A cikin littafin sa, Tahafut Al-falasifa (wato shirmen masana falsafa) Imam Ghazali ya yi wa masana falsafa raddi game da bayanin su na yadda yanayin Ruhi (Rai) yake. Abin da ya samo asali daga bayanin Plato, kuma fitattun masana falsafa na Musulunci, wato Ibn Sina da Al Farabi suka aminta da shi cewa, “Ruhi ba shi da farko (eternal) domin asalin sa guda ne, amma ya kasance yana karkasuwa zuwa jikuna sannan daga baya, bayan mutuwa sai Ruhi ya rabu da jiki ya koma Asalin inda ya fito.”
Ghazali ya fara da cewa wannan zance ba shi da inganci a hurumin tunani. Ya kafa hujja da misali cewa idan muka ɗauki ruhin mutane biyu, misali a ce Zaidu da Amru, to ko dai ruhin su iri guda ne, ko kuma suna da bambanci. Ya ce yaya za a ɗauka irin su guda ne bayan mun san cewa kowannen su mutum ne na daban domin Zaidu ya san shi Zaidu ne kuma ya san shi ba Amru ba ne. To, don haka kowane rai daban ya ke kenan. Idan kuma an ce rai iri guda ne, kawai ya na shiga mabambanta jikunan mutane ne, to, ta yaya zaka raba abu kashi-kashi, na abin da shi ba jiki ba ne (Immaterial) har ya zama biyu, biyar, goma, dubbai (ko miliyoyi)?
Mun san dai cewa idan misali abu mai jiki ne, kamar a ce ruwan teku, zai iya karkasuwa zuwa ƙoramu da koguna sannan ya koma teku, kun ga ai babu wata mishkila. Amma abin da ba shi da jiki (kamar rai) ta yaya za ka iya karkasa shi daga guda ya zama daban-daban? Wannan zancen shirme ne kawai, a cewar Ghazali.
Ibn Rushud kuma, a nasa martanin wannan raddi da Ghazali ya yi wa masana falsafa game da Ruhi cikin nasa littafin, Tahafut at-Tahafut (Shirmen Mai Shirme) sai ya ce, “Idan muka ɗauki misalin da Ghazali ya kawo, wato da ruhin Zaidu da na Amru, cewa rayuka ne guda biyu a ƙidayance (numerically different) to, haka ne, amma a siffa (form) abu guda suke, iri ɗaya. Shi ya sa wani rai ke iya samuwa daga wani (misali mace ta haihu, ko ƙwaya ta yi tsiro).
Saboda haka shi ruhi tamkar mu ce haske ne, wato idan ka haska fitila sai ta haska duk wani jiki da ke gaban ta, wato haske ɗaya ya haskaka abubuwa da dama, ya karkasu zuwa wuri-wuri amma dai tushen sa daga fitila yake. Zaruruwan haske ne ke faɗawa kan abin da aka haska sai duk a gan su. Amma da zarar ka cire duk abubuwa da ke gaban wannan haske (wato duk wani jiki) hasken dai zai koma kan tushen nan nasa zuwa abu guda. To, ta haka ake nufin rai guda ne yake karkasuwa zuwa jiki daban-daban. Haka nan mun san cewa ruhi ba ya ƙarewa, domin idan an mutu, barin jiki yake yi kawai ya ci gaba da rayuwa babu jiki. Wato ruhi ba ya ƙarewa kenan (eternal).
Sannan maganar ruhi ba shi da farko (eternal past) kamar yadda Plato da masana irin su Ibn Sina da Al Farabi suka karɓa, a nan Ibn Rushud ya yarda da haka kuma ya kawo mana hujjar cewa ruhi ba ya ƙarewa (eternal future) amma a raddin sa cikin Tahafut at-Tahafut, bai taɓo zancen ruhi ba shi da farko a baya ba (eternal past), wato abin da ya hasala su Ghazali ke ganin cewa kamar ya saɓa wa tauhidun Musulunci.
Ibn Rushud ya ba da dalilin cewa, “Inda mun fahimci cewa ruhi ba ya ƙarewa a yayin mutuwa, kuma yana karkasuwa daga abu guda ne, to ruhi ya zama dauwamamme (immortal) ba ya da farko, kuma ba ya ƙarewa. Amma wannan batu (na ba shi da farko) ba abin da za mu ci gaba da tattauna shi ba ne a nan.
Ibn Rushud ya kauce wa fede-biri-har-wutsiya, saboda a rubuce-rubucen sa ya sha nuna cewa akwai ilimin da ba a gaya wa gama-garin mutane, domin su ba masu zurfin Ilimi ba ne, imani suke buƙata kuma sun samu, don haka kada a kawo abin da ya shallake tunanin su yadda zai iya sawa su rasa imanin su.
