• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Ƙasashen Duniya

Amurka ta saka wa Afrika ta Kudu takunkumin halartar taron G20 na baɗi

New Citizen Hausa by New Citizen Hausa
November 27, 2025
in Ƙasashen Duniya
A A
0
Amurka ta saka wa Afrika ta Kudu takunkumin halartar taron G20 na baɗi
Shugaban Amurka Donald Trump (a dama) tare da Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa a fadar White House da ke Washington, D.C., Amurka, a ranar 21 ga Mayu, 21, 2025. (Hoto: REUTERS/Kevin Lamarque)

Shugaban Amurka Donald Trump (a dama) tare da Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa a fadar White House da ke Washington, D.C., Amurka, a ranar 21 ga Mayu, 21, 2025. (Hoto: REUTERS/Kevin Lamarque)

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya hana Afrika ta Kudu halartar taron ƙolin ƙasashen G20 na shekara mai zuwa da za a yi a Florida bayan Amurkar ta ƙaurace wa taron shugabannin duniya da aka yi a birnin Johannesburg.

Afrika ta Kudu ta maida martani a daren jiya Laraba, ta jaddada cewa zaman Afrika ta Kudu a matsayin membar G20 haƙƙin ƙungiyar ne — ba na Amurka ba.

Fadar Shugaban Ƙasa ta Afrika ta Kudu ta kira matakin da Trump ya ɗauka “wulaƙanci” kuma ta yi alƙawarin ci gaba da halartar dukkan tarukan G20.

Taƙaddamar ta biyo bayan watanni da aka shafe ana rashin jituwa kan manufofin cikin gida da na waje, inda Trump ya ci gaba da dagargazar Afrika ta Kudu tun dawowar sa fadar White House a watan Janairu.

Afrika ta Kudu dai a ranar Talata ta miƙa shugabancin G20 a wani ƙaramin taro na ma’aikatar harkokin waje, bayan ta ƙi yin hakan a taron ƙolin ga wani jami’in jakadancin Amurka, tana nanata cewa dole Washington ta bi “matakin da ya dace.”

Trump ya kafa wa Afrika ta Kudu ƙahon zuƙa da kafa mata tsauraran matakai kan wasu batutuwa tun dawowar sa fadar White House a Janairu, musamman kan iƙirarin da yake yi na wai ana “kisan ƙare dangi” ga fararen fatar ƙasar — iƙirarin da aka tabbatar ba gaskiya ba ne.

Tags: Afrika ta KuduAmurkaDonald TrumpG20taron ƙoli
Previous Post

Sojoji sun yi juyin mulki a Gini-Bissau, sun kama shugaban ƙasa

Next Post

Tinubu ya yi matuƙar jimamin rasuwar babban malami, Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi – Fadar Shugaban Ƙasa

Related Posts

Netanyahu ya bayyana cewa ya yi jinyar cutar sankarar ‘ya’yan maraina a asirce
Ƙasashen Duniya

Netanyahu ya bayyana cewa ya yi jinyar cutar sankarar ‘ya’yan maraina a asirce

April 24, 2026
Isra’ila ta tabbatar da sahihancin hoton soja yana bugun gunkin Yesu da guduma
Ƙasashen Duniya

Isra’ila ta tabbatar da sahihancin hoton soja yana bugun gunkin Yesu da guduma

April 20, 2026
Ɗan bindiga a Amurka ya kashe yara 8, ciki har da 7 daga cikin ‘ya’yan sa
Ƙasashen Duniya

Ɗan bindiga a Amurka ya kashe yara 8, ciki har da 7 daga cikin ‘ya’yan sa

April 20, 2026
Za mu sake datse Mashigar Hormuz, inji Iran
Ƙasashen Duniya

Za mu sake datse Mashigar Hormuz, inji Iran

April 18, 2026
Yadda tsare-tsaren CBN ke daƙile hauhawar farashi da tsadar rayuwa
Ƙasashen Duniya

CBN na shirin kafa kwamitin sulhu don warware rikice-rikicen masu taurin bashi

April 17, 2026
Iran ta kakkaɓo jirgin yaƙin Amurka a sararin samaniyar ta
Ƙasashen Duniya

Iran ta kakkaɓo jirgin yaƙin Amurka a sararin samaniyar ta

April 3, 2026
Next Post
Tinubu ya yi matuƙar jimamin rasuwar babban malami, Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi – Fadar Shugaban Ƙasa

Tinubu ya yi matuƙar jimamin rasuwar babban malami, Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi - Fadar Shugaban Ƙasa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!