Kwanaki na ƙarshe na tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, bayan kammala mulkin sa na shekaru takwas, sun kasance masu matuƙar raɗaɗi ga iyalin sa sakamakon tsananin matsalolin lafiyar sa.
Buhari dai ya haura shekaru tamanin ne lokacin da ya kammala wa’adin mulkin sa biyu.
A cikin littafin From Soldier to Statesman: The Legacy of Muhammadu Buhari, wanda Dakta Charles Omole ya rubuta, tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa, Hajiya Aisha Buhari, ta ba da labari cewa: “Kwanaki na ƙarshe sun kasance masu wahala. An kwantar da shi a sashen gaggawa a asibiti (ICU) na wasu kwanaki, sai aka kai shi ɗaki, daga nan sai aka samu koma-baya. Kwanaki ukun ƙarshe su ne mafi muni.”
Littafin ya ambato A’isha tana cewa: “Bayan barin mulki, a shekarar sa ta ƙarshe kafin rasuwar sa, kiran waya ya ƙaru, kuma tafiye-tafiye zuwa ƙetare (musamman Amurka da Turai) suka yawaita. Lokutan iyalin ta cika da jana’iza da hawa jiragen sama.
“Ya tafi Birtaniya, kamar yadda ya saba, domin duba haƙori da kuma jin daɗin iska ta lokacin bazara. Ita kuwa ta zauna a Abuja tana makokin wani ɗan’uwan ta, daga nan ta koma Landan kafin ta dawo Nijeriya lokacin da wani kawun taq ya rasu.”
Bayanin ta game da rashin lafiyar sa da rasuwar sa yana da taushi, cike da cikakkun bayanai, kuma ba tare da ɓoye gaskiya ba.
Ta ce Buhari ya taɓa zaman soja a jeji tsawon watanni 30, galibi a yankin Kudu-maso-Kudu, yana jiƙa da ruwan sama cikin khakin soja da suke bushewa a jikin sa. Bayan shekaru masu yawa, a cewar ta, sanyi ya maƙale a huhu da ƙasusuwa—lamarin da esi a ofis ta ƙara tsanantawa. Ta yarda cewa ya taɓa shan taba a baya. Nauyin shekaru kuma ya ƙara tasiri. Cutar huhu (pneumonia) ce ta zama abokin gaba na ƙarshe.
Tarihin rayuwar ya nuna cewa ’ya’yan Buhari suna yawan karakaina a hanyar asibiti, inda wata ’ya mace ta kwana a gefen sa a daren jajibirin ƙarshen rasuwar sa. Lokacin da yanayin sa ya tsananta, likitoci suka tabbatar akwai cutar numoniya mai tsanani a tare da shi—wani abu da bai gamsar da jama’a da suke neman ƙarin bayani dalla-dalla ba.
An tambaye ta cewa: “Numoniya ba ta cika kashe mutane ba.” Sai ta amince, amma ta ce: “Tana iya kashewa, musamman idan mutum ya tsufa, kuma wataƙila idan ya shafe rayuwa yana fuskantar sanyi da ƙura a wajen aiki. Shi kullum yana tari, har ma lokacin da yake dariya.”
Hajiya A’isha ta tuna da yadda ta yi ƙoƙarin ɗaga kafaɗar mijin ta domin saka matashin kai kamar yadda wata ma’aikaciyar jinya ‘yar ƙasar Gambiya ta ba ta shawarar ta yi, don rage tasirin numoniyar a huhun sa. “Sun ƙirga tare, ‘Ɗaya, biyu, uku,’ amma ba su iya ɗaga shi ba—wanda a hannun ta ya yi kamar kilo 50 na mijin ta da tarihin rayuwar su tare. Sai dai suka saka matashin kai a gefe, alamar yin sassauci. ‘Kana jin daɗi yanzu?’ ta tambaye shi. ‘E, na gode,’ ya amsa.”
Akwai sauye-sauye da addu’o’i, sauyin ’ya’yan da suke kwana a gefen sa, wani matashin likitan Nijeriya da ke burge ta, hotunan X-ray da aka ɗauka da safe sannan aka sake ɗauka daga baya da na’urar tafi-da-gidan-ka, da kuma ‘yar ƙaramar fata bayan sakamakon gwajin majina ya fito ba tare da mummunar sakamako ba. Sun ce numoniya ce, amma a shekarun sa, numoniya na iya zama mai tsanani.
Da ƙarfe 2 na rana, ta ce masa za ta koma gida ta huta, ta yi wanka, ta yi sallah, sannan ta dawo. Ya girgiza kai, idanu a rufe, yana buɗewa lokaci-lokaci cikin natsuwa da rashin kwanciyar hankali na mara lafiya, kamar yana auna tazarar da ke tsakanin yarda da ƙaddara da kuma ƙoƙarin rayuwa. Ta kira tasin Uber—tun da motocin gwamnati sun tafi tare da likitoci—ta hau ta bar asibitin.
