Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da Kasafin Kuɗin Tarayya na shekarar 2026 a gaban zaman haɗin gwiwar Majalisar Tarayya, inda ya bayyana cewa kasafin ya mayar da hankali kan ƙarfafa harkar tsaro, bunƙasa tattalin arziki, inganta jin daɗin al’umma da gina ƙasa mai ɗorewa.
Kasafin, mai taken “Kasafin Ƙarfafa Tushen Arziki, Sabunta Juriya da Samar da Cigaba Ga Kowa”, ya nuna aniyar gwamnati ta ƙarfafa nasarorin da aka samu a cikin shekaru biyu da rabi na gyare-gyaren tattalin arziki, tare da tabbatar da cewa cigaban da ake samu ya shafi rayuwar talakawa kai-tsaye.
Sha’anin Tsaro Da Kare Ƙasa
Tinubu ya bayyana cewa tsaro shi ne ginshiƙin cigaban ƙasa, inda aka ware naira tiriliyan 5.41 domin harkokin tsaro da kare ƙasa.
Ya ce za a mayar da hankali kan ƙarfafa rundunonin soji, inganta leƙen asiri, tsaron iyakoki da amfani da fasahar zamani wajen sa-ido.
Ya jaddada cewa gwamnati ba za ta yi sassauci ba wajen yaƙi da ta’addanci, ‘yan fashi da makami, garkuwa da mutane da sauran laifuffuka masu tada hankali, inda duk wata ƙungiya mai ɗauke da makamai ba tare da izinin gwamnati ba za a ɗauke ta a matsayin ƙungiyar ta’addanci.
Lafiya
A fannin lafiya, shugaban ya bayyana cewa an ware naira tiriliyan 2.48, wato kusan kashi 6 cikin 100 na kasafin baki ɗaya, domin inganta asibitoci, kayan aiki da kula da lafiyar jama’a.
Ya kuma bayyana cewa haɗin gwiwa da gwamnatin Amurka ya buɗe hanyar samun dala miliyan 500 domin ayyukan kiwon lafiya a faɗin ƙasar nan, wanda zai taimaka wajen rage raɗaɗi ga marasa galihu.
Noma Da Samar Da Abinci
Tinubu ya jaddada cewa wadatar abinci yana daga cikin manyan manufofin kasafin 2026.
Ya ce gwamnati za ta zuba jari a tallafin kayan noma, injinan ban-ruwa, ajiyar amfanin gona da sarrafa shi, domin rage asara bayan girbi da ƙara kuɗin shiga ga manoma.
Ya bayyana cewa Bankin Manoma zai jagoranci wani shiri da zai bai wa manoma damar noma hekta miliyan ɗaya, tare da samar da dubban ayyukan yi da kuma bunƙasa fitar da kayan noma zuwa ƙasashen waje.
Ilimi
A ɓangaren ilimi, kasafin ya ware naira tiriliyan 3.52, inda aka mayar da hankali kan faɗaɗa damar shiga manyan makarantu.
Shugaban ya bayyana cewa asusun rancen karatu na NELFUND ya riga ya tallafa wa sama da ɗalibai 788,000 a faɗin manyan makarantu 229, lamarin da ke rage nauyin karatu ga iyaye da ɗalibai.
Ababen More Rayuwa Da Tattalin Arziki
An ware naira tiriliyan 3.56 domin ababen more rayuwa, ciki har da hanyoyi, makamashi, tashoshin jiragen ruwa da ayyukan da ke jan jari daga masu zaman kan su.
Shugaban ya ce ba tare da hanyoyi, wutar lantarki da sufuri ba, ba za a samu ayyukan yi ko bunƙasar kasuwanci ba.
Manufofi Da Alƙibla
Tinubu ya bayyana cewa kasafin 2026 ya ta’allaƙa ne kan manyan manufofi guda huɗu: ƙarfafa tattalin arziki, inganta yanayin kasuwanci, samar da ayyukan yi da rage talauci, da kuma kare marasa ƙarfi a cikin al’umma.
A ƙarshe, shugaban ya buƙaci Majalisar Dokoki da ‘yan Nijeriya gaba ɗaya da su bada haɗin kai domin aiwatar da kasafin yadda ya dace, yana mai cewa, “Muhimmin kasafi ba shi ne wanda aka bayyana ba, sai wanda aka aiwatar.”
Kasafin na 2026, a cewar sa, zai zama ginshiƙi wajen kai Nijeriya ga tsaro, wadatar abinci, ingantaccen kiwon lafiya, ilimi mai amfani da tattalin arziki mai ɗorewa, bisa tafarkin Ajandar Sabunta Fata.







