Gwamnatin Tarayya ta bada sanarwar cewa dukkan ɗaliban makarantar St. Mary’s Catholic School da ke Papiri, Jihar Niger, da aka sace sun samu ‘yanci gaba ɗaya, ba tare da an bar ko ɗaya a hannun masu garkuwa da mutane ba.
Hakan ya fito ne daga bakin Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, a wurin taron manema labarai na ƙarshen shekara da ya gudana a yau Litinin a otal ɗin Nicon Luxury da ke Abuja.
Ministan ya ce sakin ɗaliban 130 na ƙarshe da aka yi a jiya Lahadi ya kawo adadin ɗaliban da aka ceto zuwa 230.
Ya yaba da jajircewar hukumomin tsaro, kuma ya miƙa saƙon jaje ga iyayen ɗaliban, tare da yi masu fatan samun sauƙin raɗaɗin da suka sha da kuma bikin Kirsimeti cikin annashuwa.
Nasarorin Gwamnati a 2025
A cewar Ministan, a madadin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Gwamnatin Tarayya na yin hisabi kan ayyukan da ta aiwatar a shekarar 2025 tare da bayyana tsare-tsaren shekarar 2026.
Ya bayyana cewa tattalin arzikin Nijeriya ya samu cigaba, inda kuɗin shiga suka ƙaru da kashi 3.98 cikin ɗari a zangon uku na 2025, yayin da hauhawar farashi ya ragu tsawon watanni takwas a jere zuwa kashi 14.45 cikin ɗari a watan Nuwamba 2025.
Haka kuma, ajiyar kuɗaɗen ƙasar waje ya kai kusan dala biliyan 44.56.
Ministan ya ce Nijeriya ta samu rarar kasuwanci ta naira tiriliyan 6.69 a zangon uku na shekarar, tare da samun kwanciyar hankali a harkokin kasuwanci bisa bayanan Purchasing Managers Index (PMI) da ke nuna ci gaba na tsawon watanni 12.
Wutar Lantarki da Ayyukan More Rayuwa
A fannin lantarki, Ministan ya ce Nijeriya ta kai ƙololuwar samar da wutar lantarki a tarihi, inda aka samar da megawatt-hours 128,370.75 a rana guda a watan Maris 2025.
An kuma ƙaddamar da Shirin Rarraba Mita na Shugaban Ƙasa (PMI) da kuma shirin rage basussukan lantarki.
Haka kuma, gwamnati ta ware sama da naira tiriliyan 1.5 don gina hanyoyi a 2025, ciki har da manyan hanyoyi guda huɗu da za su haɗa yankunan ƙasa baki ɗaya, kamar hanyar Legas–Kalaba, Sakkwato–Badagiri, da sauran su.
Matasa da Ilimi
Ministan ya bayyana cewa fiye da ɗalibai 788,000 sun amfana da lamunin karatu mara ruwa ta hannun NELFUND, inda aka kashe sama da naira biliyan 150.
Ya kuma ambaci shirye-shiryen 3MTT, iDICE, da Student Venture Capital Grant (S-VCG) a matsayin hanyoyin bunƙasa basirar matasa da samar da ayyukan yi.
Tsaro da Hulɗar Ƙasa da Ƙasa
A ɓangaren tsaro, Ministan ya ce Shugaba Tinubu ya ayyana dokar gaggawa ta tsaro a faɗin ƙasa, tare da ɗaukar sababbin jami’an tsaro da kafa sabuwar manhajar yaƙi da ta’addanci.
Ya jaddada cewa duk wata ƙungiya da ke satar mutane ko kai hari za a ɗauke ta a matsayin ƙungiyar ta’addanci.
A fagen diflomasiyya, ya ce Nijeriya ta ƙarfafa dangantakar ta da Amurka, inda aka rattaba hannu kan yarjejeniyar kiwon lafiya ta dala biliyan 5.1.
Har ila yau, Nijeriya ta dawo da kujerar ta a Hukumar Kula da Harkokin Ruwa ta Duniya (IMO) bayan shekaru 14.
Kasafin Kuɗin 2026
Ministan ya bayyana Kasafin Kuɗin 2026 mai suna “Kasafin Ƙarfafa Cigaba da Wadata ga Kowa”, wanda ya kai naira tiriliyan 58.18, inda aka ware mafi girman kuɗin ga harkar gine-gine da tsaro a tarihin ƙasar nan.
A ƙarshe, Idris ya ce shekarar 2025 ta kasance ta gina tubalan cigaba, yayin da 2026 za ta kasance shekarar bunƙasa tsaro, tattalin arziki da walwalar al’umma.
Ya yi wa ‘yan Nijeriya fatan barka da Kirsimeti da Sabuwar Shekara, tare da addu’ar Allah ya albarkaci Jamhuriyar Tarayyar Nijeriya.







