Kafin mu duba yadda wannan jirgin-kumbo na Voyager 1 ya kafa wannan mashahurin tarihi a ruyawar bil’adam, bari mu ɗan waiwayi tarihi. Allah cikin Suratul Rahman (Ƙ55:33) ya ba mu wata bushara cewa:
“يَا مَعْشَرَ الْجِنِّ وَالْإِنْسِ إِنِ اسْتَطَعْتُمْ أَنْ تَنْفُذُوا مِنْ أَقْطَارِ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ فَانْفُذُوا ۚ لَا تَنْفُذُونَ إِلَّا بِسُلْطَانٍ
“Ya jama´ar aljannu da mutãne! Idan kunã iya keta sãrarin sammai da ƙasã to ku keta. Bã za ku iya ketawa ba fãce da wani dalilin”.
Shekaru 1,400 kafin ɗan’adam ma ya fara wani tunanin tashi sama, Allah ya yi mana isharar cewa za mu iya tashi mu yi tafiya a sama. Kuma da alama wannan aya ce ta zaburi babban masanin kimiyya ɗin nan, Abbas Bn Firnas, a shekarar 875 miladiyya, shekaru kimanin 261 bayan hijirar Manzon Allah (SAW), ya kasance ɗan’adam na farko a tarihi da ya fara tafiya a sararin samaniya na tsawon minti goma a wajen garin Cordova, a gaban bainar jama’a. Duk da cewa lamarin bai ƙare lafiya ba saboda ya faɗo ya ji rauni a baya saboda rashin saka wutsiya (tail), tarihi ne da Turawa suka daɗe su na ɓoyewa, amma kuma da sakamakon cewa Musulmi sun koma barci bayan kafa dan’ba na kimiyyar zamani, sakamakon malamai masu kiran a koma ga Salaf, a daina tunani da nazari (binciken kimiyya da falsafa) sai a kan abubuwan da suka shafi addini kawai.
Tun daga kan wannan zaƙaƙurin malami Musulmi, ba a sake samun wanda ya sake kwatanta tashin ya yi nasara ba sai bayan shekara 1,100, wato a shekarar 1783, inda wasu ’yan’uwa biyu, wato Joseph-Michel da Jacques-Étienne Montgolfier a ƙasar Faransa, suka iya tashi sama a kan balan-balan da ke amfani da iska mai zafi. Wannan ne karo na farko da ɗan’adam ya tashi sama ya yi tafiya mai nisa ba tare da faɗowa ba.
Sai a shekarar 1891, shi kuma Otto Lilienthal, wani injiniyan ƙasar Jamus, ya ƙera jiragen shawagi (gliders) waɗanda ya riƙa tashi da su daga kan tsaunuka sama da sau 2,000, wanda ya ba da ilimin yadda iska ke ɗaga jirgi.
Sai kuma a shekarar 1903, inda su ma wasu ‘yan’uwa biyu, wato Orville da Wilbur Wright a ƙasar Amurka, suka tashi da jirgin sama mai aiki da inji na farko da mutum ke tuƙawa. Tashin farko ya ɗauki daƙiƙa 12 kacal, inda jirgin ya yi nisan ƙafa 120. Wannan aiki na Wilbur Brothers ya sahihantar da yadda za a ƙera jirgin da ya fi iska nauyi (heavier than air machine), abin da ya buɗe ƙofar keta sararin Subhana.
Cikin shekaru 25, wato a shekarar 1927, sai ga Charles Lindbergh ya iya tsallaka Tekun Atlantika, nisan kilomita 3,000 a jirgi cikin awanni 33 da rabi. Bayan Yaƙin Duniya na Biyu kuma, a shekarar 1947, Chuck Yeager ya kafa tarihin gudu a jirgi da ya wuce gudun sauti, abin da ake kira da supersonic flight, wato sai jirgin ya wuce inda kake kafin ka ji ƙarar sa. Yuri Gagarin (ɗan ƙasar Rasha) shi ne wanda ya fara barin mayafin iska da ya kewaye duniya (atmosphere) ya fara tafiya a sararin samaniya a ranar 12 ga Afrilu, 1961, a kumbo na farko, wato Vostok 1.
Neil Armstrong, a shekarar 1961, shi ne wanda ya fara taka wani tsandauri ba duniya ba, inda ya sauka a kan duniyar wata cikin kumbon Apollo 11 na Amurka.
