• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Thursday, May 14, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Ajandar Cigaba Ta Tinubu Ta Ƙunshi Ƙasa Baki Ɗaya – Minista

ALI KANO by ALI KANO
September 4, 2025
in Labarai
A A
0
Ajandar Cigaba Ta Tinubu Ta Ƙunshi Ƙasa Baki Ɗaya – Minista
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai Mohammed Idris, lokacin da ya karɓi baƙuncin Kwamishinonin Yaɗa Labarai daga jihohi 36 na Tarayyar Nijeriya, ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Yaɗa Labarai da Tsaron Cikin Gida na Jihar Borno, Farfesa Usman Tafa, a ziyarar ban-girma da suka kai a ofishin sa da ke Abuja.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai Mohammed Idris, lokacin da ya karɓi baƙuncin Kwamishinonin Yaɗa Labarai daga jihohi 36 na Tarayyar Nijeriya, ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Yaɗa Labarai da Tsaron Cikin Gida na Jihar Borno, Farfesa Usman Tafa, a ziyarar ban-girma da suka kai a ofishin sa da ke Abuja.

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ajandar cigaban da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa ta ƙunshi dukkan sassan ƙasar ba tare da nuna ɓangaranci ba, inda ake gudanar da manyan ayyuka da shirye-shirye a faɗin ƙasa.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana haka ne a Abuja ranar Laraba, lokacin da ya karɓi baƙuncin Kwamishinonin Yaɗa Labarai na jihohi 36.

Ya ce: “Ban taɓa ganin inda ake da ayyukan yi amma Shugaban Ƙasa ya ƙi aiwatarwa saboda gwamnan wannan jiha ba ya cikin APC ba. A duk abin da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi, hankalin sa yana kan ɗan Nijeriya ne.”

Dangane da cire tallafin man fetur kuwa, ya ce hakan ya bai wa jihohi damar samun kuɗaɗe fiye da da domin aiwatar da ayyuka masu muhimmanci.

Ya ce: “Cire tallafin man fetur ya buɗe hanya da ta bai wa dukkan shugabannin ku damar aiwatar da ayyuka da kawo wa jama’a amfanin dimokiraɗiyya. Ban ji wani gwamna ba, ko daga jam’iyyarmu ko wata jam’iyya, da ya ce mu dawo da tsohon tsarin.”

Idris ya tunatar da cewa kafin Tinubu ya hau mulki, jihohi 27 na fama da biyan albashi, sannan kashi 97 na kuɗaɗen shiga na ƙasa na tafiya wajen biyan bashi. Amma yanzu, a cewar sa, an samu sauyi saboda gyare-gyaren da Shugaban Ƙasa ya aiwatar.

Ya ce: “Nijeriya na kan tafiya zuwa ga ci gaba na dindindin da zai amfani kowa. Saƙo na, da kuma saƙon da muke da shi a gare ku duka shi ne ku zo ku shiga wannan jirgi domin kai Nijeriya ga inda Shugaban Ƙasa ya yi alƙawarin kai ta, kuma wanda kuke so ku gani a ƙarshe.”

Haka kuma, Ministan ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya za ta kai ziyara wasu jihohin Kudu maso Kudu da Arewa maso Gabas domin duba manyan ayyuka tare da tattaunawa da jama’a a matsayin wani ɓangare na tsarin samun ra’ayin jama’a.

A nasa jawabin, Shugaban Ƙungiyar Kwamishinonin Yaɗa Labarai, wanda kuma shi ne Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Borno, Farfesa Usman Tar, ya ce za su yi aiki tare ba tare da la’akari da jam’iyyun siyasa ba, domin ƙarfafa haɗin kan ƙasa da inganta ƙimomin al’umma.

Ya ce: “A gaban ka akwai kwamishinoni daga jam’iyyun siyasa daban-daban, daga yankuna daban-daban na ƙasar nan. Saboda haka muna wakiltar sassa daban-daban na tarayyar Nijeriya. Ba mu zo a madadin wata jam’iyya ko wani muradi na kashin kai ba. Mun zo ne bisa wani dandali na ƙasa domin tattauna hanyoyi da dabarun inganta muradin mu na ƙasa, ɗabi’unmu da kuma wayar da kan mu”

Ya ƙara da cewa ƙungiyar tasu za ta ci gaba da goyon bayan ma’aikatar wajen yaɗa muhimman kamfen na ƙasa, ciki har da wayar da kai da tarukan tattaunawa da jama’a.

Previous Post

Lashe amai: Tinubu ya dawo da shugaban NTA da ya tsige, Dembos; ya soke sabbin naɗe-naɗen kwanan nan

Next Post

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Jajen Rasuwar Mutane A Nutsewar Jirgin Ruwa A Borgu, Ta Umurci NEMA Ta Kai Agaji 

Related Posts

EFCC ta kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Nijeriya, Mustapha Abdullahi, kan zargin zambar naira biliyan 500
Labarai

EFCC ta kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Nijeriya, Mustapha Abdullahi, kan zargin zambar naira biliyan 500

May 13, 2026
Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista
Tsaro

Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista

May 13, 2026
Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75
Labarai

Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75

May 13, 2026
Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu
Ilimi

Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu

May 11, 2026
An kama Bello Boɗejo, shugaban Fulani Kuma ɗan takarar kujerar Sanata na APC a Taraba
Siyasa

An miƙa ɗan takarar Sanata kuma shugaban Fulani, Bello Boɗejo ga EFCC

May 10, 2026
Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka
Tsaro

Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka

May 9, 2026
Next Post
Gwamnatin Tarayya Ta Yi Ta’aziyyar Mutanen Da Suka Rasu A Ambaliyar Garin Mokwa

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Jajen Rasuwar Mutane A Nutsewar Jirgin Ruwa A Borgu, Ta Umurci NEMA Ta Kai Agaji 

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!