A yau Laraba waɗansu matasa ‘yan jam’iyyar NNPP mabiya rundunar Kwankwasiyya daga Ƙaramar Hukumar Ɗanbatta a Jihar Kano suka yi taron canza sheƙa zuwa APC bisa jagorancin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin.
An yi taron a ofishin Barau a Majalisar Tarayya a Abuja.
Matasan sun je wajen Barau ne a ƙarƙashin jagorancin Shugaban APC na Ƙaramar Hukumar Ɗanbatta Alhaji Mohammed Liman, tare da Alhaji Ado Rabi’u Ɗanbayero.
A taron, matasan ‘yan siyasar sun bayyana ficewar su daga NNPP ta hanyar cire jajayen hulunan su na Kwankwasiyya, shi kuma Barau ya saka masu sababbin hulana irin na mabiyan sa.
A cewar su, sun gaji da wulaƙancin da ake masu a NNPP da rundunar Kwankwasiyya.

Sanata Barau Jibrin ya yi marhabin da su, yana faɗin cewa lallai NNPP jam’iyya ce da ke kakarin mutuwa a gadon asibiti, kuma “lokaci kawai ake jira kafin ta gama mutuwa.”







