• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Sabon Kundin Dokokin Canjin Kuɗi: Yadda CBN ke ƙoƙarin hana naira tambotsai a kasuwar canjin kuɗaɗen waje ta Nijeriya 

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
June 6, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Sabon Kundin Dokokin Canjin Kuɗi: Yadda CBN ke ƙoƙarin hana naira tambotsai a kasuwar canjin kuɗaɗen waje ta Nijeriya 

 

Kwanan baya ne dai Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ƙaddamar da sabon kundin sharuɗɗan harkokin canjin kuɗaɗen waje, wato ‘Foreign Exchange Manual’, wanda wata babbar alama ce a ƙoƙarin da ake yi na dawo da tsari, sake gina amincewa da kuma ƙarfafa gaskiya a mu’amalolin canjin kuɗaɗen waje a Nijeriya.

A daidai lokacin da Nijeriya ke ƙoƙarin tabbatar da daidaiton tattalin arziki, ƙara jawo hankali da amincewar masu zuba jari na dogon lokaci daga ƙasashen waje, sabon tsarin ya samar da ƙa’idoji da dokoki masu bayyana alfanu ga dukkan masu ruwa da tsaki a harkokin canjin kuɗaɗen waje.

Tsawon shekaru, kasuwar canjin kuɗaɗen waje a Nijeriya ta fuskanci matsaloli irin su rashin bayyana gaskiya, faɗuwar-‘yan-bori da farashi ke yi, ƙarancin kuɗaɗen da ake samu a kasuwa, yawan tsarin farashi daban-daban da kuma dogaro sosai kan tsoma bakin Babban Banki. Sau da yawa, amincewar kasuwa na raguwa saboda rashin tabbas kan samun kuɗaɗen waje, jinkirin biyan kuɗi, rashin daidaito a takardu da kuma damuwa game da bin ƙa’idojin kasuwa.

A wannan yanayi ne sabon kundin dokokin canjin kuɗi ya wuce a kira shi kawai sabuntawar tsarin gudanarwa. Domin yana daga cikin wani babban yunƙuri na gina tsarin kasuwar canjin kuɗaɗen waje da ya fi bayyana gaskiya, bin ƙa’idoji da kuma dogaro da kasuwa.

Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya bayyana wannan buri a fili lokacin ƙaddamar da bugu na huɗu na kundin a Abuja, inda ya ce tsarin wani ginshiƙi ne na gyare-gyaren da ake aiwatarwa domin ƙarfafa gaskiya, zurfafa wadatar kuɗaɗe a kasuwa da kuma dawo da amincewa baki ɗaya.

Jawabin sa ya nuna babban jigon da ke tafiyar da sauye-sauyen da CBN ke aiwatarwa a yanzu: cewa ba za a iya tabbatar da ɗorewar amincewa a kasuwar canjin kuɗaɗen waje ba sai an samu ƙa’idoji bayyanannu, bin doka, ɗaukar alhaki da haɗin gwiwar masu ruwa da tsaki.

Muhimmancin sabon kundin wanda shi ne na huɗu, ya ta’allaƙa ne da lokacin da aka fitar da shi. An wallafa kundin da ya gabata ne a shekarar 2018, kafin manyan sauye-sauye su girgiza tattalin arzikin duniya da kuma yanayin tattalin arzikin cikin gida na Nijeriya.

Tun daga lokacin, kasuwannin kuɗi na duniya sun fuskanci ƙarin rashin tabbas, yayin da Nijeriya ta yi fama da hauhawar farashi, ƙarancin kuɗaɗen waje, raguwar amincewar masu zuba jari da kuma matsin-lamba kan ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje.

Saboda haka, sabon kundin wani yunƙuri ne na daidaita tsarin gudanar da harkokin canjin kuɗaɗen waje, tare da magance matsalolin da suka daɗe suna addabar tsarin.

Cardoso ya jaddada cewa canjin kuɗaɗen waje muhimmin ginshiƙi ne a kowane tattalin arziƙin da ke buɗe ga duniya, domin yana taimakawa wajen tabbatar da daidaiton farashi, sauƙaƙa kasuwanci da saisaita saɓatta-juyattar jari, tare da tasiri kan yadda masu zuba jari ke kallon ƙasa.

Wannan matsayi ya nuna dalilin da ya sa gyaran kasuwar canjin kuɗaɗen waje ya zama muhimmin ɓangare na kula da tattalin arzikin ƙasa gaba ɗaya.

Ɗaya daga cikin manyan saƙonnin da suka fito daga ƙaddamarwar shi ne muhimmancin jaddada gaskiya da tabbacin tsarin aiki. A cewar Cardoso, sabon kundin zai taimaka wajen ƙara bayyana dokoki, daidaito da inganci wajen gudanar da harkokin canjin kuɗaɗen waje.

