• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Gwamnatin Tarayya ta ce haɗaɗɗiyar hanyar yaɗa labarai za ta ƙarfafa daidaiton tsaron ƙasa, ta yaba da gyaran iyakoki ta amfani da fasaha

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
March 10, 2026
in Labarai
A A
0
Gwamnatin Tarayya ta ce haɗaɗɗiyar hanyar yaɗa labarai za ta ƙarfafa daidaiton tsaron ƙasa, ta yaba da gyaran iyakoki ta amfani da fasaha
Hagu zuwa dama: Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris; Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo; da Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Tarayya, Dakta Magdalene Ajani, a lokacin ziyarar aiki da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ya kai wa Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida a ranar Talata, 10 ga Maris, 2026, a Abuja. (Hoto: Khalid Ahmed/FMINO)

Hagu zuwa dama: Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris; Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo; da Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Tarayya, Dakta Magdalene Ajani, a lokacin ziyarar aiki da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ya kai wa Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida a ranar Talata, 10 ga Maris, 2026, a Abuja. (Hoto: Khalid Ahmed/FMINO)

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce kafa tsarin yaɗa labarai na haɗin gwiwa tsakanin ma’aikatu da kuma dabaru zai taimaka ƙwarai wajen ƙarfafa daidaiton ayyukan tsaro a ƙasar nan.

Ya bayyana haka ne a ranar Talata lokacin da ya kai ziyarar aiki ga Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo.

Idris ya ce: “Gwamnatin Tarayya ta yi imanin cewa ta hanyar mu’amala tsakanin ma’aikatu da sassa daban-daban na gwamnati, za a iya samar da tsarin sadarwa na haɗin gwiwa wanda zai ƙarfafa daidaita matakan tsaro a yaƙin da ake yi da ’yan ta’adda da ’yan fashi da makami.”

Ministan ya bayyana cewa ma’aikatar sa tana ci gaba da hulɗa da muhimman ma’aikatu da hukumomi domin fahimtar ayyukan su sosai tare da tabbatar da cewa ’yan Nijeriya suna samun cikakken bayani kan shirye-shiryen gwamnati da tasirin su ga cigaban ƙasa.

Ya ce: “Mun ga yana da matuƙar muhimmanci kada mu zauna kawai a ofisoshin mu muna jiran ku ku zo taron manema labarai.

“Muna ganin ya dace mu zo mu yi hulɗa da ma’aikatu, mu saurari bayanan su, sannan mu daidaita hanyoyin sadarwar mu domin mu tafi a hanya guda domin cigaban ƙasar mu.”

Idris ya ƙara da cewa wannan hulɗar wani ɓangare ne na ƙoƙarin da ake yi na ƙarfafa haɗin gwiwa da manyan cibiyoyin gwamnati domin inganta yaɗa bayanan gwamnati kan manufofi da gyare-gyaren da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu take aiwatarwa.

Ya ce manufar ziyarar ita ce ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ma’aikatun biyu, musamman wajen sanar da jama’a gyare-gyaren da ake yi a fannonin ayyukan shige-da-fice, tsarin biza, da sauran muhimman fannoni da ke ƙarƙashin Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida.

A cewar sa, samun ingantacciyar hanyar yaɗa labarai kan manufofin gwamnati yana da matuƙar muhimmanci wajen ƙara fahimtar jama’a, ƙarfafa amincewar ƙasa, da kuma gabatar da Nijeriya a kyakkyawar siga ga ƙasashen duniya.

Ya ce: “Aikin mu shi ne tabbatar da cewa duk abin da gwamnati ke yi, ’yan Nijeriya suna ji kuma suna fahimta.”

Ya ƙara da cewa: “Saboda haka, duk abin da kuke yi a nan, rawar da muke takawa ita ce mu taimaka wajen faɗaɗa yaɗa bayanan sa domin ’yan Nijeriya da kuma al’ummomin duniya su fahimci gyare-gyaren da ake aiwatarwa.”

Ministan ya kuma nuna muhimmancin haɗa saƙon ƙasa wuri guda kan tsaro da shugabanci, yana mai jaddada cewa dole ne cibiyoyin gwamnati su yi aiki tare domin tabbatar da cewa sahihin bayani yana isa ga jama’ar ƙasa tare da daƙile yaɗuwar labaran ƙarya.

Ya ƙara da cewa: “Akwai kuma buƙatar mu ƙara haɗa kai wajen isar da saƙon tsaron ƙasa.

“Yana da matuƙar muhimmanci Nijeriya ta kasance da labari guda ɗaya kan abin da ke faruwa a ƙasar nan da kuma yadda gwamnati take magance ƙalubalen da ake fuskanta.”

