Iran ta naɗa Mojtaba Khamenei a matsayin sabon Jagoran Ƙoli na ƙasar, sama da mako guda bayan kashe mahaifin sa, Ayatollah Ali Khamenei, a hare-haren Amurka da Isra’ila waɗanda suka jefa yankin gaba ɗaya cikin wani babban yaƙi.
An bayyana sunan Khamenei a ranar Lahadi a matsayin wanda zai gaji mahaifin sa, bayan malaman addini sun amince da shi domin jagorantar Jamhuriyar Musulunci a cikin mafi girman rikicin da ƙasar ta fuskanta cikin shekaru 47 da suka gabata.
Mojtaba Khamenei bai taɓa tsayawa takara ko shiga zaɓen jama’a ba, amma tsawon shekaru da dama yana daga cikin manyan masu tasiri a cikin da’irar masu kusanci da jagoran ƙoli, inda ya kulla alaƙa mai ƙarfi da rundunar Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC).
A cikin ‘yan shekarun nan, ana yawan ambaton sa a matsayin ɗaya daga cikin manyan waɗanda za su iya maye gurbin mahaifin sa.
Zaɓen nasa na iya nuna cewa ɓangarorin masu tsattsauran ra’ayi a cikin tsarin mulkin Iran har yanzu suna da ƙarfi, kuma hakan na iya nuna cewa gwamnati ba ta da niyyar shiga yarjejeniya ko tattaunawa nan kusa yayin da yaƙin ya shiga mako na biyu.
Majalisar Amintattu (Assembly of Experts) mai membobi 88, wadda ke da ikon zaɓen Jagoran Ƙoli na ƙasar, ta bayyana a baya cewa ta cimma matsayar rinjaye kan wanda za a zaɓa, ba tare da bayyana sunan sa ba.
Wani memba ya ce: “An zaɓi tafarkin Imam Khomeini da kuma tafarkin shahidi Imam Khamenei. Sunan Khamenei zai ci gaba.”
Ali Khamenei, wanda ya mulki Iran tsawon shekaru 37 bayan ya gaji Ayatollah Ruhollah Khomeini wanda ya jagoranci juyin juya halin 1979, an kashe shi ne a wani hari na Amurka da Isra’ila a Tehran a ranar 28 ga Fabrairu, a farkon yaƙin da yanzu ya haddasa rikici a faɗin Gabas ta Tsakiya.
Isra’ila tun kafin a ba da sanarwar sabon jagoran, ta yi barazanar kai hari kan duk wanda aka zaɓa.
A wata hira da ya yi da jaridar Times of Israel bayan an bayyana sunan sabon Jagoran Ƙolin, Shugaban Amurka Donald Trump ya ƙi bayar da cikakken bayani, inda ya ce kawai, “Za mu ga abin da zai faru,” kamar yadda jaridar ta ruwaito.
A hirar, Trump ya ƙara da cewa kawo ƙarshen yaƙin zai kasance hukunci na “ɓangarori biyu” tare da Firayim Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu.
A ranar Lahadi, Amurka ta umurci ma’aikatan ofishin jakadancin ta su fice daga Saudiyya, wanda shi ne sabon matakin rage yawan jami’an diflomasiyyar Amurka a yankin bayan Iran ta kai hare-hare kan cibiyoyin Amurka a yankin.
Sojojin Amurka sun kuma bayyana cewa wani soja Ba’amurke na bakwai ya rasu sakamakon raunukan da ya samu a harin mayar da martani na farko da Iran ta kai mako guda da ya gabata.
Wannan na zuwa ne kwana guda bayan Trump ya jagoranci karɓar gawarwakin Amurkawa shida da aka kashe da aka mayar da su Amurka.
A cewar jakaden Iran a Majalisar Ɗinkin Duniya, hare-haren Amurka da Isra’ila sun kashe aƙalla fararen hula 1,332 a Iran tare da jikkata dubban mutane.