Waɗannan ginshiƙai suna da matuƙar muhimmanci wajen dawo da amincewar masu zuba jari, domin galibi masu ruwa da tsaki suna nuna kyakkyawan martani idan dokoki suna a bayyane kuma ana iya hasashen yadda za a aiwatar da su.

Sabon tsarin ya kuma yi niyyar rage rashin tabbas a ayyukan kasuwa ta hanyar samar da tsare-tsaren da suka fi kyau wajen gudanar da ma’amaloli, bayar da rahotanni da sarrafa takardu.

Daga cikin sauye-sauyen da aka gabatar akwai gyara kan iyakokin biyan kuɗin shigo da kaya, tsarin zamani wato dijital kuɗin tafiye-tafiye, ƙarin buƙatun bayar da rahoto ga masu fitar da ayyuka da kamfanonin fasaha, sauƙaƙe tsarin takardu da kuma faɗaɗa damar amfani da asusun banki.

Waɗannan matakai na nuna ƙoƙarin amfani da hanyoyin zamani da dijital wajen gudanar da kasuwar, tare da ƙarfafa sa-ido a wuraren da a baya ake samun ƙorafe-ƙorafe, ko raunin bin doka.

Sai dai wata kila abin da ya fi ɗaukar hankali a sabon kundin shi ne ƙarfafa tsarin bin doka da hukunta masu karya ƙa’ida. Kundin ya ƙunshi tsauraran hukunci kan laifuka kamar cinikin kuɗaɗen waje ta bayan fage, amfani da takardun bogi, rashin gabatar da rahotanni da kuma karya iyakokin cinikin kuɗaɗen waje da aka amince da su.

Wannan na nuna cewa CBN na ƙoƙarin kafa tsari mai ƙarfi na ladabtar da kasuwa.

Cinikin bayan fage wanda aka daɗe ana kallon sa a matsayin ɗaya daga cikin munanan ayyukan da ke lalata kasuwar canjin kuɗaɗen waje, na daga cikin laifukan da ke fuskantar mafi tsananin hukunci.

Bankunan da aka samu da aikata irin wannan laifi za su iya fuskantar dakatar da lasisin dillancin canjin kuɗaɗen waje na aƙalla watanni shida tare da cikakken aiwatar da hukuncin, mayar da kuɗaɗen da suka samu ba bisa ƙa’ida ba, tare da ƙarin kuɗi bisa farashin kasuwa, kai su gaban Kwamitin Ɗabi’u na Kwamitin Bankuna, yiwuwar gurfanarwa a gaban hukuma da kuma kw5ace lasisi gaba ɗaya, idan suka sake maimaita laifin.

Tsananin wannan hukunci na nuna aniyar CBN ta daƙile ayyukan rashin gaskiya da ke karkatar da kasuwa da rage amincewa.

Haka kuma, kundin ya tanadi hukunci ga rashin isar da kuɗaɗe a ma’amalolin da aka amince da su, bayar da rahotannin ƙarya, amfani da kuɗaɗen waje a ɓangaren abubuwan da ba a amince da su ba da kuma rashin cikakkun takardun ma’amala.

Tsarin ya kuma yi tanadi kan hukuncin karya iyakokin matsayin cinikin kuɗaɗen waje da aka ba bankuna. Bankunan da suka wuce iyakar da aka amince da ita za su fara fuskantar gargaɗi, daga bisani dakatarwa daga kasuwar canjin kuɗaɗen waje, sannan a ƙarshe a ƙwace lasisin dillanci idan suka ci gaba da karya doka.

Abu mai muhimmanci shi ne cewa sabon kundin ya tanadi tsarin ɗaukar alhaki wanda ya wuce hukunta cibiyoyi kawai. A ƙarƙashin tanadin ƙa’idoji, ana buƙatar bankuna su kafa kwamitocin bincike na gudanarwa da kwamitin daraktoci domin gano hannun ma’aikata a laifukan da aka aikata, hukunta masu laifi da kuma bayar da tabbacin cewa ba za a sake maimaita irin waɗannan laifuka ba.

Wannan na nuna cewa ba wai kawai CBN yana neman cibiyoyi su bi doka ba ne, har ma yana son sauya halayen aiki a cikin cibiyoyin kuɗi.

Ƙarfafa Bin Doka da Ladabtar da Kasuwa

Wani muhimmin ɓangare na gyare-gyaren shi ne mayar da hankali kan dawo da kuɗaɗen da aka samu daga fitar da kaya zuwa ƙasashen waje da kuma tabbatar da bin doka a fannin fitar da kayayyakin da ba na mai ba.

Kundin ya tanadi hukunci ga masu fitar da kaya da suka kasa dawo da kuɗaɗen da suka samu cikin kwanaki 180, yayin da bankuna da hukumomin binciken kaya kafin jigila su ma za su fuskanci hukunci idan suka yi jinkiri wajen takardu, aika kuɗaɗe ko bayar da takardun shaidar da ake buƙata.

