Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayar da gudunmawar Naira miliyan 500 ga sabon Asusun Ciyarwar Abinci na Al’umma da aka ƙaddamar.
An ƙaddamar da wannan asusu ne tare da haɗin gwiwar ofishin Uwargidan Shugaban Ƙasa, Ma’aikatar Lafiya da Jin Daɗin Jama’a ta Tarayya, Hukumar Kula da Cigaban Kiwon Lafiya ta Matakin Farko ta Ƙasa, da Bankin Manoma (BOA), domin gina ingantaccen tsarin rumbun abinci a Nijeriya wanda zai kasance a ƙarƙashin asusun mai tsari, mai tsare gaskiya, kuma mai iya kaiwa ga al’umma da gidaje a faɗin ƙasar nan.
Uwargidan Shugaban Ƙasar ta bayyana wannan tallafi ne yayin ƙaddamar da shirin da kuma rantsar da kwamitin amintattu a wani taro da aka gudanar a ranar Alhamis a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
A jawabin da ta gabatar, Madam Tinubu ta nuna farin ciki kan yadda aka nuna karamci da goyon baya wajen ƙarfafa tsarin tallafin abinci ga gidaje marasa galihu a faɗin Nijeriya.
Ta jaddada buƙatar magance matsalar rashin abinci mai gina jiki mai tsanani a ƙasar nan, inda ta bayyana cewa rashin abinci mai gina jiki ga yara har yanzu babbar matsala ce ta ƙasa, tare da miliyoyin yara da ke buƙatar samun abinci mai gina jiki a kai a kai domin ingantaccen girma da cigaba.
Ta yi gargaɗi cewa, “Rashin ɗaukar mataki yana shafar lafiyar su, girman su, baiwar su da makomar su, don haka magance wannan matsala abu ne mai buƙatar gaggawa kuma muhimmi domin tabbatar da makomar ƙasa.”

Ta ƙara da cewa an tsara shirin Rumbun Abinci na Al’umma a matsayin mafita mai ɗorewa domin kawo abinci mai lafiya da gina jiki cikin sauƙi ga yara masu rauni ‘yan ƙasa da shekaru 16, tare da ƙarfafa tsarin abinci a matakin al’umma da dawo da daidaito a rabon abinci.
Ta ce, “Wannan shiri yana daidai da manufar mai girma Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na inganta tsaron abinci da kare jin daɗin yara ‘yan ƙasa.”
Uwargidan Shugaban Ƙasar ta ƙara da cewa a duniya baki ɗaya, rumbunan abinci sun nuna inganci wajen tabbatar da cewa abinci mai gina jiki ya kai ga waɗanda suka fi buƙata, ta hanyar haɗin gwiwa da manoma, masu sarrafa abinci, kamfanoni, ƙungiyoyin farar hula da cibiyoyin al’umma.
Ta yaba wa masu ruwa da tsaki irin su manyan ‘yan kasuwa, shugabannin kamfanoni, manyan jami’an gwamnati, abokan hulɗar cigaba, sarakuna da shugabannin addini, da ƙungiyoyin farar hula bisa goyon bayan da suka bayar.
Ta kuma bayyana cewa membobin kwamitin amintattun mutane ne masu ƙwarewa, tsare gaskiya da jajircewa a hidimar jama’a.
Madam Tinubu ta bayyana amannar ta cewa za su samar da jagoranci da kulawar da ake buƙata domin gudanar da asusun cikin gaskiya, inganci da riƙon amana, tare da tabbatar da cewa kowane yanki a Nijeriya ya amfana yadda ya dace.
Ta ce: “Ina taya ku murna kuma ina gode maku da karɓar wannan muhimmin nauyi na ƙasa.
“Haka kuma ina yaba wa mutane da ƙungiyoyi da suka nuna amincewa da wannan shiri ta hanyar alƙawurra da gudunmawar da suka bayar.”
Ta yi kira ga sauran ‘yan Nijeriya masu kishin ƙasa, ƙungiyoyi da cibiyoyi da su shiga wannan yunƙuri na ƙasa, inda aka tsara kai shirin zuwa dukkan yankunan siyasa guda shida na ƙasar nan.
Ta kuma yaba wa Ministan Lafiya da Jin Daɗin Jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate, da tawagar sa, da kuma Manajan Darakta kuma Shugaban Bankin Masana’antu, Dakta Olasupo Olusi, bisa haɗin gwiwa da goyon baya da suke bayarwa.
Tun da farko, Farfesa Pate ya bayyana cewa wannan shiri ya zo a wani lokaci mai muhimmanci a tarihin ƙasar nan ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda manufofin sa suka mayar da hankali kan inganta walwala, lafiya da kariyar zamantakewar ‘yan Nijeriya.
Ya kuma yaba da jagorancin Uwargidan Shugaban Ƙasa wajen ƙirƙira da jagorantar shirin, wanda ya dace da hangen nesa na Shugaban Ƙasa ga ɓangaren lafiya.
Ministan ya ƙara da cewa ma’aikatar sa tana aiwatar da gyare-gyare domin ƙarfafa tsarin lafiya ta fannoni daban-daban, yana mai jaddada cewa an faɗaɗa samun kulawar lafiya ta matakin farko domin inganta lafiyar al’umma.
Ya bayyana cewa wasu abokan Uwargidan Shugaban Ƙasa da suka buƙaci a ɓoye sunayen su sun bayar da gudunmawar dala $500,000, yayin da Gwamnatin Tarayya ta bayar da Naira biliyan 17 ta hannun Asusun Tallafin Zamantakewa ga Shirin Rumbun Abinci na Al’umma na Ƙasa.
A wajen taron, an gabatar da saƙonnin fatan alheri da gudunmawa, inda Gidauniyar Ɗangote ta bayar da Naira biliyan 20, sai kamfanin NNPC Ltd. da ya bayar da Naira biliyan 10, yayin da Gidauniyar Emeka ta bayar da Naira miliyan 500 da za a raba cikin shekaru biyar na shirin.
A cikin wata sanarwa ga manema labarai, Mataimakin Darakta na Sashen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Ado Bako, ya bayyana cewa an ƙaddamar da shirin Rumbun Abinci na Al’umma na Ƙasa ne domin rage matsalar rashin abinci mai gina jiki a tsakanin masu rauni a al’umma.
Ya ƙara da cewa za a fara aiwatar da shirin a yankuna shida na ƙasar nan daga Afrilu zuwa Yuni 2026, sannan a faɗaɗa shi zuwa dukkan ƙananan hukumomi 774 daga Yuli zuwa Disamba 2026.







