• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Friday, October 2, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Nijeriya ta gyara tafiyar ta, yanzu zamanin wadata ya zo – Tinubu

ALI KANO by ALI KANO
October 1, 2026
in Labarai
A A
0
Nijeriya ta gyara tafiyar ta, yanzu zamanin wadata ya zo – Tinubu
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa Nijeriya ta kammala matakin da ya yi wahala na sauye-sauyen tattalin arziki, kuma yanzu ƙasar ta shiga wani sabon zamani na “wadata”, inda gwamnatin sa ta mayar da hankali kan rage tsadar rayuwa, samar da ayyukan yi da rage talauci.

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a cikin jawabin da ya yi wa ’yan Nijeriya na ranar samun ’yancin kai, yayin da ƙasar ke bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kai.

Shugaban ya ce Nijeriya ta shafe shekaru tana fuskantar matsalolin tattalin arziki, rashin tsaro, rikice-rikicen siyasa da kuma gazawar wasu manufofi, yana mai cewa sauye-sauyen da gwamnatin sa ta fara aiwatarwa tun shekarar 2023 sun zama dole domin gyara kurakuran da suka daɗe suna addabar tattalin arzikin ƙasar.

A cewar sa, sauye-sauyen sun fara haifar da alamun farfaɗowar tattalin arziki, ciki har da bunƙasar tattalin arzikin da ta haura kashi huɗu cikin ɗari a bana, raguwar hauhawar farashin kayayyaki, raguwar satar ɗanyen mai, ƙaruwa da sake gina ajiyar kuɗaɗen waje, da kuma samun daidaito a kasuwar canjin kuɗin waje.

Ya kuma ce Nijeriya ta samu mafi yawan kuɗaɗen shiga daga fitar da kayayyakin da ba na mai ba a tarihi a shekarar 2025, inda kuɗin ya haura dala biliyan shida.

“Bayan shekaru uku da rabi, hujjar cewa yanayin tattalin arzikin Nijeriya ya inganta ba za a iya musantawa ba,” inji Tinubu.

Ya ce gwamnatin sa ba za ta koma baya wajen aiwatar da sauye-sauyen ba, duk da kiraye-kirayen da ake yi na komawa tsarin tallafin da ya bayyana a matsayin wanda ba zai ɗore ba.

“Sauye-sauyen mu ba su haifar da raunin tattalin arzikin mu ba. Sun fuskance su ne,” inji shi.

Tinubu ya ce babban abin da gwamnatin sa ta fi mayar da hankali a kai a yanzu shi ne sauya daga gyaran alƙiblar tattalin arzikin ƙasar nan zuwa tabbatar da “wadata mai yaɗuwa ga kowa”.

Ya bayyana cewa wadata, kamar yadda gwamnatin sa ke gani, ita ce Nijeriya inda manomi zai iya noma cikin sauƙi da ƙarancin kuɗi, masana’antu su samu wutar lantarki mai ɗorewa, ’yan kasuwa su samu damar samun rance, sannan matasa su samu ayyukan yi masu amfani.

Shugaban ya ce rage tsadar rayuwa zai kasance babban abin da gwamnati za ta ba fifiko, inda za a ɗauki matakan rage kuɗin samar da kayayyaki da kuma jigilar su zuwa kasuwanni.

Ya lissafa faɗaɗa aikin ban-ruwa ta hanyar amfani da injina da kuma noman rani, inganta damar samun iri da takin zamani, ƙara amfani da injinan noma, gina wuraren adana amfanin gona da inganta harkokin sufuri a matsayin wasu daga cikin matakan da ake ɗauka domin ƙara samar da abinci.

Ya ce gwamnati na zuba jari wajen gina hanyoyi, layukan dogo da tashoshin jiragen ruwa domin sauƙaƙa jigilar kayayyaki daga gonaki zuwa masana’antu da kasuwanni.

“Idan manomi ya samar da amfanin gona cikin ƙarancin kuɗi, idan aka rage asarar amfanin gona tsakanin gona da kasuwa, idan masana’anta ta kashe kuɗi kaɗan wajen samun wutar lantarki, idan mota mai ɗaukar kaya ta isa inda za ta je cikin sauri, kuma idan yanayin kasuwanci ya samar da gasa mai adalci, to duk waɗannan tanadin kuɗaɗen za su kasance cikin farashin kayayyaki a kasuwa,” inji shi.

Dangane da samar da ayyukan yi, Tinubu ya ce ayyukan yi, bunƙasa kasuwanci da masana’antu za su kasance a tsakiyar manufofin gwamnati, musamman ganin yadda Nijeriya ke da yawan matasa.

Ya ce gwamnati za ta yi amfani da albarkatun iskar gas na ƙasar wajen samar da wutar lantarki ga masana’antu, ta tallafa wajen farfaɗo da masana’antun da suka daina aiki, ta faɗaɗa hanyoyin sadarwar zamani zuwa yankunan da suka daɗe suna jiran shiga tattalin arzikin zamani, sannan ta zuba jari wajen koyar da ƙwarewar da masu ɗaukar ma’aikata ke buƙata.

