda Adamu Kahutu (Rarara) a matsayin Sarkin Mawaƙan Ƙasar Hausa, sannan kuma ya naɗa Alhaji (Dakta) Aminu Ladan Abubakar (Ala) Sarkin Adabin Harshen Hausa.

Waɗannan naɗe-naɗe na sarautu sun jawo ce-ce-ku-ce da yawa, wasu suna ganin wai:

(1) Sarkin Daura ba shi da hurumin naɗa sarauta kuma a kira ta da ta ƙasar Hausa.

(2) Wasu kuma suna ta muhawara ne a kan tsakanin “Sarkin Mawaƙa” da “Sarkin Adabi” wacce sarauta ce ta fi, wacce ce take gaba da ‘yar’uwar ta?

Bugu da ƙari, kalaman raha da Dafta Dauda Rarara ya rinƙa yi cewar duk wani mawaƙi da yake ƙasar Hausa sai ya je gare shi ya miƙa wuya, ya yi biyayya an sahale masa ko kuma duk waƙar da mutum zai saurara a manhajoji kamar TikTok ko Youtube, to sai ya nemi izini daga fadar sa, da sauran su.

Wannan ya sa har wasu mawaƙa irin su Naziru Sarkin Waƙa da Adamu Nagudu da sauran su sun mayar da martani.

To bari in warware waɗannan sa-toka-sa-katsi a taƙaice. Bari mu fara da ikon da Sarkin Daura yake da shi na yin naɗi a matsayin Sarautar Ƙasar Hausa.

ƘASAR HAUSA

Ƙasar Hausa ita ce wadda ta malale yawancin arewacin Nijeriya, a sashen gabas kuwa Ƙasar Hausa ta yi iyaka da ƙasashen Barno daga yamma ta dangane da ƙasar Dahomey, tun ma ba ta fuskar gabas da Kogin Kwara ba. Ta fuskar arewa ta cim ma gaɓar Ƙasar Adar a Jamhuriyar Nijar. A ɓangaren kudu kuwa ta yi iyaka da wasu garuruwan Gwari da na kudancin Zazzau da kudancin Bauchi (Ibrahim, M.S. 1982: sh:2).

Wannan bayani ya nuna inda Ƙasar Hausa take. To kuma ta haɗa garuruwa waɗanda waɗannan garuruwa sun taɓa zama dauloli masu zaman kan su.

DAULOLIN ƘASAR HAUSA

Akwai dauloli da aka yi a Ƙasar Hausa kamar:

1. Daular Zamfara

2. Daular Gobir (Birnin Alƙalawa/Sabon Birni)

3. Daular Kabi

4. Daular Daura

5. Daular Kano

6. Daular Katsina

7. Daular Zazzau

Su daulolin nan suna da damar yin abu, kuma su kira shi na Ƙasar Hausa. Misali, yanzu Sarkin Daura na iya naɗa Sarkin Mawaƙan Ƙasar Hausa, to haka shi ma Sarkin Kano yana iya naɗa nashi Sarkin Mawaƙan Ƙasar Hausan, haka na Katsina ko Kabi ko Zazzau.

TSAKANIN SARAUTAR SARKIN ADABIN HARSHEN HAUSA DA TA SARKIN MAWAƘAN ƘASAR HAUSA

Da farko dai sarautun suna da ƙima saboda duban daga inda suka fito. Sai dai bisa wacce sarauta ce ta fi girma a tsakanin su sai mu ce Sarautar Sarkin Adabin Harshen Hausa ta fi sarautar Sarkin Mawaƙan Ƙasar Hausa, bisa dalilai kamar haka:

Da farko ya kamata a sani an bayar da sarautun ne saboda (1) adabi (2) na biyu saboda waƙa. To shi adabi shi ne madubi ko hoton rayuwa na al’umma. Wannan ya ƙunshi yadda al’adun su da ɗabi’un su da harshen su da halayyar rayuwar su da abincin su, da tufar su da makwancin su da hulɗoɗin su da tunanin su da ra’ayoyin su da sauran abubuwa da suka shafi dabarun zaman duniya don ci gaba da rayuwa; kai har ma da abubuwan da suka shafi mutuwa (Ɗangambo, 1984:1).

Sannan adabin ya kasu kashi biyu: (1) adabin gargajiya (2) da adabin zamani.

A ƙarƙashin adabin gargajiyar nan akwai:

  • tatsuniyoyi da labarai
  • almara, wasa ƙwaƙwalwa, ƙissa da hikayoyi
  • waƙoƙi da kaɗe-kaɗe

Haka nan a ƙarƙashin adabin zamani akwai:

  • rubutattun waƙoƙi
  • rubutun zube
  • wasan kwaikwayo

A ƙarƙashin waƙoƙi akwai mawaƙa irin su Mamman Shata, Ɗan’anace, Ɗanƙwairo, Barmana Coge, Narambaɗa, Aminu Ala, Dauda Rarara, Naziru Sarkin Waƙa, Fati Nijar, Maryam Fantimoti, da sauran su.

