• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gwamnatin Tarayya za ta rage farashin fetur a gidajen NNPCL na wata guda

WAKILIN MU by WAKILIN MU
October 8, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Gwamnatin Tarayya za ta rage farashin fetur a gidajen NNPCL na wata guda
Wani gidan mai na NNPCL

Wani gidan mai na NNPCL

Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin sayar da man fetur a farashi mai rangwame a gidajen man NNPCL na tsawon kwanaki 30, a wani mataki na rage wa ’yan Nijeriya da ’yan kasuwa raɗaɗin hauhawar farashin makamashi da sufuri.

Ministan Kuɗi kuma Ministan da ke kula da Tattalin Arziki, Taiwo Oyedele, shi ne ya bayyana hakan a yau Alhamis lokacin da yake gabatar da sababbin matakan gwamnati na rage tsadar rayuwa.

A cewar Oyedele, za a fara amfani da rangwamen ne a gidajen sayar da man NNPCL, inda aka tsara bai wa masu motocin haya da safarar jama’a fifiko, domin rage musu kuɗin da suke kashewa wajen sayen fetur.

Ya ce manufar matakin shi ne samar da sauƙi cikin gaggawa ga masu sufuri da fasinjoji da ke fuskantar ƙarin kuɗin sufuri sakamakon tsadar man fetur.

Ministan ya kuma bayyana cewa wannan mataki ba komawar tallafin fetur ba ne, yana mai cewa gwamnati tana son samar da rangwame na wucin gadi tare da ɗaukar wasu matakai na rage sauyin farashin makamashi.

Daga cikin sauran shirin akwai tattaunawar kafa iyakar farashin saukar da fetur zuwa N1,350 duk lita, wadda za a riƙa duba ta duk wata bisa yanayin kasuwa.

Gwamnatin ta ce tana kuma ƙara mayar da hankali kan CNG da sauran hanyoyin makamashi masu rahusa, domin rage dogaro da fetur da kuma sauƙaƙa kuɗin sufuri. Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kuma bayyana cewa ana son faɗaɗa amfani da CNG domin rage kuɗin sufuri, tare da tabbatar da cewa amfanin makamashi mai rahusa ya isa ga ’yan Najeriya ta hanyar rage kuɗin hawa.

Tags: farashin maiNNPCLragi
Previous Post

Amurka ta yi asarar jiragen saman soji 81 da darajar su ta kai dala biliyan 3.3 a yaƙin Iran — Rahoton Majalisa

Next Post

Shettima ya ce Nijeriya na shirin dasa bishiyoyi biliyan 20, za ta yi koyi da tsarin noma na Habasha

Related Posts

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’

November 25, 2026
Muna samun nasarori a tsaro, ilimi da ababen more rayuwa – Tinubu 
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya ware Naira biliyan 450 domin tallafa wa manoma 500,000

November 22, 2026
Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40

November 19, 2026
CBN ya naɗa kamfanoni takwas domin kula da fitar da ɗanyen mai da iskar gas
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN da NNPCL sun ƙulla yarjejeniyar ƙarfafa tattalin arziki da samar da kuɗaɗen zuba jari a ɓangaren makamashi

November 18, 2026
CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su

November 17, 2026
Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS

November 16, 2026
Next Post
Shettima ya ce Nijeriya na shirin dasa bishiyoyi biliyan 20, za ta yi koyi da tsarin noma na Habasha

Shettima ya ce Nijeriya na shirin dasa bishiyoyi biliyan 20, za ta yi koyi da tsarin noma na Habasha

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!