A nan zan yi karambani, na feɗe birin har wutsiya sakamakon cewa a yanzu Ilimi ya bunƙasa a duniyar Musulunci kuma akwai misalai na zamani da za mu iya kawowa don ya haskaka fahimtar su Ibn Rushud wadda aka murƙushe ta a baya.
Misalin zan bayar a zamanance na hujjar cewa ruhi ɗaya ne kuma yana iya karkasuwa saɓanin fahimtar su Ghazali kamar yadda Ibn Rushud ya ba da misali da haske. Wato, idan muka ɗauki wutar lantarki daga tiransifoma ta unguwa, mun san cewa tana turo wutar lantarki (current) zuwa falwaya wadda mutane ke jan waya zuwa cikin gidajen su. Da zarar ka kunna switch ɗin ɗakin ka wuta za ta kama, haka duk wanda ya kunna ta sa a unguwarku zai ga hasken nan ya kama. Lantarkin dai guda ne (current) da ya taho daga transformer amma sai ya karkasu gida-gida, wato kun ga a kidayance zai zama daban daban, amma dai a sifarsa ta lantarki bai canza ba ko kadan, guda daya ne ke tahowa. Haka nan idan ka kashe wutar gidanka, current din nan dai zai koma cikin transformer inda ya fito. Wato abinda Ibn Rushud ke nufi kenan a misalinsa na haske, domin ya tabbatar da maganar masana falsafa da ke cewa Ruhi, guda ne amma ya na karkasuwa.
Bugu da kari shine, wato Ibn Rushud ya kaucewa tattaunawa a Tahafut at-Tahafut, na maganar Plato da su Ibn Sina da Al Farabi, na cewa Ruhi ba shi da farko (eternal past) saboda yanayin zamaninsa ne. Amma duk da haka bai tsira ba domin kamar yadda malamai su ka yi caa a kan Abduljabbar a Kano, haka shi ma Malaman zamaninsa suka saka mahukunta aka sauke shi daga Alkalin Alkalan Cordoba, aka kone littafansa aka kore shi daga garin.
To me yasa masana falsafa su ka gano haka amma Malaman addini (su Ghazali) su ka kasa ganewa?
Ruhi ba jiki ba ne wanda za’a iya gani ko a taba ballantana a iya yin nazari ko bincikensa. Shi yasa ya gagari kimiyya tun asali har gobe. Ruhi shine sirrin rayuwa ta jiki a wannan Duniya ta mu. Idan yana nan akwai Rai, idan ya kauce jiki ya mace kenan. To menene asalinsa?
Allah da kansa sai ya ce mana cikin suratul Hijri
Q15:28-29 “Kuma a lõkacin da Ubangijinka ya ce wa malã’iku: “Lalle Nĩ mai halittar wani jiki ne daga ƙẽƙasasshen yumɓu wanda ya canja.”To idan Na daidaitã shi kuma Na hũra daga RũhĩNa a cikinsa, to, ku fãɗi a gare shi, kunã mãsu yin sujada”
Ga inda ruhi ya samo asali, wato lokacin da Allah ya yi niyyar halitta a doron kasa sai ya shaidawa mala’iku cewa zai halicci jiki amma sai ya hura masa Rai daga nasa ruhin zai rayu. Kasancewar Ruhin ubangiji ba shi da farko ballantana karshe (eternal past and future) shi yasa da ya arawa mutum sai ya kasance rayukanmu sun zama sun darshi wannan dawwama (immortality) yadda Rai sai dai ya shiga ko ya fita daga jikinmu. Don haka abinda ya samo asali daga Allah kaga ba shi da farko. Abinda masana irinsu Ibn Rushud, Ibn Sina da Al Farabi su ka fahimta kenan daga wannan aya ya sa suka goyi bayan maganganun su Plato da su ka ce Rai dawwamamme ne (eternal) a baya da nan gaba saboda daga ruhin ubangiji ya samo asali.
Sannan hujjar Qurani da ta dada tabbatar da cewa Ruhi guda ne, shine bayanin cikin suratul A’araf
Q7:172 “Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya karɓi (alkawari) daga ɗiyan Ãdam, daga bãyayyakinsu, a zuriyarsu, kuma Ya shaidar da su a kan rãyukansu, (Ya ce): “Shin, bã Nĩ ne Ubangijinku ba?” Suka ce: “Na’am! Mun yi shaida!” (ya ce): “Kada ku ce a Rãnar Kiyãma: Lalle ne mũ, daga wannan, gafalallu ne.”