A gida, ta kwanta sai ta ji wani abu: wani wata fizga a ran ta mai ban-mamaki, wani tashin hankali da ya sa ƙarar agogon minti ta yi ƙarfi fiye da yadda ya kamata. “Mu koma asibiti,” ta ce wa Yusuf.
A lokacin ƙarfe 4 na yamma ne, ainihin lokacin da ta gano daga baya cewa numfashin Buhari ya sauya sannan ya tsaya. “Ba kasafai muke isa bakin ƙofar mutuwa kafin ta faru ba. Muna jin ta ne kawai a matsayin rawar jiki a bayan ƙofa,” inji ta.
Hajiya A’isha ta yi magana kan ji-ta-ji-tar da ake yi cewa wai mijin ta ya mutu ne da cutar daji, wato kansa, tana cewa sakamakon binciken likita da aka ba su dai ya nuna numoniya ce.
Ta ce: “Wasu majiyoyi sun ruwaito cewa cutar daji da ta shafi huhu, musamman pulmonary lymphoma. Masana sun ce gano pulmonary lymphoma na da wahala, domin alamominta da hotunan bincike na iya kama da na numoniya. Masu cewa Buhari ya mutu da cutar daji na iya yin kuskuren fassara alamomin da suka fita fili.”
A’isha ta dage cewa likitoci sun gano a zahiri cewa numoniya ce. Rahotannin jama’a sun bayyana “doguwar rashin lafiya,” wasu sun ambaci cutar daji ta leukemia. Rahoton BBC ya ce “ƙaramin rashin lafiya” da binne shi a Daura bayan kwana biyu; jaridar The Guardian ta ambaci “doguwar rashin lafiya” a Landan; wasu kafafe, ciki har da shafukan fafutuka, sun ambaci leukemia; kundin tarihi na Britannica ya rubuta rasuwar sa a Landan yana da shekara 82.
Labarin A’isha ya ƙara bayanai na kusa da zuciya: mujallar da ke hannun sa a ICU; ɗan barkwanci game da kai shi ɗaki na musamman, “tunda kana lafiya har kana kallon talbijin,” tana zolayar sa.
Littafin ya ambaton wasu masana cewa rashin kyakkyawar dabarar sadarwa na daga cikin raunin gwamnatin Buhari. “Ƙananan abubuwa marasa muhimmanci sun rikiɗe zuwa manyan ƙulle-ƙullen makirci saboda rashin buɗaɗɗiyar sadarwa da ingantaccen bayani,” inji littafin.
A’isha ta ƙara da cewa: “Ji-ta-ji-ta kan fara, labarai su ɗauki wani nau’in, ba tare da ingantacciyar hanya ta isar da saƙo ba. ’Yan Nijeriya ba su san abin da za su gaskata ba. Wannan hazo na sadarwa ya ci gaba har zuwa ƙarshe.”
Bayan rasuwar Buhari, ta ce, “Waɗanda a da ke riƙe da makullin samun dama—tsofaffin kawunnai da abokan hulɗa masu sauri—sun ji ikon su ya tafi tare da ubangida. Sun tsorota da ni ɗa na.”
A’isha ta ce a Iyalin ta babu wanda ke da sha’awa ko niyyar yin ramuwa a kan kowa. Ta ƙara da cewa, shigar gwamnati cikin shirye-shiryen jana’izar sa ya ceci wani jin kunya.
“Gudanarwar gwamnati kan tsarin jana’izar ta tabbatar da daidaito tare da rage damar ɓarna,” inji ta. Ita da ɗan ta “ba su zo don faɗa ba.” Tsauraran matakan fadar shugaban ƙasa sun hana tsofaffin masu leƙen asiri damar yin shisshigi ko shigar da kan su cikin tsarin. Ta kira su mutane “marasa ƙwarewa,” maza da za ta iya aiki da su “a matsayin shugaban ƙaramar hukuma,” amma ba a matsayin ginshiƙan shugabancin shugaban ƙasa ba.
A’isha ta ce idan rikicin 2017 ya fara ne a kicin, to babban filin dagar sa shi ne gidan da wannan kicin ɗin yake.
A cewar ta: “Aso Villa ba gida kaɗai ba ne, tsari ne gaba ɗaya. Gidan ya cika da ’yan’uwa da matan su da jikoki, da kuma masu shiga-da-fita da ma’aikata da suka san hanyoyin ɓoye da inuwa. ‘Sun yi ƙoƙarin fitar da kowa, har da ni.’”
Ta kammala da cewa: “Wannan gida na ne. Za ku iya zama inda kuke so, amma ba za ku riƙe ofishin miji na ba sannan kuma ku riƙe ni, matar sa, a cikin gida na.”







