Kotun zaɓe a ƙasar Kamaru ta bayyana cewa Shugaba Mista Paul Biya ne ya kashe zaɓen Shugaban Ƙasa da aka yi a ƙasar, inda ya samu sama da kashi 53 cikin ɗari na ƙuri’un da aka kaɗa.
Labarin na zuwa ne bayan an shafe tsawon kwanaki ana zanga-zangar ƙin amincewa da ta-zarcen Shugaban Ƙasar inda aka halaka aƙalla mutum huɗu.
Mista dai ɗan shekara 92 ne kuma tun a 1982 yake mulkin ƙasar.
Sai dai magoya bayan jam’iyyun adawa sun zargi hukumomin ƙasar da tafka maguɗi a zaɓen, suna faɗin cewa ɗan takara mai adawa, wato Issa Tchiroma Bakary, shi ne ya ci zaɓen, kuma har ya bayyana cewa shi ɗin ne ya yi nasara.