Ya jaddada ƙudirin Gwamnatin Tarayya na gabatar da kyawawan gyare-gyaren tattalin arziki da na shugabanci da ake yi a Nijeriya ga duniya baki ɗaya, yana mai cewa sababbin alamomin tattalin arziki da hulɗar ƙasa da ƙasa sun nuna ƙarin amincewa da ƙasar nan.

Da yake mayar da martani, Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ya jaddada cewa haɗin gwiwa tsakanin ma’aikatun biyu yana da matuƙar muhimmanci wajen yaɗa bayanai kan manufofi da gyare-gyaren gwamnati, musamman a fannoni da suka shafi zama ɗan ƙasa, kula da shige-da-fice, da tsaron ƙasa.

Ya ce: “Haɗin gwiwa tsakanin Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida da Ma’aikatar Yaɗa Labarai yana da matuƙar muhimmanci wajen yaɗa bayanai yadda ya kamata.

“Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida tana kula da al’amuran zama ɗan ƙasa da ingancin tsarin zama ɗan ƙasa, yayin da ku kuma kuke kula da wayar da kan jama’ar ƙasa.”

Ministan ya bayyana wasu gyare-gyare da ma’aikatar sa ta aiwatar a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu, musamman a Hukumar Shige-da-Fice ta Nijeriya, wanda ya haɗa da warware tarin buƙatun fasfo da suka maƙale, ƙaddamar da tsarin sabunta fasfo ta yanar gizo ga ’yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje ba tare da zuwa ofis ba, da kuma amfani da sababbin fasahohi wajen kula da iyakokin ƙasa.

A cewar sa, gwamnati ta samu gagarumin cigaba wajen inganta ayyukan shige-da-fice da kuma ƙarfafa tsarin tsaron ƙasa.

Tunji-Ojo ya ce: “Lokacin da Shugaban Ƙasa ya hau mulki a shekarar 2023, muna da tarin buƙatun fasfo guda 204,332 da ba a kammala ba. Wannan gwamnati ta warware su cikin makonni biyu da rabi kacal, tare da tabbatar da cewa ’yan Nijeriya ba za su koma zamanin ƙarancin fasfo ba.”

Ya kuma bayyana cewa ma’aikatar ta ƙaddamar da hanyoyin fasaha domin ƙarfafa tsaron iyakoki, sabunta tsarin shige-da-fice, da kuma inganta ayyukan hidima ga ’yan Nijeriya a gida da waje.

Ministan ya kuma gayyaci Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai da ta kai rangadi na musamman domin duba manyan gyare-gyare da cigaban ababen more rayuwa da ake aiwatarwa a hukumomin da ke ƙarƙashin Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, ciki har da Hukumar Shige-da-Fice ta Nijeriya, Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, Hukumar Gyaran Hali ta Nijeriya, da kuma Hukumar Tsaro da Kare Jama’a ta Nijeriya.

Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da manyan jami’ai daga ma’aikatun biyu, ciki har da Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Dakta Magdalene Ajani; Daraktan Sadarwar Jama’a, Barr. Henshaw Ogubike; Daraktan Hulɗa da Jama’a da Tsara Karɓar Baƙi, Dakta Suleiman Haruna; da manyan masu ba da shawara daga Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta Tarayya, tare da daraktoci da ma’aikatan gudanarwa na Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida.

Tags: MohammedIdrisOlubunmiTunji-OjoShigedaFicetsaroziyara
Previous Post

Mojtaba Khamenei ya gaji mahaifin sa a a matsayin sabon Jagoran Ƙolin Iran

Next Post

Tinubu ya nemi amincewar Majalisa kan naɗin Lamiɗo Yuguda a matsayin mataimakin gwamnan CBN

Related Posts

Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista
Siyasa

Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista

May 5, 2026
Ranar ’Yancin ’Yan Jarida ta Duniya: Nijeriya na neman a haɗa gwiwa a yaƙi masu yaɗa labaran ƙarya
Labarai

Ranar ’Yancin ’Yan Jarida ta Duniya: Nijeriya na neman a haɗa gwiwa a yaƙi masu yaɗa labaran ƙarya

May 4, 2026
Kwankwaso da Obi sun koma NDC
Siyasa

Kwankwaso da Obi sun koma NDC

May 3, 2026
Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi
Siyasa

Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi

May 3, 2026
Shettima ya ƙaddamar da jigilar maniyyatan Hajjin bana da kwashe alhazai 500 a Abuja
Labarai

Shettima ya ƙaddamar da jigilar maniyyatan Hajjin bana da kwashe alhazai 500 a Abuja

May 3, 2026
Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC
Siyasa

Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC

May 1, 2026
Next Post
Tinubu ya nemi amincewar Majalisa kan naɗin Lamiɗo Yuguda a matsayin mataimakin gwamnan CBN

Tinubu ya nemi amincewar Majalisa kan naɗin Lamiɗo Yuguda a matsayin mataimakin gwamnan CBN

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!