To a shekarar 1977 ne kuma Amurka ta harba ‘yan tagwayen jiragen kumbon ta guda biyu, wato Voyager 1 da Voyager 2, waɗanda aka harba daura da juna, ɗaya ya yi nan, ɗaya ya yi can. A yau ne shi jirgin Voyager 1 ya kafa tarihi na kasancewa jirgi mafi nisa daga duniya. Wannan jirgi ya shekara 50 yana sheƙa gudun kilomita 61,000 a awa guda. Wato kun ga a cikin minti 5 da daƙiƙa 29 zai iya keta Tekun Atlantika, wadda Lindberg ya kwashe awanni 33 lokacin da ya kafa tarihi. Wato a taƙaice wannan jirgi idan ya tashi daga Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano a Kano, zai isa Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Ikko cikin minti 1 da daƙiƙa 49.
To, duk wannan ba shi ne abin mamaki ba. Abin mamaki shi ne yadda bayan wannan matsanancin gudun na tsawon shekaru 50 tare da tafiyar kilomita biliyan 26, sai a yau wannan jirgi ya ci zangon kwana guda a nisan da haske yake tafiya. Saboda tsananin girman sammai, masana na amfani da haske, abin da ya fi kowanne abu sauri a halittu na zahiri da muka sani. Haske yana tafiyar kilomita 17,987,547 a minti guda, dalilin da ya sa idan hasken rana ya taso daga inda take (nisan kilomita miliyan 150), sai ya ɗauki minti 8 kafin ya iso doron duniya saboda tsananin faɗin sammai. Shi ya sa masana suke amfani da tafiyar haske wajen awon nisa a sammai. To a yau ne, bayan shekaru 50 na tafiyar Voyager, ya ci zangon tafiyar haske na kwana guda. Wato a inda Voyager yake a yau, idan haske ya taso sai gobe i-war-haka zai iso doron duniya. Haka nan, saboda zaruruwan lantar-maganaɗisu (electromagnetic waves) waɗanda suka ƙunshi zaruruwan rediyo, tangaraho, x-ray, ultraviolet, microwave duk suke da irin wannan sauri (dukkan su ‘ya’yan haske ne). Shi ya sa idan Voyager ya turo saƙo duniya sai gobe zai zo.
Kamar yadda na ce a baya, saboda tsananin girman sammai, masana ke amfani da haske wajen awon nisa a sama’u. A wannan dabakar tamu ta Milky Way, akwai kimanin taurari biliyan 400 warwatse nesa da juna, yadda tauraro mafi kusa da rukunin ranar mu, wato Proxima Centauri, tana da nisan tafiyar haske na shekara 4. Wato hasken ta sai bayan shekaru 4 idan ya taso sannan yake dukan mu. To yanzu da za a ce wannan jirgin na Voyager 1 zai doshi zuwa Proxima Centauri, sai ya ɗauki shekaru 74,000 yana nausawa. Haka nan idan aka ce jirgin ya ratsa, daga gaba-zuwa-gabar dabakar mu ta Milky Way da ke da nisan tafiyar haske ta shekaru 100,000, sai ya shafe shekaru 1,700,000,000 yana tafiya. Ko kun san irin wannan dabakar tamu ta Milky Way guda nawa ce ita kuma a sammai wadda ake iya hange? Akwai aƙalla dabakoki 2,000,000,000,000. Wa iyazu billah!
Shi ya sa cikin surar izza, wato Suratul Mulk (Ƙi67:3-4) Allah ya ƙalubalance mu da cewa:
“الَّذِي خَلَقَ سَبْعَ سَمَاوَاتٍ طِبَاقًا ۖ مَا تَرَىٰ فِي خَلْقِ الرَّحْمَٰنِ مِنْ تَفَاوُتٍ ۖ فَارْجِعِ الْبَصَرَ هَلْ تَرَىٰ مِنْ فُطُورٍ
ثُمَّ ارْجِعِ الْبَصَرَ كَرَّتَيْنِ يَنْقَلِبْ إِلَيْكَ الْبَصَرُ خَاسِئًا وَهُوَ حَسِيرٌ
“Shi ne wanda Ya halitta sammai bakawi, ɗabaƙõƙi a kan juna, bã za ka ga goggociya ba a cikin halittar (Allah) Mai rahama. Ka sãke dũbawa, ko za ka ga wata ɓaraka? Sa´annan ka sake maimaita, dũbãwa, ganin ka zai komo maka, gajiyayye, ba da ganin wata naƙasa bã.”
