Masu sayar da motoci da ke gudanar da harkokin su a Abuja sun shiga cikin matsala, yayin da Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayar da umalurnin dakatar da amfani da wuraren shuke-shuke, wuraren shaƙatawa da lambuna a cikin birnin Abuja wajen ajiye da sayar da motoci.
Umarnin yana daga cikin matakan da Hukumar Kula da Babban Birnin Tarayya (FCTA) ke ɗauka domin magance matsalar ambaliyar ruwa da ake fuskanta a wasu sassan babban birnin tarayya.
A cikin wata sanarwa da Babban Mataimakin Ministan kan Harkokin Sadarwa da Kafofin Sadarwa na Zamani, Lere Olayinka, ya fitar yau Laraba, ya ce Wike ya nuna damuwa kan yadda ake mayar da wuraren da aka ware domin shaƙatawa da wasanni, ciki har da Millennium Park da sauran makamantan su, zuwa wuraren sayar da motoci.
Saboda haka, ministan ya bayar da umurnin cewa a dakatar da amfani da wuraren shuke-shuke, wuraren shaƙatawa da lambuna wajen sayar da motoci nan take.
A cewar sanarwar, Wike ya kuma bayar da umurnin sanya ido sosai kan duk wani amfani da wuraren da aka ware domin wuraren shaƙatawa, lambuna, wasanni da wuraren shuke-shuke ba tare da izini ba, domin tabbatar da cikakken bin umurnin.
Wannan mataki yana daga cikin manyan matakan FCTA na magance ambaliyar ruwa da ake fuskanta a wasu sassan babban birnin tarayya da kuma tabbatar da cewa ana amfani da wuraren da aka ware ne kawai bisa dalilan da aka amince da su.
Saboda haka, an kafa wani kwamiti na musamman da zai aiwatar da umurnin ministan tare da tabbatar da bin doka daga masu sayar da motoci da sauran mutanen da ke amfani da wuraren shuke-shuke, wuraren shaƙatawa da lambuna ba tare da izini ba.
Wike ya kuma bayar da umurnin gudanar da bincike kan ayyukan wasu ma’aikatan gwamnati da ake zargin suna da hannu wajen bayar da izinin da bai dace ba, wanda ya ba da damar mayar da wuraren shuke-shuke zuwa wuraren sayar da motoci.
Ana sa ran binciken zai mayar da hankali kan yadda aka bayar da izinin sauya wuraren da aka ware domin lambuna, shakatawa da sauran wuraren shuke-shuke zuwa wuraren sayar da motoci ko gudanar da harkokin kasuwanci.
Shugaban Ma’aikatan FCT, Nancy Sabanti Nathan, ta gayyaci ma’aikatan da abin ya shafa, musamman Daraktocin Wuraren Shaƙatawa da Wasanni, Kare Muhalli, Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa da Harkokin Birane.
Ana sa ran gayyatar da binciken za su gano dalilan da suka haifar da bayar da irin waɗannan izini da ake zargi da saɓa doka, tare da gano waɗanda suka amince da amfani da wuraren shuke-shuke, wuraren shaƙatawa da lambunan Abuja wajen sayar da motoci.
Bincike ya nuna cewa adadi mai yawa na masu sayar da motoci a Abuja, wanda aka ƙiyasta ya kai kusan kashi 80 cikin 100, suna amfani da wuraren shuke-shuke da wuraren shaƙatawa da aka ware domin ajiye da sayar da motoci, duk da cewa suna biyan haraji da sauran kuɗaɗe ga gwamnati.
Da yake magana da jaridar Newspoint Nigeria labarai kan lamarin, wani dillalin motoci da ke Abuja, kuma mamallakin BeeCee Cars, Mukhtar Ibrahim Bichi, ya roƙi Hukumar Kula da Babban Birnin Tarayya (FCTA) da ta sake duba batun haramcin.
Bichi ya ce da yawa daga cikin wuraren shuke-shuke da wuraren shaƙatawa da masu sayar da motoci ke amfani da su a yanzu, da sun iya zama mafakar masu aikata laifuka idan dillalan motocin ba su ɗauki nauyin kula da wuraren tare da tabbatar da tsaron su ba.
Ya ce masu gudanar da harkokin ba wai kawai suna biyan maƙudan kuɗaɗen haraji ga gwamnati ba, har ma sun taimaka wajen sanya wasu daga cikin wuraren cikin amfani da kuma tabbatar da ana kula da su yadda ya kamata.
A cewar sa, maimakon gwamnati ta sanya cikakken haramci, ya kamata ta yi la’akari da kafa tsari na musamman da zai ba masu sayar da motoci damar gudanar da harkokin su a wuraren da aka ware, tare da sauya waɗannan wurare zuwa cibiyoyin shaƙatawa da za su iya karɓar baje-kolin motoci da sauran abubuwan da suka shafi harkar.






