A wata sabuwar ƙididdiga da mujallar Forbes ta yi baya-bayan nan, ta fito da jerin ‘yan wasan ƙwallon ƙafa guda 10, waɗanda suka fi sauran ‘yan wasan ƙwallo na duniya karɓar albashi mai tsoka a cikin 2025.
Ƙididdigar dai ta lissafa Cristiano Ronaldo cewa ya fi kowa yawan albashi a 2025, domin yawan na sa kuɗin sun kai dalar Amurka miliyan 280, kwatankwacin Naira biliyan 407 kenan idan aka maida kuɗin zuwa Naira.
Na biyu shi ne Lionel Messi wanda albashin sa shi ma na shekarar 2025 ya kai dalar Amurka miliyan 130. Wato bai ƙarasa ko rabin na Ronaldo ba kenan.
Ɗan wasa Sadio Mane ɗan Afrika shi ne na 8 inda ya ke karɓar dalar Amurka 54 a duk shekara. Wato albashin sa na 2025 kenan. Adadin kuwa ya yi daidai da naira biliyan 78 da ƙarin Naira miliyan 374.
Shin a jerin ‘yan kasuwar Nijeriya, in banda irin su Aliko Ɗangote da Abdulsamad Rabi’u, mutum nawa zai iya cin riba daidai da albashin Sadio Mane na shekara ɗaya, har naira biliyan 78?
Ga jadawalin ‘yan wasan su goma domin daina tantama ko jayayya.
1. Cristiano Ronaldo: $280 miliyan (€239 miliyan)
2. Lionel Messi: $130 miliyan (£111 miliyan)
3. Karim Benzema: $104 miliyan (€89 miliyan)
4. Kylian Mbappé: $95 miliyan (€81 miliyan)
5. Erling Haaland: $80 miliyan (€68 miliyan)
6. Vinicius Jr: $60 miliyan (€51 miliyan)
7. Mohamed Salah: $55 miliyan (€47 miliyan)
8. Sadio Mané: $54 miliyan (€46 miliyan)
9. Jude Bellingham: $44 miliyan (€38 miliyan)
10. Lamine Yamal: $43 miliyan (€37 miliyan).