Naɗin Mojtaba Khamenei ya girgiza Trump, wanda a baya ya ce ba za a naɗa sabon Jagoran Ƙoli ba sai da amincewar sa.
Mojtaba Khamenei, mai shekaru 56, zai wakilci wani nau’in gadon mulki na iyali—ra’ayin da mahaifin sa ya taɓa ƙin amincewa da shi a shekarar 2024.
Iran dai ta kawo ƙarshen sarautar daular sarakuna da ta shafe ƙarnuka tana mulki ƙarƙashin Shah bayan juyin juya halin 1979.
An haifi Mojtaba Khamenei a ranar 8 ga Satumba, 1969 a birnin Mashhad, birni mai tsarki a gabashin Iran. Shi ne ɗaya daga cikin ‘ya’ya shida na marigayi Jagoran Ƙoli.
Saboda yadda yake nisantar bayyana kan sa a tarukan gwamnati da kuma a kafafen yaɗa labarai, ainihin tasirin sa ya daɗe yana zama abin hasashe a tsakanin al’ummar Iran da kuma a tsakanin jami’an diflomasiyya.
Shi ne kaɗai daga cikin ‘ya’yan tsohon Jagoran Ƙoli da ake ganin yana da wani matsayi a fili, duk da cewa ba shi da wani muƙami na hukuma.
Ana ganin yana kusa da ɓangaren masu ra’ayin mazan jiya, musamman saboda alaƙar sa da rundunar IRG, wadda ita ce rundunar aƙidar ƙasar.
Wannan alaƙa ta samo asali tun lokacin da ya yi hidima a wata rundunar yaƙi a ƙarshen yaƙin Iran da Iraƙi (1980–1988).
Ma’aikatar Kuɗi ta Amurka ta sanya takunkumi kan Mojtaba Khamenei a shekarar 2019 a lokacin mulkin Shugaban Amurka Donald Trump, tana cewa yana wakiltar Jagoran Ƙoli duk da cewa bai taɓa samun zaɓe ko naɗin muƙamin gwamnati ba sai aikin da yake yi a ofishin mahaifin sa.
Ma’aikatar ta ce Ali Khamenei ya ba ɗan sa wani ɓangare na alhakin jagoranci, inda yake aiki kusa da jami’an tsaron Iran domin ciyar da manufofin yankin da ake ganin suna haddasa rashin kwanciyar hankali da kuma manufofin cikin gida masu tsauri.
Masu adawa sun zarge shi da taka rawa a murƙushe zanga-zangar da ta biyo bayan sake zaɓen shugaban ƙasa mai tsattsauran ra’ayi Mahmoud Ahmadinejad a shekarar 2009, wanda ya haddasa gagarumar zanga-zanga a ƙasar.
A cewar wani bincike da kamfanin labarai na Bloomberg ya gudanar, wanda ya ambato majiyoyi marasa suna da rahotannin hukumomin leƙen asirin ƙasashen yamma, Mojtaba Khamenei ya tara dukiya da ake ƙiyasta ta haura dala miliyan 100.
Rahoton ya ce an zuba kuɗaɗen da aka samu daga sayar da man fetur cikin saka hannun jari a gidaje masu tsada a Birtaniya, otal-otal a Turai, da kadarori a Dubai ta hanyar kamfanonin ɓoye a wuraren guje wa haraji.
A ɓangaren addini kuma, ya yi karatun tauhidi a birnin Ƙom, kudu da Tehran, inda ya kuma koyar.
Ya kai matsayin Hujjat al-Islam, wani matsayi na malaman addini na matsakaici, wanda yake ƙasa da matsayin Ayatollah da mahaifin sa da kuma wanda ya kafa juyin juya hali Ruhollah Khomeini suke da shi.
Matar sa, Zahra Haddad-Adel, ‘yar tsohon kakakin majalisar dokokin Iran, ita ma Amurka da Isra’ila sun kashe ta a hare-haren da suka kai har suka kashe Jagoran Ƙoli, kamar yadda hukumomin Iran suka bayyana.






