• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Ƙasashen Duniya

Sojoji sun yi juyin mulki a Gini-Bissau, sun kama shugaban ƙasa

Jami’an soji sun bayar da umurnin dakatar da tsarin zaɓe da rufe iyakoki kwana guda kafin a fitar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa.

New Citizen Hausa by New Citizen Hausa
November 26, 2025
in Ƙasashen Duniya
A A
0
Sojoji sun yi juyin mulki a Gini-Bissau, sun kama shugaban ƙasa
Birgediya Janar Denis N’Canha, shugaban ofishin sojin fadar shugaban ƙasar Gini-Bissau, yana bada sanarwar karɓar mulki a ranar 26 ga Nuwamba, 2025. (Hoto: AFP)

Birgediya Janar Denis N’Canha, shugaban ofishin sojin fadar shugaban ƙasar Gini-Bissau, yana bada sanarwar karɓar mulki a ranar 26 ga Nuwamba, 2025. (Hoto: AFP)

Wani gungun hafsoshin soji a ƙasar Gini-Bissau sun bayyana cewa sun karɓi “cikakken iko” na ƙasar, kwana guda bayan manyan ’yan takara biyu a zaɓen shugaban ƙasa sun yi iƙirarin nasara kowannen su.

A cikin sanarwar da suka karanta a talbijin a ranar Laraba, inda suka kira kan su “Babban Kwamandan Soji don Dawo Da Tsari”, hafsoshin sun ce sun bayar da umurnin dakatar da tsarin zaɓe “har sai an ba da wani umarni”.

Haka kuma sun bayar da umarnin a rufe dukkan iyakokin ƙasar, da tashoshin jiragen sama da na ruwa, tare da saka dokar hana fita da dare.

Matakin ya zo ne jim kaɗan bayan an ji harbe-harbe a kusa da hedikwatar hukumar zaɓe, fadar shugaban ƙasa da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida a babban birnin ƙasar, wato Bissau.

An yi tsammanin za a fitar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da aka yi ranar Lahadi – inda Shugaba Umaro Sissoco Embalo da babban abokin hamayyar sa Fernando Dias suka kara – a ranar Alhamis a ƙasar Afrika ta Yamma.

“An kifar da ni,” inji Embalo ga gidan talbijin na Faransa France24 ta wayar tarho, ya ƙara da cewa yana “a hedikwatar rundunar soji”.

Shugaban babbar jam’iyyar adawa ta PAIGC, Domingos Simoes Pereira, shi ma an kama shi.

Gidan talbijin na Aljazeerah ya ruwaito cewa hafsan sojin da ke jagorantar juyin mulkin, Denis N’Canha, shi ne shugaban rundunar tsaro ta shugaban ƙasa.

Zaɓen shugaban ƙasa da ake ƙalubale

Gini-Bissau ta sha fama da juyin mulki da yunƙurin juyin mulki tun bayan samun ’yancin kai daga Portugal a 1974.

Ingancin zaɓen makon nan ya fara jan hankalin ƙungiyoyin farar hula da masu sa ido, bayan jam’iyyar PAIGC ta samu cikas aka hana ta tsayawa takarar shugaban ƙasa.

“An riga an hango cikas a kan wanda zai yi nasara a zaɓen wannan makon, shi ya sa sojoji suka shiga lamarin,” inji wakilin Aljazeerah.

Duk Embalo da Dias sun riga sun ayyana nasara ba tare da wata hujja mai ƙarfi ba.

“Ba za a yi zagaye na biyu ba,” inji Oscar Barbosa, mai magana da yawun kamfen ɗin Embalo, ga kamfanin labarai na AFP a ranar Talata, ya ƙara da cewa shugaban ƙasar “zai samu wa’adi na biyu”.

Dias ma ya ayyana nasara, inda a cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafukan sada zumunta ya ce: “An ci wannan zaɓe. An ci shi tun a zagaye na farko.”

Zaɓen shugaban ƙasa na baya a Gini-Bissau a 2019 ya jawo rikici na watanni huɗu bayan manyan ’yan takara biyu sun yi iƙirarin nasara. A wancan lokacin Embalo ne ya fafata da Pereira.

Kiran dawo da tsarin mulki

A halin da ake ciki, ECOWAS da masu sa ido na Tarayyar Afrika sun bayyana damuwar su kan juyin mulkin soji da ya faru a Gini-Bissau, a cewar wata sanarwa da ƙungiyoyin biyu suka fitar tare.

– Tare da rahoton Aljazeerah

Previous Post

Tinubu ya bayyana dokar ta-ɓaci kan tsaro tare da ba da umurni ga hukumomin tsaro da su ɗauki ƙarin ma’aikata

Next Post

Amurka ta saka wa Afrika ta Kudu takunkumin halartar taron G20 na baɗi

Related Posts

Musulmi za su ɗara Kiristoci yawa a duniya nan da shekarar 2035, inji wani bincike
Ƙasashen Duniya

Musulmi za su ɗara Kiristoci yawa a duniya nan da shekarar 2035, inji wani bincike

November 19, 2026
Ministocin Yaɗa Labarai na Afirka sun nemi samar da tsarin sadarwa na bai-ɗaya
Ƙasashen Duniya

Ministocin Yaɗa Labarai na Afirka sun nemi samar da tsarin sadarwa na bai-ɗaya

November 18, 2026
An kama ‘yan Najeriya takwas a Kanada kan satar motoci na dala miliyan 4.5
Ƙasashen Duniya

An kama ‘yan Najeriya takwas a Kanada kan satar motoci na dala miliyan 4.5

November 17, 2026
Amurka ta yi asarar jiragen saman soji 81 da darajar su ta kai dala biliyan 3.3 a yaƙin Iran — Rahoton Majalisa
Ƙasashen Duniya

Amurka ta yi asarar jiragen saman soji 81 da darajar su ta kai dala biliyan 3.3 a yaƙin Iran — Rahoton Majalisa

October 8, 2026
Ƙasashen Duniya

July 3, 2026
Isra’ila ta tura dakaru da jami’an leƙen asiri zuwa Azabaijan yayin yaƙi da Iran – CNN
Ƙasashen Duniya

Isra’ila ta tura dakaru da jami’an leƙen asiri zuwa Azabaijan yayin yaƙi da Iran – CNN

June 5, 2026
Next Post
Amurka ta saka wa Afrika ta Kudu takunkumin halartar taron G20 na baɗi

Amurka ta saka wa Afrika ta Kudu takunkumin halartar taron G20 na baɗi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!