Shugaban Hukumar Lamunin Ɗalibai ta Ƙasa (NELFUND), Mista Akintunde Sawyerr, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta riga ta raba fiye da naira biliyan 80 ga cibiyoyin ilimi daban-daban a Nijeriya domin tallafa wa ɗalibai da lamunin biyan kuɗin makaranta.
Ya ce kimanin ɗalibai 745,000 ne suka nemi lamunin, inda a yanzu fiye da 400,000 suka amfana da lamunin.
Wasu daga cikin ɗaliban suna samun biyan kuɗin makaranta kai-tsaye zuwa jami’o’in su, sannan masu neman tallafin kashe kuɗi suna karɓar N20,000 a kowane wata cikin zangon karatu.
Sawyer ya bayyana cewa duk lamunin da ake bayarwa ba su da kuɗin ruwa a kan su.
Ya ce akwai nau’i biyu na lamuni, na biyan kuɗin makaranta wanda ake turawa kai-tsaye ga makaranta, da kuma na tallafin kuɗin kashewa ga ɗalibi.
A cewar Sawyer, shirin NELFUND na taimaka wa ɗalibai, yana rage yawan masu daina zuwa makaranta a matakin gaba da sakandare saboda ƙarancin kuɗi.
Ya ce hukumar tana ci gaba da karɓar sababbin masu rajista, inda cikin sa’o’i 24 da suka wuce kaɗai aka samu sama da 2,700 daga sababbin ɗalibai sun nema.




