Kwamandan rundunar JTF ta “Operation Fansan Yamma” na yankin Arewa maso Yamma, Manjo Janar Warrah Idris, ya umurci dakaru da su ci gaba da matsa lamba kan miyagun da suka yi garkuwa da ɗaliban Makarantar Katolika ta Saint Mary’s (St. Mary’s Catholic School) da ke Papiri, Ƙaramar Hukumar Agwara, Jihar Neja, ba tare da sassauci ba.
Jami’in Yaɗa Labarai na “Operation Fansan Yamma”, Kyaftin David Adewusi, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa inda ya ce Idris ya yi wannan jawabi ne lokacin da ya ziyarci makarantar a jiya Asabar.
A yayin ziyarar, Kwamandan ya gudanar da binciken gaggawa a wurin da abin ya faru domin samun sahihin bayanin aiki kai-tsaye.
An tarbe shi tare da yi masa cikakken bayani daga Babban Hafsan Runduna ta 2 da kuma Kwamandan “Sector 3 OPFY’, Manjo Janar C.R. Nnebiefe, kan ƙoƙarin haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin ganin an kuɓutar da dukkan ɗaliban da aka sace.

Yayin da yake jaddada ƙudirin rundunar, Idris ya jaddada buƙatar ci gaba da bin diddigin miyagun, yana mai cewa, “’Yan bindigar suna jin zafin ayyukan mu kuma ba za su sami mafaka a ko’ina ba. Ku kasance masu sa ido kuma ku ci gaba da bin su ba tare da ba su hutu ba, har sai an kuɓutar da kowane ɗalibi gaba ɗaya kuma an mayar da su zuwa ga iyalan su.”
Yayin da yake bayyana ƙwarin gwiwar sa a kan dakarun, ya tabbatar da cewa za a samar da dukkan kayan aiki da tallafi da duk wata buƙata ta aiki domin tabbatar da nasarar wannan aiki.







