• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Gwamnatin Tarayya Za Ta Gina Hanyar Kano Zuwa Katsina Da Kuma Gadar Legas A Kan Naira Biliyan 493

IRO MAMMAN by IRO MAMMAN
August 14, 2025
in Labarai
A A
0

 

GWAMNATIN Tarayya ta kasafta jimillar naira biliyan 493 domin wasu manyan ayyuka biyu: kammala hanyar Kano zuwa Katsina mai tsawon kilomita 152 da kuma gina sabuwar Gadar Carter a Jihar Legas.

Ministan Ayyuka, David Umahi, shi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja jim kaɗan bayan taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta a ranar Laraba, 13 ga Agusta, 2025.

Ministan ya ce an yi babban ƙari a kuɗin aikin hanyar Kano zuwa Katsina saboda yanayin tattalin arziki da ake ciki.

Umahi ya ce a da, gwamnatin da ta gabata ta raba aikin hanyar ne gida biyu.

Ya ce: “Sashe na Ɗaya, mai tsawon kilomita 74.1, da farko an ba da kwangilar sa ne a cikin 2013 a kan kuɗi naira biliyan 14, aka ƙara shi zuwa naira biliyan 24. To yanzu kuma an ƙara shi zuwa naira biliyan 68.

“Sashe na Biyu, mai tsawon kilomita 79.5 da aka bayar a cikin 2019 a kan kuɗi naira biliyan 29, aka ƙara shi zuwa naira biliyan 46, yanzu kuma ya koma naira biliyan 66.115.”

Jimillar kuɗin ayyukan a yanzu shi ne kimanin naira biliyan 134, sannan aka kasafta naira biliyan 6 a Kasafin Kuɗin shekarar 2024 da naira biliyan 34 a Kasafin Kuɗin 2025 don Sashe na Ɗaya. Shi kuma Sashe na Biyu an ware masa naira biliyan 80 a tsawon waɗannan shekaru biyu.

A game da Gadar Carter kuwa, Umahi ya ce daga binciken ƙarƙashin ruwa da aka gudanar a shekarun 2013 da 2019, an gano cewa masu haƙar ma’adinai ba bisa doka ba da kuma zaizayar ƙasa sun yi wa jikin gadar da turakun ta lahani sosai.

Kamfanin Julius Berger, wanda shi ne ke da alhakin yi wa gadar gyara a ƙarƙashin ruwa da tuwasun ta, ya ba da shawarar cewa gadar ta wuce a ceto ta, abin da ya kamata kawai shi ne a sake gina ta baki ɗaya.

Ita dai Gadar Carter, an gina ta ne a cikin 1901, kuma tana daga cikin manyan gadoji uku da suka haɗa Tsibirin Legas (wato Island) da babban garin Legas. Sauran su ne Gadar Third Mainland da Gadar Eko.

An raɗa mata sunan Sir Gilbert Thomas Carter ne, wani gwamnan Legas na zamanin mulkin mallaka.

An sha yi mata gyare-gyare bayan samun mulkin kai, domin a shekarun 1970s ma sai da aka kwance ta gaba ɗaya sannan aka sake haɗa ta.

Tags: Carter BridgeDavidUmahiFECgadahanyaKanoKatsinaLegas
Previous Post

Cewar NELFUND: Mun raba sama da naira biliyan 80 ga ɗalibai 400,000

Next Post

Cire Tallafin Mai Ya Taimaka Mana Wajen Aiwatar da Ayyuka, Inji Gwamna

Related Posts

Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya
Labarai

Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya

September 29, 2026
Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
Next Post

Cire Tallafin Mai Ya Taimaka Mana Wajen Aiwatar da Ayyuka, Inji Gwamna

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!