• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Tinubu ya kawo ƙarshen dokar ta-ɓaci a Ribas

Wakilin Mu by Wakilin Mu
September 17, 2025
in Labarai
A A
0
Hayaniyar siyasar 2027 ba za ta ɗauke hankalin Tinubu daga alƙibla ba – Idris
Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bada sanarwar kawo ƙarshen dokar ta-ɓaci da ya sanya a Jihar Ribas a ranar 18 ga Maris, 2025.

A cikin jawabin da ya gabatar daga fadar shugaban ƙasa a yau, Tinubu ya ce an kafa dokar ta-ɓacin ne sakamakon rikicin siyasa da ya yi ƙamari tsakanin Gwamnan jihar, Siminalayi Fubara, da ’yan majalisar dokokin jihar.

Shugaban ya bayyana cewa rikicin ya kai ga gaza gudanar da harkokin gwamnati, inda aka samu rarrabuwar kawuna tsakanin ’yan majalisar, guda huɗu na goyon bayan gwamna yayin da sauran 27 ke goyon bayan kakakin majalisar.

Ya ce hakan ya hana gabatar da kasafin kuɗi, abin da ya haddasa durƙushewar gwamnati gaba ɗaya, lamarin da Kotun Ƙoli ta tabbatar da shi a hukuncin ta, inda ta bayyana cewa babu gwamnati a Jihar Ribas.

Tinubu ya ce duk da ƙoƙarin sa da na wasu ’yan Najeriya don shawo kan rikicin, ɓangarorin biyu sun ƙi sasantawa, lamarin da ya tilasta shi amfani da sashe na 305 na kundin tsarin mulkin 1999 wajen kafa dokar ta-ɓaci.

“Idan ban ɗauki wannan mataki ba a lokacin da aka kai ga mummunan halin da gwamnati ta gaza aiki, to da na gaza wajen kare zaman lafiya da tsaron jama’a,” inji shi.

Ya kuma gode wa Majalisar Tarayya, sarakunan gargajiya da jama’ar Ribas bisa goyon bayan da suka bayar yayin dokar ta-ɓacin.

Shugaban Ƙasa ya ce bayan samun sabon yanayi na fahimtar juna da shirye-shiryen komawa ga tsarin dimokiraɗiyya, babu dalilin ci gaba da dokar ta-ɓacin bayan cikar watanni shida.

Saboda haka, daga misalin ƙarfe 12 na daren 17 ga Satumba, 2025, dokar ta-ɓacin ta ƙare. Gwamna Fubara, mataimakiyar sa Ngozi Nma Odu, da kakakin majalisar, Martins Amaewhule, tare da ’yan majalisar za su koma bakin aiki daga ranar 18 ga Satumba, 2025.

Tinubu ya yi amfani da damar wajen tunatar da sauran gwamnonin jihohi da majalisun dokoki cewa zaman lafiya da kyakkyawan shugabanci su ne tushen kawo romon dimokiraɗiyya ga ’yan ƙasa.

Tags: dokar ta-ɓaciJihar RibasShugaba Bola Ahmed TinubuSiminalayi Fubara
Previous Post

Gwamnatin Tarayya ta fara aikin samar da lantarki daga hasken rana a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano

Next Post

Gwamnatin Tarayya ta dawo da karatun Tarihi tilas a firamare da sakandare 

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Gwamnatin Tarayya ta dawo da karatun Tarihi tilas a firamare da sakandare 

Gwamnatin Tarayya ta dawo da karatun Tarihi tilas a firamare da sakandare 

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!