A ƙarƙashin rubutun zube aka samu irin su Abubakar Imam, Bature Gagare, Bilkisu Funtuwa, Rahama Abdulmajid, Ibrahim Sheme, Nazir Adam, Aminu Ala, da sauran su.

A ƙarƙashin wasan kwaikwayo aka sami irin su Haji A. Kano da S. Maƙarfi da Umar Ɗanjuma Katsina da Bashari Farouk Roukbah, Ali Nuhu, Aminu Ala da sauran su.

Dukkan waɗannan suna ƙarƙashin “adabi” na gargajiya ko na zamani. Idan haka ne, to Sarautar Sarkin Adabin Harshen Hausa ta fi sarautar Sarkin Waƙa daraja, ta fi ta Sarkin Mawallafa daraja, ta fi ta Sarkin Wasan Kwaikwayo daraja, kuma tana sama da su. Don haka a nan, a sarautun da Sarkin Daura ya ba fasihai za mu iya cewa Alhaji (Dr.) Aminu Ala yana sama da Alhaji (Dr.) Dauda Adamu Kahutu Rarara.

Alhaji (Dakta) Aminu Ladan Abubakar (Ala), Sarkin Adabin Harshen Hausa, da Alhaji Dauda Adamu Kahutu (Rarara), Sarkin Mawaƙan Ƙasar Hausa

SHIN AMINU ALA YA CANCANCI ZAMA SARKIN ADABIN HARSHEN HAUSA?

A bisa wasu dalilai da na kalato daga rayuwar marubucin kuma mawaƙin kuma ɗan wasan kwaikwayon za mu iya cewa e, bisa dalilai kamar haka:

1. Waƙa – A fagen waƙa an kira Aminu Ala baharu, sannan ya karɓi sarautu na waƙa a garuruwa, don haka a nan ya cancanta.

2. Rubutun zube – A fagen rubutun zube, Aminu Ala marubuci ne fitacce, da ya rubuta littattafai da dama, ciki har da wanda hukuma ta daular Kano ta wallafa, bayan ta sahale ta yarda shi marubuci ne. To a nan ma ya cancanta.

3. Wasan kwaikwayo – A nan ma, Aminu Ala ya taɓa fitowa a fim ɗin Hausa, ya zama furodusa a wasu shekaru na can baya, ya kuma ba da gudunmawa ta rubutawa. Nan ma ya ɗosano.

4. Hikimomin baka – Ƙari a kan bayanan da suka gabata, Aminu Ala ma’abocin hikimomin baka ne a waƙoƙin sa da zantukan sa da suka zama ababen nazarta.

A ƙarshe, ma iya cewa an ajiye ƙwarya a gurbin ta, kuma ina kira ga sauran masu sarautun fasaha, musamman daga Daular Daura, su miƙa ragamar sarauta ga sarkin su, su yi gaisuwar ban-girma. Allah ya taya riƙo, amin.

* Malam Kabiru Yusuf, ɗalibi a harshen Hausa, mazaunin Kano ne

Tags: AlanWakaRararasarautasarkiSarkinDauraƘasarHausa
Previous Post

CBN ya umurci bankuna da su riƙa sayar wa ‘yan canji dala 150,000 a kowane mako

Next Post

Gwamnatin Tarayya ta ƙarfafa tsaro a Arewa-ta-Tsakiya bayan harin Kwara – Idris

Related Posts

Hausa Zalla Ko Zallar Jahilci?
Mahanga

Hausa Zalla Ko Zallar Jahilci?

March 29, 2026
Mahanga

Yadda Aka Raba Musulmi Da Ƙur’ani

February 22, 2026
Taƙaddamar Imam Ghazali Da Ibn Rushud A Kan Ruhi (Rai)
Mahanga

Taƙaddamar Imam Ghazali Da Ibn Rushud A Kan Ruhi (Rai)

February 18, 2026
Musulunci Da Masu Yi Masa Zagon Ƙasa A Nijeriya
Mahanga

Musulunci Da Masu Yi Masa Zagon Ƙasa A Nijeriya

February 15, 2026
Cewar Shugaba Tinubu: Bikin Argungu shaida ce ta dawowar zaman lafiya, na yi alƙawarin goyon baya ga noma da yawon buɗe ido
Nishaɗi Da Al'adu

Cewar Shugaba Tinubu: Bikin Argungu shaida ce ta dawowar zaman lafiya, na yi alƙawarin goyon baya ga noma da yawon buɗe ido

February 14, 2026
Bikin Argungu alama ce ta haɗin kan ƙasa da samun karɓuwa a idon duniya – Gwamnatin Tarayya
Nishaɗi Da Al'adu

Bikin Argungu alama ce ta haɗin kan ƙasa da samun karɓuwa a idon duniya – Gwamnatin Tarayya

January 21, 2026
Next Post
Gwamnatin Tarayya ta ƙarfafa tsaro a Arewa-ta-Tsakiya bayan harin Kwara – Idris

Gwamnatin Tarayya ta ƙarfafa tsaro a Arewa-ta-Tsakiya bayan harin Kwara – Idris

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!