Shugaban Amurka, Donald Trump, ya hana Afrika ta Kudu halartar taron ƙolin ƙasashen G20 na shekara mai zuwa da za a yi a Florida bayan Amurkar ta ƙaurace wa taron shugabannin duniya da aka yi a birnin Johannesburg.
Afrika ta Kudu ta maida martani a daren jiya Laraba, ta jaddada cewa zaman Afrika ta Kudu a matsayin membar G20 haƙƙin ƙungiyar ne — ba na Amurka ba.
Fadar Shugaban Ƙasa ta Afrika ta Kudu ta kira matakin da Trump ya ɗauka “wulaƙanci” kuma ta yi alƙawarin ci gaba da halartar dukkan tarukan G20.
Taƙaddamar ta biyo bayan watanni da aka shafe ana rashin jituwa kan manufofin cikin gida da na waje, inda Trump ya ci gaba da dagargazar Afrika ta Kudu tun dawowar sa fadar White House a watan Janairu.
Afrika ta Kudu dai a ranar Talata ta miƙa shugabancin G20 a wani ƙaramin taro na ma’aikatar harkokin waje, bayan ta ƙi yin hakan a taron ƙolin ga wani jami’in jakadancin Amurka, tana nanata cewa dole Washington ta bi “matakin da ya dace.”
Trump ya kafa wa Afrika ta Kudu ƙahon zuƙa da kafa mata tsauraran matakai kan wasu batutuwa tun dawowar sa fadar White House a Janairu, musamman kan iƙirarin da yake yi na wai ana “kisan ƙare dangi” ga fararen fatar ƙasar — iƙirarin da aka tabbatar ba gaskiya ba ne.







