• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Monday, September 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Wasanni

Amurka ta hana alƙalin wasa ɗan Somaliya Omar Aytan shiga ƙasar ta don halartar Gasar Kofin Duniya

* Ba damuwa, zan fuskanci sauran al'amurran da ke gaba na, inji shi

ALI KANO by ALI KANO
June 9, 2026
in Wasanni
A A
0
Amurka ta hana alƙalin wasa ɗan Somaliya Omar Aytan shiga ƙasar ta don halartar Gasar Kofin Duniya
Omar Abdulkadir Artan

Omar Abdulkadir Artan

Gwamnatin Amurka ta hana fitaccen alƙalin wasa ɗin nan (rafari) ɗan ƙasar Somaliya, Omar Abdulkadir Artan, damar halartar Gasar Kofin Duniya bayan da ta hana shi shiga ƙasar ta.

Ba tare da ambaton sunan sa ba, Hukumar Kwastam da Kula da Iyakokin Amurka (CBP) ta tabbatar a ranar Litinin cewa an hana wani ɗan ƙasar Somaliya da aka shirya zai yi alƙalanci a gasar shiga ƙasar saboda wata damuwa da ta taso yayin tantance bayanan sa.

Daga baya a ranar Litinin, Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) ta tabbatar da cewa Artan ba zai samu damar halartar horo ko gudanar da wasanni a Gasar Kofin Duniya ɗin ba.

A cikin wata sanarwa, FIFA ta ce ba ta da hannu a harkokin shige da fice, kuma hukumomin da abin ya shafa sun sanar da ita cewa matsayin Artan “ba zai canza a halin yanzu ba.”

FIFA ta ƙara da cewa, “Kamar yadda aka saba a sauran manyan gasa na FIFA, gwamnatin ƙasar mai masaukin baƙi ce ke da ikon yanke hukunci kan wanda za a ba biza da kuma wanda za a bari ya shiga ƙasar ta.”

An ruwaito cewa Artan, wanda aka zaɓa a matsayin mafi kyawun alƙalin wasa a Afrika a bara, yana da ingantacciyar bizar shiga Amurka duk da cewa Somaliya tana cikin jerin ƙasashen da ke ƙarƙashin dokar taƙaita shiga Amurka.

Jami’an Somaliya sun soki matakin, suna cewa hakan “na raunana ƙudirin ƙwallon ƙafa na tabbatar da adalci, cancanta da ruhin wasa cikin gaskiya.”

FIFA ta sake tabbatar da labarin tare da jaddada cewa ba ta da hannu a tsarin shige da fice.

Haka kuma, an hana wasu ma’aikatan tallafin tawagar ƙasar Iran shiga Amurka, yayin da ɗan wasan gaba na Iraƙi, Ayman Hussein, ya shafe sa’o’i da dama a filin jirgin saman Chikago kafin daga bisani a ba shi izinin shiga ƙasar.

A cikin wata sanarwa, Artan ya gode wa “iyalan ƙwallon ƙafa” saboda saƙonnin goyon baya da suka aika masa, kuma ya yi wa abokan aikin sa fatan samun nasara a Gasar Kofin Duniya.

“Duk da abin da ya faru, ina cikin kyakkyawan yanayi kuma ina mai da hankali kan ƙalubalen da ke gaba a harkar alƙalanci ta,” inji Artan. “Ina gode wa FIFA da Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afrika saboda dukkan goyon bayan da suka ba ni, kuma na yi alƙawarin ci gaba da inganta matakin alƙalanci na yayin da nake mayar da hankali kan makoma.”

Gasar Kofin Duniya ta bana dai za ta gudana ne a ƙasashen Amurka, Meziko da Kanada. Za a fara gasar ne a ranar Alhamis a Birnin Meziko.

Tags: alƙalin wasaAmurkabizaFIFAGasar Kofin DuniyaHukumar Ƙwallon Ƙafa ta AfOmar ArtanrafariSomaliyaWorld Cup
Previous Post

CBN ya umurci bankuna su riƙa bibiyar dalilin yadda kwastomomi ke tura kuɗaɗe daga asusun kuɗaɗen wajen su, ko su fuskanci tarar naira miliyan 100

Next Post

Ranar Dimokiraɗiyya ta 2026: Tinubu yana gina ƙwaƙƙwarar Nijeriya, ta kowa da kowa – Minista

Related Posts

Burkina Faso ta ragargaji Flying Eagles da ci 4-1, ta katse mafarkin Nijeriya na zuwa gasar Kofin Duniya na U-20
Wasanni

Burkina Faso ta ragargaji Flying Eagles da ci 4-1, ta katse mafarkin Nijeriya na zuwa gasar Kofin Duniya na U-20

August 9, 2026
Lauya ta rasu saboda ɗokin nasarar Ghana a kan Panama a gasar Kofin Duniya
Wasanni

Lauya ta rasu saboda ɗokin nasarar Ghana a kan Panama a gasar Kofin Duniya

June 19, 2026
Ku jaruman gaske ne na ƙasar mu, Uwargidan Shugaban Ƙasa ta faɗa wa ‘yan wasa a taron kammala Gasar Naƙasassu ta Ƙasa karo na 3
Wasanni

Ku jaruman gaske ne na ƙasar mu, Uwargidan Shugaban Ƙasa ta faɗa wa ‘yan wasa a taron kammala Gasar Naƙasassu ta Ƙasa karo na 3

April 3, 2026
CAF ta ƙwace kofin zakarun AFCON na 2025 daga Senegal, ta bai wa Morokko
Wasanni

CAF ta ƙwace kofin zakarun AFCON na 2025 daga Senegal, ta bai wa Morokko

March 17, 2026
Gwamnatin Tarayya ta taya Super Eagles murna bisa samun lambar tagulla a gasar AFCON
Wasanni

Gwamnatin Tarayya ta taya Super Eagles murna bisa samun lambar tagulla a gasar AFCON

January 17, 2026
AFCON: Gwamnatin Tarayya ta zaburar da Super Eagles gabanin wasan kusa da na ƙarshe da Marokko
Wasanni

AFCON: Gwamnatin Tarayya ta zaburar da Super Eagles gabanin wasan kusa da na ƙarshe da Marokko

January 14, 2026
Next Post
Ranar Dimokiraɗiyya ta 2026: Tinubu yana gina ƙwaƙƙwarar Nijeriya, ta kowa da kowa – Minista

Ranar Dimokiraɗiyya ta 2026: Tinubu yana gina ƙwaƙƙwarar Nijeriya, ta kowa da kowa - Minista

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!