Gwamnatin ƙasar Amurka ta bayyana cewa za ta kashe dala miliyan 200 na tallafi kai-tsaye ga fiye da asibitoci guda 900 na mabiya addinin Kirista a cikin shekaru biyar masu zuwa.
Wannan wani ɓangare ne na wata Yarjejeniyar Fahimta (MOU) ta haɗin gwiwa tsakanin Amurka da Nijeriya kan kiwon lafiya ta tsawon shekaru biyar, wadda ta kai dala biliyan 5.1, domin ƙarfafa Shirin Kiwon Lafiya na Duniya na America First.
Wata sanarwa da Ofishin Jakadancin Amurka a Abuja ya fitar ta ce: “Ƙarƙashin wannan yarjejeniyar, Amurka tana shirin bayar da dala biliyan 2.1 a matsayin tallafi, yayin da Nijeriya za ta zuba dala biliyan 3.0 daga cikin kuɗaɗen ta na harkar kiwon lafiya cikin shekaru biyar — wannan shi ne mafi girman haɗin zuba jari da kowace ƙasa ta taɓa yi ƙarƙashin wannan shiri zuwa yanzu.
“Wannan yarjejeniya ta shekaru biyar za ta ƙarfafa tsarin kiwon lafiyar Nijeriya, ta ceci rayuka, kuma ta sa Amurka ta fi zama mai aminci, ƙarfi da wadata.”
Sanarwar ta ƙara da cewa yarjejeniyar ta haɗa da kusan dala miliyan 200 na tallafi kai-tsaye ga fiye da cibiyoyin kiwon lafiya 900 na addinin Kirista, domin faɗaɗa samun damar ayyukan lafiya haɗaɗɗu na HIV, tarin fuka (TB), zazzaɓin cizon sauro (wato maleriya), da kuma lafiyar uwa da jariri.
Ta ce: “Cibiyoyin kiwon lafiya na addinin Kirista suna wakiltar kusan kashi 10 cikin ɗari na masu ba da hidimar kiwon lafiya a Nijeriya, amma suna hidimta wa fiye da kashi 30 cikin ɗari na al’ummar Nijeriya miliyan 230, musamman a yankunan da ba su da wadatattun kayan aiki.
“Da yake Nijeriya tana fuskantar ɗaya daga cikin mafi munin matsalolin mutuwar uwa da jarirai a duniya, tare da ɗaukar kashi 30 cikin ɗari na nauyin cutar zazzaɓin cizon sauro a duniya, wannan tallafin na Amurka yana kare rayukan ’yan Nijeriya da na Amurkawa tare da ƙarfafa haɗin gwiwar mu ta ƙasashe biyu.”








