• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Idris ya nemi haɗin kan ƙasashen Afirka wajen yaƙi da yaɗuwar labaran ƙarya

FATI ABDUL by FATI ABDUL
November 17, 2026
in Labarai
A A
0
Idris ya nemi haɗin kan ƙasashen Afirka wajen yaƙi da yaɗuwar labaran ƙarya
Daga dama: Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al'umma, Alhaji Mohammed Idris, tare da Ministan Yaɗa Labarai, Sadarwa da Tattalin Arzikin Dijital na ƙasar Kenya, William Kabogo Gitau, a lokacin ziyarar yau a Abuja

Daga dama: Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al'umma, Alhaji Mohammed Idris, tare da Ministan Yaɗa Labarai, Sadarwa da Tattalin Arzikin Dijital na ƙasar Kenya, William Kabogo Gitau, a lokacin ziyarar yau a Abuja

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga ƙasashen Afirka da su ƙarfafa haɗin kai wajen yaƙi da yaɗuwar labaran ƙarya, dawo da amincewar jama’a da kuma tabbatar da murya guda ta Afirka kan batutuwan da suka shafi nahiyar.

Idris ya yi kiran ne ranar Talata a yayin ganawa da takwarorin sa na Kenya, William Kabogo Gitau, da Sudan, Khalid Ali Al-Aiser, a gefen Taron Hulɗar Jama’a na Duniya na shekarar 2026 (World Public Relations Forum, WPRF) da ke gudana a Abuja.

Ministan ya ce dole ne ƙasashen Afirka su ƙara haɗin kai wajen tunkarar ƙalubalen sadarwar da suke fuskanta, musamman yaɗuwar labaran ƙarya.

Ya ce: “Dole ne mu nemo hanyoyin yin aiki tare a matsayin ƙasashen Afirka. Muna da muradu iri ɗaya kuma muna fuskantar ƙalubale iri ɗaya, don haka ya kamata matakan da za mu ɗauka su kasance bisa manufa guda. Muna buƙatar ƙarfafa haɗin kai domin tabbatar da cewa sahihan bayanai sun isa ga al’ummar mu, kuma ana wakiltar murya da ra’ayin Afirka yadda ya kamata.”

Dangane da alaƙar Nijeriya da Kenya, Idris ya bayyana shirye-shiryen Nijeriya na ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu. Ya ce zai tattauna da hukumomin da abin ya shafa kan batutuwan da wakilin Kenya ya gabatar, ciki har da batun biza da sauran al’amuran da suka shafi ƙasashen biyu.

Ya kuma bayyana goyon bayan Nijeriya ga ƙarin tattaunawar diflomasiyya, ciki har da shirin ziyarar aiki ta shugaban ƙasa.

A nasa jawabin, Ministan Yaɗa Labarai, Sadarwa da Tattalin Arzikin Dijital na ƙasar Kenya, William Kabogo Gitau, ya nuna damuwa kan wahalhalun da ’yan Nijeriya suke fuskanta wajen samun biza da tafiya Kenya. Ya ce ’yan Kenya na iya shiga Nijeriya ba tare da biza ba na tsawon kwanaki 60, don haka ya buƙaci a samar da daidaito da sauƙaƙa zirga-zirga tsakanin ƙasashen biyu.

“Muna da buƙata dangane da samun biza da kuma matakan da ’yan Nijeriya ke bi yayin tafiya Kenya. Muna fatan za a magance wannan domin sauƙaƙa zirga-zirga tsakanin ƙasashen mu biyu,” inji Mista Kabogo.

Dangane da Sudan kuwa, Idris ya sake jaddada goyon bayan Nijeriya ga ƙasar tare da bayyana fatan samun zaman lafiya da kawo ƙarshen rikicin da ake fama da shi. Ya ce ƙasashen biyu suna da daɗaɗɗiyar alaƙa ta tarihi, al’adu da dangantakar iyali, musamman tsakanin al’ummomin arewacin Nijeriya da Sudan.

Ya ƙara da cewa Nijeriya tana da muradin ganin Sudan ta samu zaman lafiya da farfaɗowa daga rikicin.

A nasa ɓangaren, Ministan Al’adu, Yaɗa Labarai, Kayayyakin Tarihi da Yawon Buɗe Ido na Sudan, Malam Khalid Ali Al-Aiser, ya gode wa gwamnatin Nijeriya bisa goyon bayan siyasa da take bai wa ƙasar sa, inda ya bayyana Nijeriya a matsayin muhimmiyar abokiyar hulɗa.

Ya yi kira da a farfaɗo da haɗin gwiwar ƙasashen biyu, tare da roƙon Nijeriya ta yi amfani da tasirin kafafen yaɗa labaran ta da alaƙar diflomasiyyar ta wajen taimakawa wajen bayyana halin da ake ciki a Sudan yadda ya kamata.

Hagu zuwa dama: Magatakardan Hukumar Hulɗa da Jama’a ta Nijeriya (NIPR), Cif Uzoma Onyegbadue; Mataimakin Shugaban Ofishin Jakadancin Sudan, Ambasada Ahmed Tabuul; da Ministan Yaɗa Labarai, Al’adu, Tarihi da Yawon Buɗe Ido na ƙasar Sudan, Khalid Ali Aleisir, da Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar da Kan Al’umma na Nijeriya, Alhaji Mohammed Idris, da Ƙaramar Sakatare ta Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta Sudan, Sumaya Elhadi Ahmed; da Jakaden Sudan a Nijeriya, Mohammed Abdelaal; da Mataimakin Musamman kan Yaɗa Labarai ga Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Malam Rabiu Ibrahim, lokacin da Ministan Sudan ɗin ya kai wa Mohammed Idris ziyarar aiki a ofishin sa da ke Abuja, a ranar Talata, 17 ga Nuwamba, 2026. (Mai Hoto: Khalid Ahmed/FMINO)

Ya nuna sha’awar ƙarfafa alaƙar kafafen yaɗa labarai na ƙasashen biyu da kuma cimma yarjejeniyar fahimtar juna (MoU).

“Muna godiya da goyon bayan siyasar da Nijeriya ta ba mu a wannan lokaci mai wuya. Muna kallon Nijeriya a matsayin babbar abokiyar hulɗa, kuma a shirye muke mu yi aiki tare domin farfaɗo da kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin ƙasashen mu,” inji Al-Aiser.

Ganawar ta gudana ne gabanin taron teburin ministocin yaɗa labarai na Afirka da aka tsara gudanarwa ranar Laraba, 18 ga Nuwamba, a matsayin wani ɓangare na shirin WPRF.

Ana sa ran taron zai ba ministocin damar tattauna muhimman batutuwan sadarwa da suka shafi nahiyar tare da duba hanyoyin ƙarfafa haɗin gwiwa.

Tags: 2026 World Public Relations Forum (WPRF)AfrikaKenyaKhalid Ali Al-Aiserlabaran ƙaryaMohammed IdrisSudanWilliam Kabogo Gitau
Previous Post

EFCC ta samu nasarar hukunta mutumin da ya yi ƙoƙarin sumogar zinari mai darajar Naira biliyan 4.4 a Kano

Next Post

Ministocin Yaɗa Labarai na Afirka sun nemi samar da tsarin sadarwa na bai-ɗaya

Related Posts

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura
Labarai

Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura

November 25, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa
Labarai

Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa

November 24, 2026
Next Post
Ministocin Yaɗa Labarai na Afirka sun nemi samar da tsarin sadarwa na bai-ɗaya

Ministocin Yaɗa Labarai na Afirka sun nemi samar da tsarin sadarwa na bai-ɗaya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!