
Gwamnatin Tarayya ta buƙaci ɗaukacin ‘yan Nijeriya dake zaune a ƙasar Iran da sauran ƙasashen yankin Tekun Fasha da su kasance cikin tsananin sa ido da kiyaye kai, biyo bayan takun-saƙa da hare-haren soji da suka ɓarke a yankin.
A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Waje ta fitar a ranar Asabar, 28 ga Fabrairu, 2026, wadda kakakin ma’aikatar, Kimiebi Imomotimi Ebienfa, ya sanya wa hannu, gwamnatin ta bayyana cewa tana sanya idanu sosai kan yadda al’amura ke sauyawa bayan hare-haren da Isra’ila da Amurka suka kai kan wasu wurare a Iran, da kuma martanin da ita ma Iran ɗin ta mayar.
Don tabbatar da tsira da lafiyar ‘yan ƙasar nan, ma’aikatar ta fitar da wasu shawarwari guda biyar kamar haka:
* Gwamnati ta shawarci ‘yan Nijeriya da su guji zirga-zirga a kusa da sansanonin soji, gine-ginen gwamnati, ko wuraren da ake ganin za su iya zama matattarar rikici.
* An buƙaci mutane da su zauna a gida muddin ba wata muhimmiyar buƙata ce ta fitar da su ba, sannan su guji shiga taron jama’a ko zanga-zanga.
* An buƙaci ‘yan kasa da su kiyaye dukkan dokoki da matakan tsaro da hukumomin ƙasashen da suke ciki suka gindaya.
* Ma’aikatar ta buƙaci mutane da su riƙa sauraron kafafen yaɗa labarai na ƙasa da ƙasa masu gaskiya, sannan su kiyayi yaɗa labaran bogi.
* Sanarwar ta tabbatar da cewa ofisoshin jakadancin Nijeriya da ke Tehran (Iran), Ƙatar, Bahrain, Kuwait, Haɗɗaɗiyar Daular Larabawa (UAE), da Saudi Arabiya suna cikin shirin ko-ta-kwana don tallafa wa duk wani ɗan Nijeriya da ya shiga cikin matsala.
A ƙarshe, gwamnatin ta yi kira ga ɗaukacin ɓangarorin da rikicin ya shafa da su kwantar da hankalin su, su ajiye makamai su koma kan teburin tattaunawa domin samar da zaman lafiya a duniya.
Ta kuma sake jaddada cewa kare rayukan ‘yan Nijeriya a duk inda suke a faɗin duniya shi ne babban burin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.







