Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga masu watsa shirye-shirye da su tabbatar da sahihanci, adalci da bin ƙa’idojin aikin jarida wajen gudanar da rahotanni yayin da Nijeriya take tunkarar zaɓen 2027, yana mai jaddada cewa watsa shirye-shirye cikin ɗa’a yana da matuƙar muhimmanci wajen kare dimokiraɗiyya.
Mai Taimaka wa Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a kan Harkokin Yaɗa Labarai, Rabiu Ibrahim, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.
Ya ce ministan ya yi wannan kiran ne a ranar Litinin a Bauchi, a cikin jawabin da Darakta-Janar na hukumar gidan rediyon Muryar Nijeriya (VON), Malam Jibrin Baba Ndace, ya gabatar a madadin sa a taron ƙasa na shekara-shekara karo na uku na Society of Nigerian Broadcasters (SNB).
Idris ya ce irin faɗin tasirin kafafen watsa shirye-shirye ya ɗora wa masu aikin wannan fanni nauyin ƙwarewa na tabbatar da cewa bayanan da suke gabatar wa da jama’a sahihai ne, an tantance su, kuma an gabatar da su cikin mahallin da ya dace.
Ya ce, “Duk da haka, bai kamata a fahimci watsa shirye-shirye cikin ɗa’a a matsayin watsa shirye-shirye masu goyon bayan wani ɓangare ba. Kafafen yaɗa labarai masu ƙwarewa dole ne su ci gaba da tambayar gwamnati, jam’iyyun siyasa, ’yan takara da hukumomin gwamnati. Dole ne su gudanar da bincike, su tantance, sannan su ɗora alhakin ayyukan su a kan waɗanda ke riƙe da muƙaman da ke da alhaki.”
Ministan ya buƙaci masu watsa shirye-shirye da su bambanta tsakanin gaskiya, zarge-zarge, ra’ayoyi da iƙirarin da ba a tantance su ba, musamman a wannan lokaci da ƙirƙirarrar fasaha basira (AI) da kafafen sada zumunta suke sauƙaƙa yaɗuwar bayanan ƙarya da kuma abubuwan da aka sauya ko aka ƙirƙira.
Ya ce, “Ba za a ɗauki tantance sahihancin bayanai a matsayin wani abu da ake yi lokaci-lokaci a ɗakin labarai ba; dole ne ya kasance ginshiƙin aikin watsa shirye-shirye na ƙwararru.”
Idris ya ce dole ne masu watsa shirye-shirye su guji kalaman ƙiyayya, tunzura ƙabilanci da addini, da kuma yaɗa bayanan ƙarya da gangan a lokacin zaɓen 2027, tare da ci gaba da samar da damar gudanar da sahihin muhawara da suka.
Ya ce, “Gasar siyasa wani muhimmin ɓangare ne na dimokiraɗiyya, amma bai kamata a bari ta zama sanadin tunzura jama’a, kalaman ƙiyayya, tunzura ƙabilanci ko addini, ko kuma yaɗa bayanan ƙarya da gangan ba.”
Bugu da ƙari, Ministan ya bayyana irin jarin da Gwamnatin Tarayya take zubawa a ɓangaren watsa shirye-shirye, ciki har da dandalin ‘Digital Switch Over’ (DSO) da kuma shirin zamanantar da NTA, FRCN da VON.
Ya ce, “Fasaha ce za ta tsara makomar harkar watsa shirye-shirye, amma amincin da jama’a za su yi da ita zai ci gaba da dogaro ne da mutane.”
Ya buƙaci SNB da masu watsa shirye-shirye da su ƙara ƙarfafa horas da ma’aikata, musamman kan rahotannin zaɓe, tantance sahihancin bayanai da kuma matakan daƙile yaɗuwar bayanan ƙarya da aka ƙirƙira ta amfani da fasahar AI.






