• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya umurci bankuna su yi gwajin ƙarfin jure matsin tattalin arziki

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
March 8, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki, Rahoton Musamman
A A
0
Yadda tsare-tsaren CBN ke daƙile hauhawar farashi da tsadar rayuwa
Babban Bankin Nijeriya (CBN)

Babban Bankin Nijeriya (CBN)

Yayin da saura makonni uku wa’adin ƙarfafa jarin bankuna da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya gindaya su cika, yanzu kuma CBN ya umurci dukkan bankunan kasuwanci su yi gwajin ƙarfin juriyar matsin tattalin arziki, wato ‘stress test’.

Wannan umarni ya zo ne yayin da yake ci gaba da sa-ido kan tsarin bankunan domin gano yiwuwar rauni a cikin su.

An fito da wannan umarni ne a cikin wata wasiƙa da jaridar The Cable ta ruwaito cewa ta gani a ranar Asabar.

Wasiƙar dai an aika ta ga dukkan bankuna, kuma tana ɗauke da umarnin ne a ranar 6 ga Maris, 2026.

Wannan rana dai kuma ita ce ranar da CBN ya sanar cewa tsarin bankunan Nijeriya yana nan cikin kwanciyar hankali kuma yana da ƙarfi.

Wannan sabon umurni na mai kula da bankuna ya zo ne a daidai lokacin da bankuna ke cikin shirin ƙara jarin su, yayin da wa’adin ranar 31 ga Maris, 2026 da CBN ya sanya ke gabatowa.

Menene Gwajin Jure Matsin Tattalin Arziki?

Gwajin dai wata hanya ce da ake amfani da ita domin auna yadda banki zai iya jure matsanancin yanayin tattalin arziki, kamar irin su tsananin durƙushewar tattalin arziki, faɗuwar kasuwanni ko wasu nau’ukan tangal-tangal da girgiza tattalin arziki.

Dalilin Umarnin CBN

A cikin wasiƙar, CBN ya ce wannan umarni ya yi daidai da tanadin dokar da ‘Banks and Other Financial Institutions Act (BOFIA) ta 2020, musamman sashe na 13 da na 63, waɗanda suka tanadi cewa bankuna dole su riƙa riƙe jari mai isasshen ƙarfi domin rufe duk wata barazana da haɗurran da ke tattare da ayyukan su.

CBN ya kuma ce wannan umarni bai sauya ƙa’idojin gwajin da aka fitar a Maris 2019 ba.

Abubuwan Da CBN Ya Umurci Bankuna Su Gwada

CBN ya umarci bankuna su gwada yadda kundin jimillar bashin su zai iya jure matsin tattalin arziki cikin watanni 12.

Za su yi hakan ta hanyar kwaikwayon abubuwa da suka haɗa da lalacewar ingancin kadarori, haɗarin shugabanci da gudanarwa, faɗuwar farashin kayayyaki a kasuwa, motsin hawa da saukar farashin canjin kuɗi a kasuwar musayar kuɗaɗen waje, canje-canje a kasuwannin kamfanonin da suka karɓi bashi, tangarɗar tsarin samar da kayayyaki, sai kuma raguwar buƙatar kayayyaki.

Abubuwan Da za Da Za A Tantance

Gwajin zai tantance tasirin waɗannan abubuwa ga a kan sikelin bashin da ba a biya ba, wato a Turance Non-Performing Loans – NPLs, adadin tanadin asarar bashi, da kuma wadatar jari na banki.

Yayin gwajin, CBN ya umurci bankuna su haɗa da dukkan bashin da ke cikin littafin su, bashin da ba a rubuta kai tsaye ba, sai kuma bashin da ya shafi daraktoci ko ma’aikatan ciki.

Haka kuma dole ne su yi hasashen cewa dangane da wasu basussukan za su matsa wa zuwa mataki mafi haɗari bisa ƙa’idodin PG da CBN ya gindaya.

Dangane da buƙatar ƙarin jari idan aka samu giɓin jari, CBN ya ce idan sakamakon gwajin ya nuna cewa banki yana da giɓin jari, to dole bankin ya tara kashi 100% na giɓin jarin da gwajin bankin ya nuna, ko kuma kashi 50% na giɓin da CBN ya lissafa, wato duk wanda ya fi yawa a tsakanin biyun. Kuma za a baiwa bankin watanni 18 domin cike wannan giɓin jari.

Bayan haka, wannan sabon matakin jari zai zama sabuwar buƙatar jarin bankin bisa barazanar haɗarin da ka iya aukawa kan jarin banki, har zuwa zagayen gwaji na gaba.

Daga nan CBN ya umurci bankuna su miƙa rahoton wannan gwajin da kwamitin gudanarwar su zai amince da shi kafin ƙarshen aiki a ranar 30 ga Afrilu.

Idan kuma banki bai nuna giɓin jari ba bayan gwajin, to za a ci gaba da yin wannan gwajin duk bayan watanni 12.

Previous Post

Bankuna 30 ne suka cika sababbin ƙa’idojin ƙarfafa jari – CBN

Next Post

Mojtaba Khamenei ya gaji mahaifin sa a a matsayin sabon Jagoran Ƙolin Iran

Related Posts

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gangamin CBN a Kano: A daina wulaƙanta takardun naira, a riƙe su cikin inganci da nagarta – CBN

September 29, 2026
Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Rahoton Musamman

Taƙaitaccen Tarihin Ɗanwaire Da Ƙasar Ruma

September 16, 2026
Next Post
Mojtaba Khamenei ya gaji mahaifin sa a a matsayin sabon Jagoran Ƙolin Iran

Mojtaba Khamenei ya gaji mahaifin sa a a matsayin sabon Jagoran Ƙolin Iran

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!