A ƙarshe, aya ta gaba (Ƙ67:5) sai ya ce:
“وَلَقَدْ زَيَّنَّا السَّمَاءَ الدُّنْيَا بِمَصَابِيحَ
“Kuma lalle Mun ƙawãta samar farko da fitillu”.
Wannan bayanin na ƙarshe, kimiyya a yau ta tabbatar da shi. Allah ya ce a duk waɗannan taurari da muke iya hange (observable universe) suna cikin sama ta farko. Hasashen kimiyya na cewa daga san da aka haifi wannan sammai daga fashewar Big Bang
Q21:30 “أَوَلَمْ يَرَ الَّذِينَ كَفَرُوا أَنَّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ كَانَتَا رَتْقًا فَفَتَقْنَاهُمَا ۖ
Shin kuma waɗanda suka kãfirta ba su gani da cewa lallai sammai da ƙasa sun kasance ɗinke (singularity), sai Muka tarwatsa su (Big Bang)?”
Bayan wannan Big Bang sai sammai ta fara faɗaɗa zuwa sassan kudu da Arewa, Gabas da Yamma, Ƙur’ani ya bayyana mana cikin Ƙ51:47 da cewa:
“وَالسَّمَاءَ بَنَيْنَاهَا بِأَيْدٍ وَإِنَّا لَمُوسِعُونَ
“Kuma sama, mun gina ta da wani irin ƙarfi (Big Bang) alhãli kuwa lallai Mũ ne Mãsu faɗaɗa ta (expand)”
Wannan faɗaɗar, masana kimiyya na cewa saurin ta shi kuma ya fi na tafiyar haske, wanda Edwin Hubble ya gano a shekarar 1929. Lokacin da yake nazarin dabakoki a Mount Wilson, ya gano wasu na yin shuɗi, wasu na yin ja, abin da ke nuna cewa masu yin ja (red shift) na nisantar mu da tsananin gudu. A yanzu an ƙiyasce fadin wannan sammai da muke iya hange ya kai tafiyar haske ta shekara biliyan 92 daga gaba-zuwa-gaba, sannan a duk sakan samman faɗaɗa take ƙara yi. Duk abin da ya kai gaba (horizon) ya ɓace kenan, har abada ba za mu iya sake hangen sa ba saboda sammai na daɗa faɗaɗa, shi ne ƙalubalen waccan aya ta Suratul Mulk da ke ce mana “Ganin ka zai komo maka gajiyayye”.
A yau bayan kwana guda na tafiyar haske, Voyager 1 yana can yana ci gaba da nausawa sama’u kafin batirin sa ya mutu a shekarar 2040. Ko da batirin ya mutu, zai ci gaba da tafiya in dai ba wani maganaɗisu ne ya zuƙe shi ko ya yi karo da wani dutse ba. Duk da yake masana kimiyya ba su da tabbacin ko akwai wasu halittu bayan mu, amma san da za a harba shi an ɗauki gaisuwa a muryoyi na yaruka 55 na duniya, ko Allah zai sa ya haɗu da wata halitta. Amma tuni Allah ya gaya mana (Ƙ42:29) cewa:
“وَمِنْ آيَاتِهِ خَلْقُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَثَّ فِيهِمَا مِنْ دَابَّةٍ ۚ وَهُوَ عَلَىٰ جَمْعِهِمْ إِذَا يَشَاءُ قَدِيرٌ
“Kuma akwai daga ãyõyin Sa, halittar sammai da ƙasa da abin da Ya wãtsa a cikin su na dabba alhãli kuwa Shĩ Mai ĩko ne ga tãra su, a lõkacin da Yake so”.
Wannan makekeyiyar sammai ta fi ƙarfin a ce mu kaɗai ne a cikin ta, kamar yadda wannan aya ke tabbatar mana cewa akwai halittu warwatse cikin sammai. To, ko Allah zai haɗa Voyager 1 da su ko a’a, Allahu A’alam!
A ci gaba da gashi Voyager 1.







