• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Kiwon Lafiya

Amurka za ta kashe dala miliyan 200 na tallafi kai-tsaye ga fiye da asibitoci 900 na mabiya addinin Kirista a Nijeriya

* ... ita da Nijeriya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar dala biliyan 5.1 ta tsawon shekaru biyar kan kiwon lafiya

ALI KANO by ALI KANO
December 21, 2025
in Kiwon Lafiya
A A
0
Amurka za ta kashe dala miliyan 200 na tallafi kai-tsaye ga fiye da asibitoci 900 na mabiya addinin Kirista a Nijeriya
Ministan Kiwon Lafiya da Walwala, Farfesa Ali Pate, da Ministan Ilimi, Wale Edun, da wani babban jami'in Ofishin Jakadancin Amurka a lokacin taron saka hannu a yarjejeniyar

Ministan Kiwon Lafiya da Walwala, Farfesa Ali Pate, da Ministan Ilimi, Wale Edun, da wani babban jami'in Ofishin Jakadancin Amurka a lokacin taron saka hannu a yarjejeniyar

Gwamnatin ƙasar Amurka ta bayyana cewa za ta kashe dala miliyan 200 na tallafi kai-tsaye ga fiye da asibitoci guda 900 na mabiya addinin Kirista a cikin shekaru biyar masu zuwa.

Wannan wani ɓangare ne na wata Yarjejeniyar Fahimta (MOU) ta haɗin gwiwa tsakanin Amurka da Nijeriya kan kiwon lafiya ta tsawon shekaru biyar, wadda ta kai dala biliyan 5.1, domin ƙarfafa Shirin Kiwon Lafiya na Duniya na America First.

Wata sanarwa da Ofishin Jakadancin Amurka a Abuja ya fitar ta ce: “Ƙarƙashin wannan yarjejeniyar, Amurka tana shirin bayar da dala biliyan 2.1 a matsayin tallafi, yayin da Nijeriya za ta zuba dala biliyan 3.0 daga cikin kuɗaɗen ta na harkar kiwon lafiya cikin shekaru biyar — wannan shi ne mafi girman haɗin zuba jari da kowace ƙasa ta taɓa yi ƙarƙashin wannan shiri zuwa yanzu.

“Wannan yarjejeniya ta shekaru biyar za ta ƙarfafa tsarin kiwon lafiyar Nijeriya, ta ceci rayuka, kuma ta sa Amurka ta fi zama mai aminci, ƙarfi da wadata.”

Sanarwar ta ƙara da cewa yarjejeniyar ta haɗa da kusan dala miliyan 200 na tallafi kai-tsaye ga fiye da cibiyoyin kiwon lafiya 900 na addinin Kirista, domin faɗaɗa samun damar ayyukan lafiya haɗaɗɗu na HIV, tarin fuka (TB), zazzaɓin cizon sauro (wato maleriya), da kuma lafiyar uwa da jariri.

Ta ce: “Cibiyoyin kiwon lafiya na addinin Kirista suna wakiltar kusan kashi 10 cikin ɗari na masu ba da hidimar kiwon lafiya a Nijeriya, amma suna hidimta wa fiye da kashi 30 cikin ɗari na al’ummar Nijeriya miliyan 230, musamman a yankunan da ba su da wadatattun kayan aiki.

“Da yake Nijeriya tana fuskantar ɗaya daga cikin mafi munin matsalolin mutuwar uwa da jarirai a duniya, tare da ɗaukar kashi 30 cikin ɗari na nauyin cutar zazzaɓin cizon sauro a duniya, wannan tallafin na Amurka yana kare rayukan ’yan Nijeriya da na Amurkawa tare da ƙarfafa haɗin gwiwar mu ta ƙasashe biyu.”

Ministocin Nijeriya da jami’an gwamnatin Amurka suna rattaba hannu kan yarjejeniyar
Tags: Amurkaasibitocin Kiristakiwon lafiyayarjejeniya
Previous Post

Ɗaliban Papiri: Nasara da kwanciyar hankali ga Nijeriya sun zo – Idris

Next Post

Duk ɗaliban da aka sace a Neja sun kuɓuta, tattalin arzikin Nijeriya yana ci gaba da farfaɗowa – Minista

Related Posts

Tinubu ya naɗa Fatima Zuntu shugabar hukumar NBMA
Kiwon Lafiya

Tinubu ya naɗa Fatima Zuntu shugabar hukumar NBMA

April 20, 2026
Likitoci za su fara yajin aiki na gama-gari daga Talata
Kiwon Lafiya

Likitoci za su fara yajin aiki na gama-gari daga Talata

April 5, 2026
Uwargidan Shugaban Ƙasa ta ƙaddamar da Asusun Ciyarwar Abinci na Ƙasa, ta ba da gudunmawar naira miliyan 500
Kiwon Lafiya

Uwargidan Shugaban Ƙasa ta ƙaddamar da Asusun Ciyarwar Abinci na Ƙasa, ta ba da gudunmawar naira miliyan 500

April 3, 2026
Ranar Ji ta Duniya 2026: Dalilan da za a iya kauce wa suna ci gaba da haddasa naƙasar ji a tsakanin yara a Nijeriya – Minista
Kiwon Lafiya

Ranar Ji ta Duniya 2026: Dalilan da za a iya kauce wa suna ci gaba da haddasa naƙasar ji a tsakanin yara a Nijeriya – Minista

March 3, 2026
Nijeriya ta rattaba hannu kan babbar yarjejeniyar zuba jari a fannin kiwon lafiya
Kiwon Lafiya

Nijeriya ta rattaba hannu kan babbar yarjejeniyar zuba jari a fannin kiwon lafiya

February 5, 2026
Cewar Minista: Gwamnati ta saki da naira biliyan 32.9 don inganta kiwon lafiya
Kiwon Lafiya

Cewar Minista: Gwamnati ta saki da naira biliyan 32.9 don inganta kiwon lafiya

October 14, 2025
Next Post
Duk ɗaliban da aka sace a Neja sun kuɓuta, tattalin arzikin Nijeriya yana ci gaba da farfaɗowa – Minista

Duk ɗaliban da aka sace a Neja sun kuɓuta, tattalin arzikin Nijeriya yana ci gaba da farfaɗowa – Minista

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!