Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta dawo da Tarihi a matsayin ɗaya daga cikin fannonin da tilas ɗaliban makarantun firamare da ƙaramar sakandare za su riƙa karanta su a faɗin ƙasar nan.
Jami’an gwamnati sun ce wannan wani babban mataki ne da zai sake haifar da sanin ƙasa, haɗin kai, da kishin ƙasa a Nijeriya.
Gwamnatin ta bayyana matakin ne a cikin wata sanarwa a shafin X na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya a yau Laraba.
Sanarwar ta ce, “A karon farko a tsawon ɗimbin shekaru, yara ‘yan makaranta a Nijeriya za su karanci Tarihi babu ƙaƙƙautawa daga aji 1 na Firamare zuwa aji 3 na Ƙaramar Sakandare, yayin da ɗaliban SSS1–3 za su karanci sabon kwas mai suna ‘Civic and Heritage Studies’, wanda ya haɗa Tarihi da Ilimin Zamantakewa.”
Za a karantar da ‘yan firamare aji 1–6 asali, gwarzaye, sarakuna, al’adu daban-daban, siyasa, tattalin arziki, addinai, mulkin mallaka, da mulki bayan samun ‘yanci na Nijeriya.
Ɗaliban JSS1–3 za su karanci al’ummomin Nijeriya da aka yi, daulolin dauri, hanyoyin kasuwanci, haɗuwa da Turawa, haɗe Kudu da Arewa don ƙirƙirar Nijeriya, ‘yancin kan Nijeriya, da halayen zamantakewar jama’a.
Sabon kwas da za a karantar da ɗaliban SSS1–3, wato ‘Civic and Heritage Studies’, a cikin sa an gwamutsa Ilimin Zamantakewa (Civic Education) da wasu muhimman sassa na tarihin Nijeriya, wanda aka tsara don a samar da al’umma tagari tare da cusa alfahari da ƙasar haihuwar mu.
Ma’aikatar ta bayyana wannan matakin da sunan “babbar tsaraba” ga rayuwar gobe ta ƙasar nan, tana mai nuni da cewa za ta sake haɗa yara da asalin su yayin da take saka alfahari, haɗin kai da sanin asali a zukatan su.
Ta ce, “Tarihi ba kwas kaɗai ba ne; madubi ne wanda ta cikin sa ƙasa take ganin inda ta fito, take fahimtar inda take a yanzu, kuma take shirya wa kan ta inda ta nufa.”
Don tabbatar da aiwatar da tsarin ba tare da mishkila ba, Ma’aikatar Ilimin ta ce ta rarraba manhajar karatu da ta yi wa garambawul ga makarantu a faɗin ƙasar nan, kuma za ta fara gagarumin aikin horas da malamai kan kwasakwasai, da bitar kayan koyarwa, da bin diddigi da sake nazari mai ƙarfi.
Jami’an harkar ilimi na Gwamnatin Tarayya dai sun yi na’am da wannan matakin, suna cewa rashin koyar da Tarihi a makarantu a tsawon shekaru ya hana ɗalibai su san asalin su da ainihin yadda Nijeriya ta ci gaba da tafiya kawo yanzu.