Shugaban ya ce yana son ganin ƙarin kayayyakin da ’yan Nijeriya ke samarwa, da ƙarin amfanin gonakin Nijeriya da ke ciyar da birane da samar wa masana’antu kayan aiki, da kuma ’yan kasuwar Nijeriya suna fitar da kayayyakin ƙasar nan zuwa duniya.

Ya kuma ƙarfafa matasa da su kafa kamfanonin fasaha tare da samar da guraben ayyukan yi ga wasu a cikin ƙasar nan.

Sai dai Tinubu ya amince cewa miliyoyin ’yan Nijeriya suna ci gaba da fuskantar matsaloli wajen samun abubuwan yau da kullum, ciki har da abinci, kuɗin makaranta, magani da kuma sufuri.

Shugaban ya ce gwamnati na ƙarfafa shirye-shiryen tallafa wa marasa galihu, ciki har da ba da tallafi kai tsaye ga iyalai masu ƙaramin ƙarfi da kuma inganta Rajistar Ƙasa ta Mutanen da ke Buƙatar Tallafi, domin tabbatar da cewa tallafin ya isa ga waɗanda suke buƙatar sa da gaske.

Ya yi nuni da Asusun Ba da Lamunin Ilimi na Nijeriya (NELFUND), yana mai cewa shirin na taimaka wa ɗaliban da suka fito daga iyalai masu ƙaramin ƙarfi wajen samun damar yin karatun gaba da sakandare.

Haka kuma ya ce CREDICORP na bai wa ’yan Nijeriya damar samun rancen kuɗi domin sayen muhimman kayayyaki kamar motoci, tsarin samar da wutar lantarki ta hasken rana da na’urorin zamani.

Tinubu ya ce Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da aiki tare da gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi domin ƙarfafa kiwon lafiya na matakin farko, ilimin bai ɗaya da sauran muhimman ayyukan gwamnati da talakawa suka fi dogaro da su.

Ya kuma ce tun daga shekarar 2023, gwamnatin sa ta kasance tana biyan albashi da fansho a kan lokaci kuma cikakke, yayin da aka yi gyare-gyare a tsarin fansho na ƙasa domin inganta jin daɗin ’yan fansho da sauran masu rauni.

“Waɗannan shirye-shiryen ba madadin wadata ba ne. Gada ce da za ta taimaka wa ’yan ƙasar mu a kan hanyar su ta zuwa wadata,” inji shi.

“Manufar mu ba ita ce mu fi iya tafiyar da talauci ba. Za mu kayar da shi.”

Shugaban ya amince cewa rage talauci zai ɗauki lokaci, kuma zai buƙaci ci gaba da bunƙasar tattalin arziki tare da samar da miliyoyin guraben ayyukan yi masu amfani.

Duk da haka, ya ce Nijeriya yanzu tana cikin matsayi mafi kyau na cimma waɗannan manufofi saboda, a cewar sa, an gyara alƙiblar tattalin arzikin ƙasar.

“Zamanin sauye-sauye ya yi aikin sa. Yanzu zamanin wadata ne ya fara,” inji Tinubu.

Yayin da yake waiwayen shekaru 66 da Nijeriya ta yi da samun ’yancin kai, Shugaban ya buƙaci ’yan Nijeriya su ci gaba da kasancewa masu fata da haɗin kai, yana mai cewa ƙasar ta riga ta shawo kan lokuta masu wahala a tarihin ta kuma za ta iya gina makoma mai wadata.

Ya ce bai kamata ’yan Nijeriya su waiwayi baya ba, sai dai su ci gaba da tafiya da ƙarfin gwiwa da imani da kan su da kuma ƙasar su.

“Nijeriya ta gyara tafiyar ta. Mun ratsa namu siraɗin. Wannan ba lokacin waiwayen baya ba ne,” inji shi.

Tinubu ya bayyana “Ƙasar Alƙawari” da ke gaban Nijeriya a matsayin ƙasa mai yalwa da damarmaki, inda za a raba wadata cikin adalci, kuma kowane yaro zai iya yin mafarkin samun makoma fiye da yanayin da aka haife shi a ciki.

“Mun ga inda za mu dosa. Ginshiƙan mu suna da ƙarfi. Alƙiblar mu a bayyane take. Don haka mu ci gaba. Kada mu waiwayi baya,” inji Shugaban.

Ya kammala jawabin nasa da taya ’yan Nijeriya murnar ranar samun ’yancin kai tare da addu’ar Allah ya ci gaba da albarkar Tarayyar Nijeriya.

Previous Post

Ranar Zuciya ta Duniya: Idris ya yi kira da a ƙara kaimi wajen yaƙi da cututtukan zuciya

Related Posts

Ranar Zuciya ta Duniya: Idris ya yi kira da a ƙara kaimi wajen yaƙi da cututtukan zuciya
Kiwon Lafiya

Ranar Zuciya ta Duniya: Idris ya yi kira da a ƙara kaimi wajen yaƙi da cututtukan zuciya

September 30, 2026
Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya
Labarai

Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya

September 29, 2026
Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!