• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Tinubu ya yi matuƙar jimamin rasuwar babban malami, Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi – Fadar Shugaban Ƙasa

Wakilin Mu by Wakilin Mu
November 27, 2025
in Labarai
A A
0
Tinubu ya yi matuƙar jimamin rasuwar babban malami, Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi – Fadar Shugaban Ƙasa
Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi a lokacin kamfen ɗin zaɓen 2023

Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi a lokacin kamfen ɗin zaɓen 2023

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana matuƙar alhini kan rasuwar babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, wanda ya rasu a yau Alhamis yana da shekaru 101.

A cikin wata sanarwa da fadar Shugaban Ƙasa ta fitar, Tinubu ya ce rasuwar Sheikh Ɗahiru babban rashi ne ba kawai ga iyalai da mabiyan sa ba, har ma ga ƙasar nan gaba ɗaya, yana mai jaddada cewa marigayin ya sadaukar da rayuwar sa wajen shiryar da al’umma zuwa ga tafarkin gaskiya.

Shugaban ya bayyana Sheikh Ɗahiru Bauchi a matsayin jagoran Ɗariƙar Tijjaniyya da ya yi fice wajen wa’azi, karantarwa da kuma yaɗa zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Ya ce: “Sheikh Ɗahiru Bauchi malami ne, uba, kuma muryar da ke kira da hikima da natsuwa. A matsayin fitaccen mai tafsirin Alƙur’ani, ya kasance ginshiƙi wajen ƙarfafa zaman lafiya da tsoron Allah. Mutuwar sa ta bar giɓi mai faɗi a wannan fage.”

Shugaban ya kuma tuna da addu’o’i da goyon bayan da Sheikh Ɗahiru ya ba shi a lokacin yaƙin neman zaɓen 2023.

Shugaban ya miƙa ta’aziyyar sa ga iyalan marigayin, mabiyan sa da dukkan al’ummar Musulmi a cikin ƙasar nan da waje.

Ya roƙe su da su ci gaba da ɗaukaka sunan marigayin ta hanyar bin koyarwar sa ta zaman lafiya, kyautata zamantakewa da ƙarfafa kusanci da Allah.

Tags: rasuwaSheikh Ɗahiru Usman BauchiShugaba Bola Ahmed Tinubuta'aziyya
Previous Post

Amurka ta saka wa Afrika ta Kudu takunkumin halartar taron G20 na baɗi

Next Post

Tinubu yana gina ginshiƙi mai ƙarfi na makomar Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

Related Posts

Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista
Siyasa

Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista

May 5, 2026
Ranar ’Yancin ’Yan Jarida ta Duniya: Nijeriya na neman a haɗa gwiwa a yaƙi masu yaɗa labaran ƙarya
Labarai

Ranar ’Yancin ’Yan Jarida ta Duniya: Nijeriya na neman a haɗa gwiwa a yaƙi masu yaɗa labaran ƙarya

May 4, 2026
Kwankwaso da Obi sun koma NDC
Siyasa

Kwankwaso da Obi sun koma NDC

May 3, 2026
Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi
Siyasa

Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi

May 3, 2026
Shettima ya ƙaddamar da jigilar maniyyatan Hajjin bana da kwashe alhazai 500 a Abuja
Labarai

Shettima ya ƙaddamar da jigilar maniyyatan Hajjin bana da kwashe alhazai 500 a Abuja

May 3, 2026
Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC
Siyasa

Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC

May 1, 2026
Next Post
Tinubu yana gina ginshiƙi mai ƙarfi na makomar Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

Tinubu yana gina ginshiƙi mai ƙarfi na makomar Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!