Bayan Allah ya halicci Rai kamar yadda a waccan ayar ta baya ya yiwa mala’iku busharar halittar Adam. A nan sai ya ce ya karbi alkawarin rayuka gaba daya sun shaida kadaitakarsa, wanda rayuka da suke dunkule gaba daya, a matsayin Adam, su ka amsa cewa hakika sun shaida Allah ne ubangijinsu. Ni da kai da ku, ba mai iya tuna wannan lokaci saboda ba a daidaikun rayukanmu muka yi wannan alkawari ba, a dunkule ne rayuka a matsayin “Adam” su ka amsa. Shi yasa sai wannan dabi’a ta damfaru cikin kowane Rai shi yasa babu wani mahaluki da baya karkata ga wani Iko sama da shi, ko da kuwa ya ayyana kansa a mulhidi. Zuciyar Dan Adam na karkata ga bautawa wani abu da ta san ya na sama da ita, hatta mulhidai.
To, ta yaya masana falsafa a baya su ka tsinkayi wannan Ilimi na Ruhi? Idan ka yi nazarin magabata irinsu Plato, Aristotle da musamman Socrates, zaka gane cewa annabawa ne a zamaninsu domin ilimin da su ke da shi babu yadda za su iya samunsa ba ta hanyar wahayi ba. Socrates ya cika duk wasu sharuda na annabta da gwagwarmayar annabci idan muka yi nazarin tarihinsa sosai.
Kuma kada mu manta Allah da kansa ya gaya mana cewa
Q10:47 “Kuma ga kowacce al’umma mun aika Manzo”
Don haka babu wata al’umma da ba ta sami sakon shiriya ba, shi ya sa babu wanda ya san iya yawan manzannin da Allah ya aiko Duniya. Wasu na cewa akwai manzannin 124,000, amma dai hasashe ne kawai domin hatta Annabi Muhammad kan sa Allah ce masa yayi
Q40:78 “Kuma lalle haƙĩƙa, Mun aika wasu Manzanni daga gabãninka, daga cikinsu akwai wanda Muka ƙissanta maka lãbãrinsa kuma daga cikinsu akwai wanda ba Mu ƙissanta lãbãrinsa ba a gare ka”
Don haka mu gane cewa shi lamarin ruhi ya na daga cikin abubuwa da Allah ya barwa kansa sani. Shi ya sa da Yahudawa suka zo domin tantance annabtar Annabi Muhammad, a cikin tambayoyi uku da suka bijiro masa da ita shine “Menene Ruhi?”
Sai Allah ya ce ya gaya musu
Q17:85 “Sunã tambayar ka ga me da rũhi. Ka ce: “Rũhi daga al’amarin Ubangijina ne, kuma ba a bã ku (kõme) ba daga ilmi fãce kaɗan.”
Daga cikin guntun ilimin da Allah ya bamu shine na sanin daga ina ya samo asali, mu na gane idan akwai shi (life) ko idan babu shi (death), sannan mun san cewa an fara halittarsa kafin a yi jiki, kuma bayan jiki ya mutu zai ci gaba da rayuwa har abada (eternal). Kuma sakamakon Rai ba ya samuwa sai ta ruhin ubangiji shi yasa babu wani mahaluki da zai iya kirkirar wata halitta daga wani abu mara Rai, abinda ya sa Allah ya kalubalance mu daga nan har zuwa tashin kiyama cewa
Q22:73 “Ya ku mutãne! An buga wani misãli, sai ku saurãra zuwa gare shi. Lalle ne waɗanda kuke kira baicin Allah, bã zã su iya halitta ƙudã ba, kõ da sun tãru (gaba daya) gare shi’
Shi yasa kuma a zahiri na halittu a doron Duniya, za ka samu cewa kowacce halitta ta na iya samuwa ne kadai daga wata halitta, babu wadda ta kasance katsam sai dai ta silar iyayenta a tsari mai kama da jerin carbi. Hujjar da ke tabbatar da cewa Rai guda daya ne ya ke ta karkasuwa zuwa jikuna daban-daban tamkar yadda current na wutar lantarki ke samar da haske a warwatse ko’ina, kamar yadda masana falsafar mu ta addinin musulunci, Ibn Sina, Al Farabi da Ibn Rushud, su ka gano sama da shekaru dubu da su ka wuce.
Amma kasancewar malamai irinsu Imam Ghazali su ne su ke juya akalar addinin sai aka murkushe falsafa gaba daya daga cikin addinin musulunci aka kafirtar da ita. Su Ghazali sun gina yin amfani da Takfir, wato kafirta duk wanda ya sabawa fahimtarsu, domin ya kafirta Ibn Sina da Al Farabi cikin Tahafut Al-falasifa. Wannan dabi’a ita ce ginshikin koma bayan musulmi a Duniya bayan kaiwa tsaiko da su ka yi a baya. Idan muna fatan dawo da martabar mu sai mun dawo da fifita Ilimi, nazari da bincike fiye da makauniyar biyayya ta wadannan Salaf, domin hakan na saka mu cikin jerin wadanda Allah ya zarga a baya da cewa “Inna wajadna aba’ana”.
Barkan mu da shigowa Ramadan…Allah ya karbi ibadun mu!!!






