Shugaban ƙungiyar IPOB mai rajin kafa ƙasar Biafra, Nnamdi Kanu, a yau ya finjire ya ƙi kare kan sa a kotu, yana faɗin babu wata tuhuma a kan sa.
Da aka koma kotu a yau Litinin a Abuja, wanda wanda a da ya kori lauyoyin sa a kes ɗin tare da iƙirarin zai kare kan sa da kan sa, yanzu kuma ya ce wai ya duba fayilolin kes ɗin bai ga inda ake tuhumar sa ba.
Ya ce: “Ku taya ni gode wa Allah. Na duba fayilolin kes ɗina, ban ga inda ake tuhuma ta ba.
“Babu wata doka da aka girke a ƙasar nan wadda masu ƙara ta za su iya kawo tuhumar su a kai na. Idan har akwai, to ina so Mai Girma Mai Shari’a ya karanta mani ita.
“Don haka, ba zan fara kare kai na a tuhumar da babu ita a ko’ina a dokar Nijeriya ba. Ina kira a gare ka da ka sake ni ko kuma ka ba ni beli.”
Gwamnatin Tarayya tana tuhumar Kanu ne da laifuffuka bakwai da suka danganci ta’addanci.
A ranar Jumaʼa, ya buƙaci kotun da ta ɗage shari’ar bayan ya faɗa wa Mai Shari’a James Omotosho cewa lauyoyin sa na da waɗannan ke ƙarƙashin jagorancin tsohon Antoni-Janar na Tarayya kuma tsohon Ministan Shari’a, Cif Kanu Agabi (SAN), ba su ba shi fayil ɗin kes ɗin nasa ba.
Kuma tun da farko ya bayyana cewa a shirye yake ya kare kan sa da kan sa a rubuce, kuma zai kira shaidu, sannan ya buƙaci a tura masu da sammaci.
To amma da aka zo kotu a yau sai ya ce bai ga tuhumar da ake masa ba.
Ya ce tunda dai tuhumar da ake masa ba bisa doka take ba, kuma masu ƙarar sa sun gaza kawo hujjoji, bai ga buƙatar ya yi wani kare kan sa ba.
A nan, sai Mai Shari’a Omotosho ya umurce shi da ya kawo bayani a rubuce inda zai faɗi matsayar sa kuma ya miƙa kwafen jawabin ga masu ƙarar.
Alƙalin ya shawarci shugaban na IPOB da ya tuntuɓi masana a fagen shari’ar manyan laifuffuka don ya fahimci idan akwai matsala a matakin nasa.
Daga nan alƙalin ya ɗage sauraren shari’ar zuwa ranakun 4, 5, da 6 ga Numba domin a karɓi jawabai na ƙarshe, bisa matsayar Kanu ta cewar babu hujja da aka bayar a kan sa don haka ne ya ƙi amincewa da duk kariya da zai yi wa kan sa.