Wannan ya yi daidai da manufar ƙara hanyoyin samun kuɗaɗen waje da kuma ƙarfafa fitar da kayayyakin da ba na mai ba a matsayin tushen samar da kuɗaɗe ga kasuwa.

Cardoso ya sha bayyana cewa a ƙarshe dai manufar wannan gyare-gyaren ita ce samar da wadatar kuɗaɗe a kasuwa. A cewar sa, kasuwa mai zurfi da wadatar kuɗaɗe za ta rage karkacewa, za ta ƙara samun amincewar masu zuba jari da kuma rage dogaro da tsoma bakin Babban Banki.

Wannan ya nuna babban sauyi daga tsarin da aka saba, inda masu ruwa da tsaki ke jiran tsoma bakin CBN domin samun kuɗaɗen waje.

Ƙaruwar yawan ma’amaloli a kasuwa na ɗaya daga cikin manyan shaidu na wannan sauyi, inda a cewar sa, matsakaicin yawan kuɗaɗen da ake mu’amala da su a kullum ya tashi daga kusan dala miliyan 100 a farkon gwamnatin yanzu zuwa tsakanin dala miliyan 400 da dala miliyan 600, tare da wasu lokuta da ya kai dala biliyan 1.

Wannan ci gaba yana da muhimmanci domin yawan ma’amaloli na nuna zurfin kasuwa, wadatar kuɗaɗe da kuma amincewar masu ruwa da tsaki.

Burin CBN na kaiwa ga hadahadar sama da dala biliyan 1 a kullum na nuna aniyar sanya kasuwar Nijeriya ta yi gogayya da kasuwannin ƙasashe masu tasowa da suka ci gaba.

Har ila yau, bayanan CBN kan ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje sun nuna cewa ajiyar kuɗi kariya ce ga tattalin arziki, ba wai tushen kai tsaye na samar da kuɗaɗe ga kasuwa ba.

Cardoso na nuna cewa ana ƙoƙarin barin tsarin da ya dogara sosai kan tsoma bakin CBN zuwa tsarin da ya fi dogaro da wadatar kuɗaɗe da amincewar masu ruwa da tsaki.

A wannan tsari, akwai matuƙar buƙatar ƙara haɗin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki, kamar yadda

Cardoso ya jaddada cewa ba za a iya samun daidaito da amincewa a kasuwar canjin kuɗaɗen waje ta hanyar aikin CBN shi kaɗai ba.

A zahiri, goyon bayan da bankuna za su bayar yana da muhimmanci, domin nasarar aiwatar da tsarin za ta dogara ne kan yadda bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi masu gudanar da yawancin ma’amalolin canjin kuɗaɗen waje za su bi dokoki.

Matakin da CBN ya ɗauka na raba kuɗin kyauta ga dukkan bankunan da dillalai ke amfani da su ma yana nuna ƙoƙarin sa na tabbatar da bin doka da sauƙaƙa samun bayanai.

Mataimakin Gwamnan CBN mai kula da Sashen Manufofin Tattalin Arziki, Muhammad Sani Abdullahi, ya ce an gudanar da tattaunawa mai zurfi da bankuna, masu fitar da kaya, hukumomin gwamnati, kamfanoni da abokan hulɗar ci gaba kafin a kammala kundin.

Ya ce irin wannan haɗin gwiwa zai taimaka wajen karɓuwar tsarin, domin masu ruwa da tsaki sun shiga cikin tsara shi.

Abdullahi ya kuma danganta kundin kai tsaye da manyan gyare-gyaren da ake aiwatarwa ƙarƙashin jagorancin Cardoso, yana mai cewa an tsara shi ne domin rage matsaloli, kawar da cikas da kuma gina tsarin da ya fi bin ƙa’idoji da dogaro da kasuwa, wanda zai inganta gano farashi da jawo jarin da zai ɗore.

Tags: Babban Bankin Nijeriya (CBN)CardosoCBNforeign exchangemanual
Previous Post

Isra’ila ta tura dakaru da jami’an leƙen asiri zuwa Azabaijan yayin yaƙi da Iran – CNN

Next Post

CBN ya umurci bankuna su riƙa bibiyar dalilin yadda kwastomomi ke tura kuɗaɗe daga asusun kuɗaɗen wajen su, ko su fuskanci tarar naira miliyan 100

Related Posts

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gangamin CBN a Kano: A daina wulaƙanta takardun naira, a riƙe su cikin inganci da nagarta – CBN

September 29, 2026
Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Next Post
Manyan nasarorin da CBN ya samu cikin 2025

CBN ya umurci bankuna su riƙa bibiyar dalilin yadda kwastomomi ke tura kuɗaɗe daga asusun kuɗaɗen wajen su, ko su fuskanci tarar naira miliyan 100

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!